Skip to content

Chapter 57

Chapter 57

Zumuncinmu A Yau Book One Complete Hausa Novels 1 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

ba, bani da kudi haka na goyashi saboda bashi da kayan sawa, ga rashin karfi nawa da nashi, Cikin ikon Allah muka samu motar zuwa Gombe, saida muka kwana uku a hanya muna tafiya, duk kauyen da muka tsaya anan zan roki ruwan zafi in mishi wanka, wata baiwar Allah ce ta hada min da wani maganin da nasha har na samu karfin jikina, sannan ta bani wanda na barbada ma cibiyarshi hade da gishiri, koda muka isa gida nan ma akayi min caaa ana Allah wadai dani, ban saurari kowa ba na shiga gurin mahaifiyata na roki gafararta, nace mata zan tafi neman abun da zan rike ďa na, Bata kalleni ba amma shashshekar kukanta shi ya tabbatar min da tana cikin tsananin damuwa, har na kai kofa ta kirani, dawowa nayi naga ta kwanto gefen zaninta ta fito da kudi masu yawa na furar da takeyi ta bani ba tare da ta kalleni ba, Murmushin farin ciki nayi na dauki wannan kudin a matsayin sa min albarka tayi, nan nayi mata sallama na fita, A tsakar gida sai zunde na sukeyi, babu wanda ya kula da halin da zamu shiga ni da dana, su dai burinsu in rabasu da abin kunyar da na dauko musu, cikin gari na wuce dan neman aikin da zanyi in ciyar da kaina, Da farko a wani kango muke kwana wanda ake gininshi kullum, kayan sawa na dasu nake dukunkuneshi saboda bashi da na sawa, da safe in masu ginin sun zo sai in goyashi in tayasu dan in samu wani abun rikewa a hannu, a haka har mukayi sati daya a cikin gurin, Ranar da muka cika kwana takwas Abdallah ya tashi da ciwo mai zafi kamar bazai yi ba, saboda rashin sanin abin yi na zauna na tasa shi a gaba nayi ta kuka, daya daga cikin masu kula da gidan ne ya tausaya min ya dauke mu a gurin ya kaimu wani shagon kwano yace mu dinga kwana a ciki, Sannan ya nemo min bedi da yawa da icce da tukunya yace in dafa mishi ya dan sha ruwan in mishi wanka, kafin inyi mishi godiya naga ya fita ya karbo wata kwarya, tuwon dawa ne a ciki da miyar kuka, nan na hau ci kamar karamar zakanyar da taga nama, A haka dai muka cigaba da rayuwa har na samu aikin shara a wani gurin gwamnati, saida na shekara biyu ina aiki a gurin, a lokacin Abdallah ya fara girma amma yau da lafiya gobe babu, kullum matsalar cibiya yake fama da ita, saida ya shekara bakwai sannan na kaishi asibiti, anan ne ake fada min tarin datti ne ya shiga cibiyar, jinjina tsawon rai irin nashi likitan yayi da na bashi labarin yadda na sameshi yace "lallai yaron nan Allah yana san saukar da rubutacciyar aya ta dalilinshi, anan dai likitan yayi mishi aiki, cikin lokaci kalilan ya samu lafiya muka dawo aikinmu, kullum tare muke zuwa yana tayani, A gefen gurin da nake shara akwai wata makaranta, da naga yana yawan zuwa gurin ya tsaya, kuma yana sha'awar karatun, sai na kaishi makarantar, islamiyya ma yana zuwa ta allo sannan ina koyar dashi a gida.. gwagwarmaya babu irin wacce bamu sha ba ni dashi, Lokacin da ya gama makaranta, ya fito da sakamako mai kyau, gwamnati ce ta dauki nauyin cigaban karatunshi saboda hazakar shi, A lokacin da yake karatun ne muka dan fara samun sauki saboda in aka bashi kudi a nan gida yake barin su, ya gwammaci in ya dawo gida muyi amfanin da kudin, *Nasara* ta Allah ce amma ni zan iya cewa ita ainihin kalmar ma'anarta shine Abdallah, shekarar da ya gama jami'a aka