Skip to content

Chapter 1

Chapter 1

Zumuncinmu A Yau Book One Complete Hausa Novels 1 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

[04/12 09:41] Meela Adeel: 1⃣ ° *ZUMUNCINMU A YAU* ° By Aysha Ya'u Kurah *FIKRAH WRITERS ASSOCIATION* '''BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM''' Sadaukarwa ga mahaifi na kwarai *LATE ALHAJI YA'U KURAH* Allah SWT ya jikanka ya kai rahama kabarinka.. *SHIMFIDA* "Assalamu alaikum" Ta faďi karo na uku cikin siririyar muryarta, cikin ďaga murya taji ance, "Wai wacece ta ke ta kwaďa mana sallama ne haka?!" A hankali jikinta na rawa ta amsa. " Ni ce." "Tooo!! Sannu NI CE, me ya kawoki?" Cikin rawar murya ta ce "Mamma ce ta aikoni in kawo muku abinci." Daga cikin ďakin ta jiyo muryar dattijon wanda ya bata tabbacin shima yana ciki. "Toh ki ce an gode, je ki ďauki naira ashirin a saman tagar ďakina kiyi gaba." A hankali ta sauke ďankwalin da aka ďaure kayan a ciki ta kwance ta fito da sababbin samirun tuwo da miya ta cire ďankwalinta tace "Nagode BAFFA, Allah ya saka da alkhairi." Ta ďauki ashirin ďin ta fita cikin k'unan rai. A hanyar da zata sada ta da kofar gida taci karo da su Husna rik'e da manyan kuloli suna tafe suna nishi da kyar, rab'ewa tayi ta basu guri dan su wuce, suna karasowa dab da ita suka kwashe da dariya haďe da faďin "Nadiya roba-roba." Badariyya ta ajiye kular hannunta ta shafi kayan jikin Nadiya tace "Kaiii!! Wannan ba roba bace rai fess ce." Suka sake tintsirawa cikin shakiyanci suka ce "Su Nadiya bana an samu canji, daga atamfar roba zuwa shaddar roba." Cikin sanyin jiki tayi gaba tana jiyo ihunsu har suka shige cikin gidan. Tana fita tayi tafiyar minti biyar sannan ta isa titin da zata roki masu mota su ďauketa da naira ashirin ďin da aka bata, dan in tace zata tafi gida a kafa sai ta kai yamma saboda nisa, zuciyarta cike take da mamakin yadda zumuncin zamani ya koma, tun tana karama ta ga mahaifiyarta na fuskantar irin waďannan wulakancin saboda kasantuwarsu talakawa, sau tari takan tambayi mahaifiyarta anya Baffa ne ya haifeta kuwa? Acikin gidan kuwa, su Husna na shiga babu ko sallama suka faďa ďakin, zabura Baffa yayi ya sakko daga kan gado yana faďin. "Lale da matana, lale-lale." Badariyya ta faďa jikinshi tana faďin "Kakus, ina barka da Sallah na?" Cikin rawar jiki yasa hannu a aljihu ya ciro yan ďari biyar-biyar sababbi ya k'irga goma ya bata, yatsina fuska ta yi tace "Haba kakus, dubu biyar fa ka bani, ni gaskiya sunyi min kaďan Pizza kaďai zanci da su." Washe baki ya yi yace "To yar lele, an gama." Ya karo mata wasu biyar ďin ta mike a jikinshi babu ko godiya sai ma faďin "Ko kaifa, ai da na sake ka yanzun nan,,, Husna ta matsa kusa dashi tace " Saura ni kakus." Dubu goman itama ya bata saboda yasan sakon barka da sallan shi na tafe don tun safe y'arshi mafi soyuwa a gareshi ta kirashi tace zata aiko MUSADDIQ da sak'o, yasan sakon bai wuce na kuďi. "Ina yayanku? Ko ba tare kuka zo ba?" Baffa ya tambaya yana gyara aljihu. Badariyya tace "Ka ji kakus a kofar gidannan fa muka sameshi, yana fita muna shigowa dan ya riga Nadiya fita ma." Kallon mamaki yayi musu yace "Aiko bai shigo ba." Goggo ta rufe kular da ta bude ta ce "Kasani ko ya manta da wani abu ne?" "Hakane kuma." Ya faďi tare da basar da maganar. Nan suka hau hira da ciye ciye, sun ma manta da samirun tuwon da Nadiya ta kawo saboda sunsan babu wani abun arziki a ciki. Zaune take tayi tagumi tana jiran shigowar