Chapter 142
Chapter 142
basu sake ganinta ba... Da matsanancin kuka ta farka amma ta gaza furta komai dan daga ta buďe idonta zata maida ta rufe, hawaye ne kaďai bai yanke mata, ga azabar ciwo da take ji a hakarkarinta da hannunta, babu irin tambayar da Kamal baiyi mata ba taki kulashi sai ma kallo kawai da take binshi dashi, Dr Marliyya ce ta hanashi matsa mata domin gudun kar wani abu ya sameta, badan yaso ba ya kyaleta har suka fara shirin tafiya airport a motar asibitin..... **** Satin Taheer ďaya ya warke sosai kamar bai taba ciwo ba, saidai ita Nadeeyah kamar lokacin ciwon ya sameta domin ta jikkata sosai a jikinta, Sau huďu Kamal na zuwa gidan Alh Mukhtar sai ya samu a rufe, karshe karya yayi ma Taheer yace mishi sun bar kasar kwata kwata, sannan Number Raliya sam basa samu, haka gidanta sau uku mai gadin gidansu na zuwa bai samunta.. Da haka Taheer ya hakura ya maida hankalinshi kan nemawa Nadeeyah lafiya, duk wadannan abubuwan da yakeyi yana yinsu ne kawai dan Allah da kuma wani abu da yake ji a cikin jininshi game da Nadeeyah, amma bawai dan ta dawo mishi ba, tunda yaji labarin tana da ciki yasan lallai Nadeeyah tayi mishi nisan da bazai taba kamo ta ba, yasan duk inda mijinta yake yana nan yana nemanta, ya dauki alwashin sai ta warke sarai sannan zai maida ta gidan mijinta domin shine silar ciwonta... Watanta uku ta fara tafiya kaďan kaďan da taimakon su Amal da Aman domin Taheer ko rabar kusa da ita bayayi, shidai burinshi ta warke sosai, a kullum in ya tambayeta number wanda zata kira sai dai ta fashe mishi da kuka, samm bata da number Hafeez da shi zata bayar domin tasan yana can cikin tashin hankali, number Hilal ma in tayi yunkurin kawota kanta sai ta manta domin gargadin da su Raudha sukayi mata na su ba danginta bane.. wahalar da take sha kashi biyu ce, ga ta rabuwa da Musaddiq wacce tayi mata kiki kaka a cikin zuciya, ga kuma ta azabar ciwo wanda take tunanin babu ranar warkewa.... Cikinta na wata takwas da kwanaki ta warke sarai har tana iya hawa da sauka, babu wanda baiyi farin ciki ba a cikinsu, Anty Saude kula sosai take bata domin bata san wacece ita ba a lokacin, duk tunaninta wata ce daban wacce danta ya bige da mota yake taimaka mata... *Nadeeyah....* Ajiye ice cream din da take sha tayi tace "Na'am uncle, kujerar da ke fuskantar gadon da take ita ya zauna yace "Ina son yau mu kai karshen komai, kinga lafiya ta gama samuwa a gareki, ki faďa min inda yan uwanki da mijinki suke dan in maida ki, nasan yanzu hankalinsu na nan a tashe, a yanzu na daukeki tamkar kanwata ta jini, babu zancen soyayya a tsakaninmu.. bazan so inga wani naki ya cutu saboda ni ba, Dan Allah ki faďa min inda suke domin mu samu mu maida ke hankalinsu ya kwanta muma namu ya kwanta... Tunda ya fara maganar take kuka, "Kuka bazaiyi mana magani ba, ki faďamin matsalarki, in zan iya inyi miki maganinta, nasan bani da hurumin sanin damuwarki, dan Allah ki faďa min ko zan samu sukuni.... "Ya sakeni, Mijina ya sakeni, sun ce kar in sake zuwa inda suke, sunce bani da asali uncle.. bani da number wayar yayana, yana zaune a gombe, nasan shi kaďai ne yake cikin damuwa, sai Papy, sai kanwata Zainab.... Rashin asali na bazai barni in zauna cikin masu asali ba, nasan mahaifina mutumin kirki ne, ba barawo bane kamar yadda su---ka fadaaa.... runtse idonta tayi saboda yadda taji wani irin ciwo a bayanta... Share hawaye