Skip to content

Chapter 14

Chapter 14

Zumuncinmu A Yau Book One Complete Hausa Novels 1 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

mishi da addua dan dama zuwanka bazai maido shi ba, yaja tsaki ya kashe wayar cike da takaicin halin son kai irin na Hafeez, (Dama Halin mutum na Kwarai ko kirki baya bayyana Sai yayi arziki).... Jiki na rawa Hafeez ya Mike, Ya dauki riga Ya sawa jikinshi, ko jiran farkarshi baiyi ba yayi waje yana jiyo muryarta tana kwala ihun kiranshi, inaaa bai ko waigo ba bare yayi tunanin komawa dakin Ya sallameta, Motarshi Henesy ya shiga ya tayar Ya fara gudun fitar hankali, hanyar Kaduna Ya dauka yana tafe yana kukan dana sani.... Takwas da rabi ya iso gidan lokacin ana kici kicin daukar gawar Malam Adamu, kuka ya fashe dashi da ya hada ido da mamma, Kure shi tayi da ido cike da mamaki da takaici, durkushewa yayi a gabanta yana kuka Mai Sosa zuciya, ganin da yayi za'a fitar da gawar ne Ya sanya shi mikewa da sauri ya nufi gawar, ya sa hannu zai karbi makarar a hannun Musaddiq yaji wata gigitacciyar tsawa a bayanshi, " IDAN KA KUSKURA TA TABA MAKARAR NAN BAZAN TABA YAFE MAKA BA,, Chakkk ya tsaida hannunshi ya waigo ya Kalli cikin idonta, kau da kanshi yayi da sauri saboda abun da ya gani a kwayar idon, soyayya mai dishi dishin kiyayyar bacin rai ya gani, "Kiyi Hakuri Suwaiba, mahaifinshi ne Ya zame mishi dole yayi rakiyar gawarshi, Sailuba matar malam Sada ta fadi tana share hawaye, "Ban hanashi rakiya ba, amma kar kazamin hannunshi ya kuskura ya taba min gawar miji, ta karashe hade da mai da kanta jikin bango tana gunshekar kuka, fitar da gawar akayi nan gidan ya sake gawraye da kukan mutane musamman makusantan gawar..... Mrs Tijjani Shattima [04/12 09:49] Meela Adeel: ZUMUNCINMU A YAU By Aysha Ya'u Kurah 1⃣5⃣ Ranar murna, mun cinye gasar BBC, proudly fikriansπŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ» Safiyya ciyaledi i ❀ u bebi..... FIKRAH WRITERS Bamu fi kowa ba, Amma da wuya ka samu irinmu, komai namu daban yake... Yin na Allah ne ba namu ba ALHAMDILILLAH..... "Ita Rayuwar nan da kake ganin ta Hafeezu kamar gari ne kaje wanda ba naka ba, kaga komai daren dadewa, komin dadin zaman garin nan dole ka barshi, saboda ba garin ka bane, bakunta ne ya kaika... TALAUCI jarrabawa ce babba wacce cinyeta yana da matukar wahala, duk karfin imaninka dole wata rana zuciyarka ta raurawa saboda zafin wannan jarabawar, Haka shima *ARZIKI* Jarabawa ce mai wuya kuma mai sauki ga wanda ya fi karfin zuciyarshi, ina mai baka shawara da kayi yaki da zuciyarka, ka tafiyar da arzikin da ya fara ziyartar hannunka ta hanyar da ya dace, domin akwai ranar da zakayi bayanin hanyar da ka kashe su, nayi maka farin ciki matuka na samun abin yi Allah ya sanya wannan arzikin ya zama sanadiyyar shigarka aljanna, Allah ya baka ikon sauke hakkinmu kafin mu bar duniyar nan domin Allah shi kadai yasan gawar fari.......... **** Durkushewa Hafeez yayi idonshi na hango murmushin fuskar mahaifinshi yayin da yake mishi wannan Nasihar, Wayyo Allah na, wayyo Baba, kaico na, kaicon rayuwata, ya Allah ka dauki raina nima in huta da wannan bakin cikin, wayyyyo baba..., dakyar mazan gurin suka iya dagashi saboda yadda ya cije yana buga kanshi a kasa, ku sakeni Dan Allah rayuwata bata da sauran amfani, dan Allah ku barni in mutu, Tsawa mai karfi Daddy ya daka mishi hade da ma mutanen alamu da su sake shi, hannu yasa a bakinshi yace "wallahi zan bata maka rai idan kayi yunkurin sake koda nishi kwakwkwara a gurin nan, in har so kakeyi ka nuna mana ka fita