bashi aikin koyar da yan aji daya a makarantar, duk inda yaje a unguwarsu zakiji Ana fadin *Abdallah Hanne*, da sunan da yake amfani kenan ko a makaranta, ko kuma ace uncle Abdallah.. yaran unguwa yake tarawa yayi ta koya musu karatu.. jan majina tayi dan kuka na neman cin karfinta ta cigaba da cewa "tunda muke da Abdallah sau daya ya taba cemin "Ina Babana *ANNE* sunan da yake kirana kenan tun yana yaro, a ranar nayi kuka sosai wanda ya tayar da hankalinshi, tun daga ranar duk gorin da ake mishi bai damunshi, saboda yasan wani mai uban ma bazai nuna mishi jin dadi ba, A kullum saidai in dinga fada mishi kana da uba, kai ba dan shege bane, kai dan sunna, aure ne ya samar dakai, Kullum addu'ata Allah ya hadani da mahaifin Abdallah koda sau daya ne ya ji wannan farin cikin da yayi dakon su shekara da shekaru, bayan ta kai aya ta kalli Papy da ya fita hayyacinshi saboda tsabar kuka tace "shine mahaifinka Abdallah, wannan shine ya haifeka! Rungume Anni Papy yayi ya tsananta kukanshi yace "duk duniya babu na biyunki Anni, saboda ni kika bar gida, kika bata rayuwarki da lokacinki! saboda ni kika ki yin aure, saboda ki inganta rayuwata kika hana taki ta zama ingantacciya, why Anni, Why?? Ya karashe yana kuka sosai, Itama kukan takeyi tace "bani nayi ba Abdallah, Allah ne, yin Allah ne, in ba Allah ba waye zai rabaka da iyayenka, babu mamaki yayi haka ne domin ka zama nagartacce, ya rabaka da danginka ne dan ka zama gawurtaccen mutum, babu mamaki da kana gida duk wadannan abubuwan bazasu samu a gareka ba, dalilin da yasa Allah ya barka da rai bayan ka shiga karkashin kasa ba karamin dalili bane.. Maimuna ma ta taka rawar gani a cikin rayuwarka, tasoka a lokacin da kowa ke kiranka da dan gaba da fatiha, Duk kushe ka da akeyi a lokacin kamar ana zugata ne, ta tubure sai ta aureka, Maimuna ta nuna mana kauna lokacin da kowa ya kyamace mu, Cikin Kuka Mami tace "kinyi jarumtar da ko kwatanshi banyi ba Anni, hadasu yayi ya rungumesu yace "banyi regretting rashin tashi a cikin yan uwana ba, domin babu abin da ban samu ba a gareku, uwa, uba, mata, kawa, Aboki, ni ko me zancewa Allah, babu abin da zance sai tarin godiya a gareshi da ya hada ni daku.... Shuru ne ya dan ratsa gurin, sai ajiyar zuciyar kuka kawai ke tashi, kallon farin ciki Baffa yakewa Papy, fuskan nan tasu jike sharkaff da hawaye, Hannun shi ya kamo ya sake fashewa da kuka yana fadin *SAIFULLAH*, Ma'u dana ne, *SAIFULLAH*, jinina ne Ma'u...... Mrs Tijjani Shattima..... [19/03 8:17 PM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 4⃣0⃣ By *Aysha Ya'u kurah* *Rayuwa takaitacciya ce. Kada ka cika ta da damuwa. Kada dogon Buri ya dauke hankalinka daga mutuwa. Aikata alheri a kowane lokaci watakila shi zai zamo mabudin Aljanna a gare ka*. Alkalamina bashi da karfin rubuta irin gigitar da Ma'u tayi, a zaune take amma jinta take tamkar a tsaka tsaki take, ita bata kai kasa ba haka bata kai sama ba, jinta take kamar wacce take lilo a tsakiyar iska, gaba daya hanyoyin sadarwa na jinin jikinta da kwakwalwarta sunyi balaguron wucin gadi.. Jin hannu da tayi cikin nata ya sanyata dawowa cikin hayyacinta a firgice, kallon hannun tayi hade da mamallakin hannun, ido cikin ido sukayi Anni tace "Da fatan kin gamsu da bayani na, da fatan kin tuno abubuwan da

Table of Contents

Chapters

156 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156