Taheer yayi bayan ya dawo daga shock din labarin sakin da ta bashi.. Mikewa yayi saboda yadda yaga tana cije baki, Subhanallah, lafy? Ya faďi da karfi bayan ya isa gurinta, mararta ta rike tana kokarin mikewa ta kasa, "Momm---- gani nan Tee, gani nan, ina jinku, duk abinda kuke faďi inaji, ashe dama itace Nadeeyar da ta yaudareka? "Momma plss help her, in muka dawo gida zamuyi maganar nan, kinsan sunce kar mu bari tayi labour, c.s zasuyi mata, hararashi tayi ta kamo Nadeeyah domin tasan ciwon nakuda bazata taba barinta cikinshi ba, amma tabbas lokacin barinta gidanta yayi..... Suna isa asibitin babu bata lokaci suka karbeta sukayi aune aunensu, bayan sun gama suka yankata suka ciro santalellen yaro wanda ya shiga cikin zuciyar Anty saude a ganin farko, farin ciki a gurin Taheer da Amal ba'a cewa komai, tun daga nan yaro ya fara ganin gata ta musamman domin yini yakeyi a hannu... Ranar Suna yaro yaci suna Mukhtar.. Hilal, shima dakyar Nadeeyah ta faďi dan da cewa tayi su sa da kansu, duk yadda Anty Saude taso ta nuna ma Nadeeyah bata kaunarta Taheer ya hana domin ya nusar da ita cewar ba laifinta bane... Akwai wani dare da tace mishi "Kar dai so kakeyi ka koma gurin bazawarar yarinyar nan, to wallahy Taheer in har tunaninka kenan gara ka janye dan bazan taba yarda su kashe min kai ba, karka yarda kace zaka dawo da ita cikin rayuwarka in ba haka ba sai nayi mugun saba maka, Shidai kwantar mata da hankali yayi bai bata amsa ba.... Watanta biyu da haihuwa Taheer ya fara lallabata su tafi gida, cikin kankanin lokaci ta yarda cike farin cikin sake ganin Musaddiq, tasan in yaga gudan jininshi zai dawo da ita su cigaba da rayuwarsu cikin kaunar juna, Saboda tsabar sonshi da takeyi ta manta da irin wulakancin da yayi mata shi da su Anty Raudha, tayi musu uzuri na ajizancin dan adam... Ganin yadda take farin ciki ya sanya Taheer soma shirin tafiyarta, ranar da suka tafi tare dasu Amal saida Anty saude tayi kewa, tayi matukar sabawa da Junior, komai ita ke mishi, tsanar da tayi wa Nadeeyah sam bata shafi danta ba, domin sau daya takk a rayuwarta ta taba samun opportunity din raino, sai gashi Allah ya kawo mata wani wanda kaddarashi tazo da ta tsani mahaifiyarshi, Soyayyar Taheer ce kadai tasa ta yarda Nadeeyah ta zauna har wadannan kwanaki, sai kuma soyayyar dan mala'ikan Allah..... Lagos Nigeria.. Da murnarta ta sauko a cikin motar haďe da lumshe idonta, memories din baya ya shiga yi mata yawo, kofar gate din ta kama ta tura, Mummunan gamon da tayi shi ya sanyata sakin kofar Garammmmmm.... ta koma motar su Taheer da sauri tana sheshshekar kuka... "Lafiya Nadeeyah? Menene, "Muje kawai uncle, zanyi maka bayani, tada motar yayi yajata ya fita daga layin ya wuce hotel din da ya sauka kwanakin baya, daki biyu ya kama da parlor, saida suka gama kimtsawa sannan ne ya tambayi Nadeeyah da har lokacin bata bar kuka ba... "Babu amfanin komawa garesu Uncle, sun manta dani, Musaddiq ya riga yayi aure, ya auri Faida wacce tayi sanadiyyar rabuwarmu, Dan Allah uncle karka matsamin in koma gurinsu, domin rayuwata bazata taba inganta ba, bazasu taba barina na zama independent ba, kowa a cikinsu ya manta dani, bani da sauran gatan da ya wuce in nemi ilimi, ku tafi kawai, zan shiga duniya neman ilimi har Allah yasa in dace da tsayuwa da kafafuwata... Tissue ya mika mata yace ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156