a musulunci to kaje daga wajen makabartar nan akwai rijiya ka fada, domin wannan duk haukan banza kakeyi, Nutsuwar da daddy yaga ta bayyana jikin Hafeez ne yasa shi ya sakko ya dafa shi yace "zai fi kyautuwa ka tsuguna kayi mishi addu'a domin a wannan gabar ita kadai yafi bukata a gurinka ba kuka ba, Hannun Daddy Hafeez ya kama yana kuka sosai, yace "in na rokeshi gafara zai ji ni ya yafe min, idon Daddy ya ciko da kwallar tausayi domin yana auno shine mahaifinshi ya mutu yana fushi dashi, rungumeshi yayi yace "nasan ya yafe maka Hafeez kai dai ka dage mishi da addu'a da sadaka su kadai zasu nuna zallar soyayyarka a gareshi.... limamin da ya jagoranci sallar gawar ne yayi addu'oi hade da nasihohi, sannan duk suka juya suka bar makabartar suna masu yi ma mamacin fatan dacewa...... CYPRUS Tsaye yake jikin wagegen bud'ad'd'en windon dakinshi, iska na kada labulen windon yana taba gefen fuskarshi, hannunshi rike da daya daga cikin zanen, ya kura mishi jajayen idanuwanshi, zuciyarshi a karye take a wannan lokacin, wayarshi ya dauko ya sake kiran Musaddiq, wannan karan ma bai daga ba, wurgi yayi da wayar hade da dafe kanshi yana mai jin radadi a cikin zuciyarshi, komawa gado yayi ya kwanta ruf da ciki, shi kanshi a yawancin lokuta yana mamakin yadda Nadeeyah ke makale a cikin dukkan kewayen zuciyarshi, tun baisan kalmar So ba yake jinta a ranshi, tun ganin da yayi mata lokacin da ita kanta bata san kanta ba, yana mamakin da a kullum bashi da zanen da ya wuce nata, kullum kara auno fuskarta yake da yanayin girmanta, gyara kwanciya yayi yanata juye juye, a kunnenshi akayi kiran sallar asuba, mikewa yayi jiki ba kwari yayi alwala ya fito dan zuwa masallaci, Anty Reemah da Papa ya hango zaune a parlon kasa sunyi jugum jugum cike da damuwa, da sauri ya sakko daga sama har yana bige kafarshi a matakalar karshe, baibi takai ba ya karasa gurinsu, Mum, Papa, "meya faru na ganku haka? Ya tambaya yana mai tsugunawa kusa da mahaifiyarshi, uhhmm Anty Reemah tace, sannan ta cigaba da cewa, "mijin Mama Suwaiba ne ya rasu cikin dare, yanzu Raliya ta kirani ta fadamin, "innalillahi wa inna ilaihir rajiun, kalmar da Hilal keta maimatawa kenan a cikin zuciyarshi, tunanin shi ya tafi gun sanin halin da Nadeeyah take ciki, zungurinshi Anty Reemah tayi tace "bakaji an tada Sallah bane, mikewa yayi a firgice ya bi bayan Papa da yake kokarin fita daga kofar palon..... Kuka sosai Badar takeyi hannunta rike da kanta tana shashsheka, saboda tsabar kuncin da take ciki bata san gari har ya waye ba, rana ce ta kyallaro ta jikin dan tsagin labulen ta kashe mata ido, a daidai lokacin ta mike da niyyar wucewa daki tayi tozali da madubin parlon, wani irin kamanni ta gani a tattare da ita mai wuyar fassaruwa, fuskar nan tayi jawur hancin yayi suntum saboda kukan da tasha, wani kukan ta sake fashewa dashi hade da rugawa cikin daki, cikin kunan rai ta fada bayi ta kunna pampo tana watsa ruwa a fuskarta tana magana cikin kuka, "Nadeeyah bazan taba kyaleki ba, kamar yadda kikayi min ruining wannan ranar sai nayi ruining life dinki gaba dayanta, bazan taba iya tuna rabon da na zubda hawaye ba, amma yau na zubar sanadiyar ki, na tsaneki, na tsaneki Nadeeyah!! ta karashe hade da kifa kanta jikin bangon bayin........ Mrs tijjani shattima..... [04/12 09:49] Meela Adeel: ZUMUNCINMU A YAU By Aysha Ya'u Kurah 1⃣6⃣ A yau ne malam Adamu ya cika kwana bakwai da mutuwa, in kaga Nadeeyah da mamanta a wannan lokacin sai ka

Table of Contents

Chapters

156 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156