Skip to content

Chapter 92

Chapter 92

Zumuncinmu A Yau Book One Complete Hausa Novels 1 1,199 words 0 views Progress saved
Download Book

ta fara kunno wutar tashin hankali da masifa a gidan, idan Allah yasa ranar a dakin Anni Baffa zai kwana tofa babu bacci, dan ta dinga dukan kofar da muciya kenan, abun ba karamin damun Baffa yakeyi ba, Anni ke hanashi magana ta nusar dashi yanzu tsufa yazo, ba lokacin sa'insa bane, lokacin da zamu koma ga Allah ne, haka zasu mike suyi ta Sallah har ta gaji ta koma daki tana zage zage kamar wata yarinya, Yau ma kamar Kullum Anni na tsakar gida ita da mai aikinta suna girkin sadaka , Shinkafa ce da wake sai lettuce da su tumatur, suna gamawa aka fara zubashi a farantai ana fita dasu waje almajirai na rige rigen karba, makota masu karamin karfi suma suka shigo da robobinsu aka zuba musu, sunyi nisa sosai gurin rabo Goggo ta fito da bokitin fenti karami, fitsari ne a ciki ya kai rabi, nan ta doshi katuwar tukunyar ta antaya fitsarin a ciki, Da kyar Anni ta iya danne bacin ranta dan ta harzuka matuka, rufe tukunyar tayi tace "Harira, ki kira almajirai su kwashe abincin nan su kai ma dabbobi yau ranar tasu ce, tana kaiwa nan tayi hanyar dakinta, gabanta Goggo tasha ta dinga dura mata zagi, ita dai Anni dariya kawai takeyi tana fadin nagode, "ni yanzu ai bana fada, fada na yara ne da kuma wanda bai samu abinda yake so ba, ni kuwa me zance ma Allah, ai sai godiya, in nayi fada ai na butulce mishi, inaaa ni ba butulu bace, Allah ya gamai min komai, Hannu Goggo ta daga yana rawa zata kwadama Anni, da sauri Baffa ya rike hannun ya maida nashi kan fuskarta, Rike hannunshi Anni tayi tace "Haba dan Allah, ba girmanka bane, yanzu kaga ni bata mareni ba, ka mareta, da ka kyaleta wallahi bazai min tabo ba, Dan Allah mijina kar ka sake daga hannu a kan mace koda kuwa yarinya ce, kasan daraja garemu, sake matse hannun tayi tace muje kaci abinci ka fita nemo mana halal, Duk abin nan da akeyi akan idon Mummy da su Radiya ake yinshi, nan ran Mummy ya kara baci, a harzuke ta iso kusa da Baffa tace "Baffa duka? Dukan mahaifiyata Baffa, dama irin ukubar da take ciki kenan, habawa kamar an bude famfo Goggo ta fara kuka mai sauti, riketa Radiya tayi tana harara Baffa da Anni, Murmushi Anni tayi tace "cikin jin dadi take wannan ma tsauts----- rufe min baki, Mummy ta katseta cikin tsawa, "wacece ke da zaki samin baki a cikin magana ta, da wanda ya haifeni nake ba da ke ba, ki tsaya a matsayinki kin gane ko? Murmushin dake kan fuskarta bai gushe ba ta sake damke hannun Baffa dan taga yana yunkurin kwacewa yayi wata aika aikar tace "muje mijina, kar yunwa tayi maka lahani, Bayanta yabi suka bar su da sakkaken baki, Goggo kuwa kuka takeyi bilhakki da gaskiya wanda ya zame mata dan kullum, wannan kukan da Baffa ke sata tasan bashi ne, duk ranar da ya dawo hannunta sai ya kwashi kashinshi a hannu, dan walhi bazata barshi ba, bari dai asirin da Anni tayi mishi ya sakeshi, ita kuma ta daura nata, "a tunaninta asiri Anni tayi mishi dan yadda ya zama sauna akanta tasan ba lafiya ba, bata san kyautatawa da kissa yafi asiri tasiri a gurin namiji ba... Wata ashar Raudha da Radiya suka saki da Mummy ta labarta musu shirin da Daddy yayi na auren Musaddiq, Raudha ta daga murya tace "Wallahi bazai yiwu ba, wannan uwar daular da Musaddiq ya shiga ni kadai na santa, sannan