Nadiya dan tasan in Allah Ya yarda zata samu ko ďari biyar ce a gurin su Baffa na barka da sallah, Zainab ce ta taso rike da robar abinci tace "Mamma zan kara abinci." Janyota ta yi jikinta tace "Yi hakuri auta, yanzu Anti zata dawo har madara ma sai kisha in kinaso kinji?" Gyaďa kanta tayi cikin murna ta kurawa kofar gidan ido tana jiran b'ullowar yayarta. A gajiye ta shigo gidan ta nemi guri ta zauna tana maida numfashi, da sauri Zainab ta mike ta ďauko mata ruwa, karb'ar ruwan tayi haďe da janyota jikinta tace " Kin ci abinci?" D'aga mata kai tayi, "Eh naci amma ban koshi ba. Mamma ta ce zaki kawo kuďi a siyo min madara." A hankali ta ďago jajayen idanuwanta ta sauke kan mahaifiyarta, kallon tausawa juna sukayi sannan suka kau da kawunansu, cikin sark'ak'ak'k'iyar murya Nadiya tace "Mamma na kai musu, Baffa ya bani naira ashirin, ki tayani yi mishi godiya dan ya taimakamin, da a kafa zan dawo gida." Cikin b'oye b'acin rai Mamma tace "Kai madallah!! Allah ya biyashi da aljanna, gaskiya naji daďi, tashi maza kije kiyi sallah." Tana kokarin mikewa taji anyi sallama, juyowa tayi haďe da amsa sallamar, suna haďa ido tayi saurin kau da kanta, Mamma ta mike cike da murna tace "Maraba da Musaddiq, yanzu kake tafe?" "Eh Mamma ina wuni." "Haba dai daga tsaye?" Ta faďi haďe da shimfiďa dadduma. Zama yayi yana sosa k'eya suka gaisa sosai, kuďi ya zaro a aljihunshi kusan dubu dari biyu yace; "gashi inji mummy tace a kawo muku" bai jira jin me zata ce ba ya ajiye kuďin ya fice daga gidan da sauri dan yasan in ya daďe a gidan to asirinshi zai tonu.. Kasa tab'a kuďin tayi saboda firgici Kai anya Musaddiq yaji inda aka aikeshi da kyau kuwa? Wannan kyautar tayi yawa dan tsakanin ta da yar uwarta bai wuce kyautar dubu biyar, "Nadiya mik'o min wayar can" tace tana mai nuna ma nadiya wayar, da sauri ta ďauko ta mik'a mata. Hannu na rawa ta fara neman lambar yar uwarta, sai da ta kusa tsinkewa sannan ta ďaga cikin isa da tak'ama, murya na rawa Mamma tace "ina yini Hajiya" "lafiya" kadai tace murya can k'asa, bata damu da amsawar ba dan in da sabo ta Saba, sai ta cigaba "yanzu Musaddiq Ya kawo min sak'o shine nace bar..." Dakatar da ita tayi ta hanyar cewa "ina da abin yi Suwaiba nasan godiya kika kira kiyi, bakomai yiwa kai ne" tayi saurin kashe wayar, cikin mamaki ta ajiye wayar tana duban kuďin zuciyarta cike da farin cikin yar uwarta ta fara sanin muhimmancin zumunci.... Musaddiq na fita ya nufi motarshi ya kashe wayoyinshi ya ta da motar yayi gaba yana nazarin yadda zaiyi ya fahimtar da mahaifiyarshi da kakanninshi muhimmancin zumunci, A kullum yana mamakin yadda zumuncin zamanin yanzu ya zama sai in kana da kuďi, yana takaici matuka saboda irin wulak'ancin da Mamma suwaiba da ya'yanta ke fuskanta saboda kawai basu dashi, bashi da wani burin da ya wuce yaga kan zuri'arsu ya haďu, Mai shi ya taimaki mara shi, amma kullum abun k'ara lalacewa yakeyi saboda masu shi ďin basa taimakawa na jikinsu saidai na neman suna.. Mrs Tijjani Shattima... [04/12 09:42] Meela Adeel: 2⃣ °ZUMUNCINMU A YAU ° BY Aysha Ya'u Kurah "Nadiya amshi maza kira min yayanku, cike da murna ta karbi wayar ta latso number, Yana zaune ya kifa kanshi a wheel barrow yana tunanin ta inda zai fara, 'Dan kudin dakon da ya samu na Sallah shi ya had'a yayi ma kannenshi kayan sallah, ragowar ya ba mahaifiyarshi tayi abincin

Table of Contents

Chapters

156 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156