yadda muka ci burin aura mishi Faida mahaifinta yasa a kara mishi girma nan take shine Daddy yake mana bakin ciki, wallahi bazata taba sabuwa ba, wallahi da ya auri Nadeeyah gara ya mutu ba Aure, haka nan ga inda ake harkar arziki mu kare a dangin tsiya, dangin marasa asali, wallahi da kaina zanyi maganin abun, karma kisa kanki Mummy, ki bani kwana Hudu zakiji labarin ya wargaje, badai ni ke zaune dashi a lagos din ba, zanyi brain washing dinshi, ki barni dashi kawai, ki nunawa Daddy kin amince sai mu cigaba da shirya musu kulli ta bayan kasa... Assalamu Alaikum, Anni ta fadi hade da shigowa dakin ta ajiye musu cooler, "ga abin kari da fatan ban shiga cikin maganarku ba, tsaki Mummy taja ta juya baya dan bata kaunar ganin fuskar Anni, dariya tayi tace "na barku lafiya, A kofar fita ne tayi karo da Raliya, da sauri Anty Raly taja baya ta tsuguna ta gaida ta, mika hannu Anni tayi ta karbi Fadeel tace "Maigidan da babu cefane, muje daki na baka abincin tunda dai ni baka bani ba, dariya kawai Anty Raly tayi tace "Baffa na ciki, "yana wanka Anni ta bata amsa cike da kulawa, Daki ta wuce da Fadeel tana tunanin kalaman Rauda, ta rasa irin wannan kiyayyar da ake ma Suwaiba da 'yayanta, amma in shaa Allahu zata nuna musu itama tanada rawar takawa cikin rayuwar su Nadeeyah... waya ta dauka ta kira Papy tace "duk abin da yakeyi ya barshi yazo yau, da yake bashi da wani aiki ran monday sosai sai ya fara shirin tahowa..... Ita kuwa Raliya hankalinta ba karamin tashi yayi ba dan bata san ko kadan Nadeeyah ta kasance cikin danginsu, tasan zata sha wahala matuka, ta riga ta gama auno mata zamanta gurin Taheer wanda take da tabbacin zata ji dadi a gurinshi, a take ta kalli Mummy tace "gaskiya Mummy zanje in samu Daddy, dan Nadeeyah na bukatar wasu familyn bamu ba, nasan in ta auri little, ba karamin wahala zata sha ba, nan take Mummy ta gimtse farin cikinta dan duk tunaninta Raliya ta dawo hanya ne, ashe ita wani tunanin takeyi daban, nan suka shiga zaginta sosai har ta hassala ta tashi ta fita ta wuce gidan su..... Tana shiga gidan ta wuce dakin Musaddiq, a tsaye ta sameshi yana taje gashin kanshi yana yar waka, Ajiye Fadeel tayi a kasa tace "Zo ka zauna Diku ina son magana dakai, ajiye brush din hannunshi yayi ya dawo kusa da ita ya dauki fadeel suka zauna tare, kallonshi tayi sosai tace "baka isa aure ba kanina, in kana so ma zan iya tsuguna maka, Dan Allah ka hakura da Nadeeyah, she deserve better life, kasan halin da zaka sata in ka aureta mahaifiyarka bata so, ka hakura da ita, in har kana santa zaka so ganin ta cikin farin ciki, Dan Allah Diku kayi hakuri, ka barta tayi aure cikin wani familyn ba namu ba, kaga akwai wani makocinmu Taheer, inaga ma zaka ganeshi, wanda yazo nan suka samu matsala da Hilal, wallahi yana mutuwar kaunarta, kuma inada assurance akanshi, dan na dade da sanin shi da mahaifiyarshi, mu hadu ni da kai mu samar mata farin ciki mai daurewa kaji kanina... "Ajiye Fadeel yayi ya kamo hannunta yace "Anty Raly bakya sona ko? Kin fi son bare a kaina, yanzu har in furta ina son Nadeeyah kuce in hakura, ke da nayi tunanin zaki mara min baya ki taimakeni in samu abin da nake so, sai gashi kece kike iya cewa ni bazan bata farin ciki ba, kin fi son wani ya sameta bani ba

Table of Contents

Chapters

156 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156