Chapter 119
Chapter 119
a cikinsu ya tanka ta dan anyi mata mai kankat.... Dakinta ta shiga ta tattare kayanta da gwalagwalanta ta fice ta bar mishi gidanshi.... ********* Saida Musaddiq ya kwana uku a asibiti, lokacin ya farfaďo yana gane duk wanda ke kanshi, babu abinda yakeyi daga kallon su Daddy sai bacci in allurai sun ratsashi, tunda ya farfaďo kamar an tafi da hawayen da yakeyi, magana ba ya yinta ko kadan sai dai in sunyi ya bisu da ido, Da support yake zuwa yayi alwala da wanka saboda jikinshi samm babu kwari, a wannan lokacin ne aka yarda kowa yazo ya ganshi dan jikinshi yayi kyau matuka, abinci da ya zamo aminin Musaddiq yanzu ya maidashi babban makiyinshi domin sai anyi bacin rai kafin ya yarda yayi cokali daya, kowa burinshi ya farantawa Musaddiq dan dai kawai su samu ya saki jikinshi ya cigaba da Mu'amala kamar yadda ya saba, Zainab da Ruwaida ne samm ba'a yarda suje inda yake ba saboda har yanzu bakinsu bai bar tambayar inda Nadeeyah take ba... A cikin kwanan shi na bakwai aka sallameshi, har wannan lokacin babu wanda yayi mishi maganar inda Nadeeyah take, shidai yafi bada an binneta shiyasa ma baiyi yunkurin tambaya ba, dan kar ya sake tayar wa da hankalin su Daddy, Suma kuma har lokacin basu bar neman Nadeeyah ba, dan har police station suka kai, tunda Allah baiyi sunga gawarta ba sunsan tabbas tana raye, in da rai wata rana dole su haďu in shaa Allah.... **** "Karka damu Daddy, i will take care of myself, Kallon Zubair Daddy yayi yace "Dan Allah ka kula dashi, karka barshi ya dinga tunani, ka---- "Nace i will take care of myself, i'm nt a kid, yadda yayi maganar da tsawa ya sanya Anty Reemah matsowa kusa dashi, Dafa kafaďunshi tayi tace "Laifi ne dan ance a kula dakai, tafiyar nan ance ka hakura da yinta, baka da lafiya, ka dage sai kayi ta, dole a nemi mai kula da kai.. Hannunta ya cire a kafadunshi ya dauki brief case haďe da kallon Daddy yace "kayi min addu'a in shaa Allah babu abinda zai sameni, tunani shi ke yin kanshi, with ur Du'a komai zai daidaita, Murmushi Daddy yayi yace "In shaa Allah son, Allah ya tsare ku ya bada sa'ar abinda aka je nema... Gurin da Hilal ya ke tsaye Musaddiq ya kalla, suna haďa ido ya karaso inda yake ya rungumeshi, rashin walwalar Musaddiq na matukar damunshi, babu abinda yake sanya shi farin ciki, dariya kanta ya manta yadda akeyinta, domin wani sashi na yin dariyarshi ya mutu a ranar da ya rasa Nadeeyah, "Take care kaji, in na gama project zanzo Singapore inyi keeping dinka company, gyaďa kai kawai Musaddiq yayi suka fita, dukkansu yan parlon kowa na mishi fatan alkhairi haďe da adduar Allah ya kara sanya farin ciki a cikin zuciyarshi...... Mutum kamar Musaddiq wanda baisan menene bacin rai ko fushi ba a ganshi a haka dole hankalin makusantanshi ya tashi dan sun san ba karamin abu bane yake sanya Musaddiq fushi, Daddy yaso yayi quiting aikin da yakeyi amma Musaddiq sam yaki, saboda shi kadai ne yake ganin zai dabe mishi kewa, badan Daddy yaso ba haka nan ya yarda dan yaso ya zauna tare dashi har ya samu sassauci a zuciyarshi... Duk wani shiri na barin gidan su Badariyya sunyi domin abun kawai da ya rage musu shine su tarwatsa kuttun tsafin Bokan gaba daya, layar dake bakinsu suka matsa dan bacewa suka ji su har lokacin a gurin, cike da tashin hankali suka kalli juna haďe da sake latsata, hankalinsu bai kara tashi ba sai da sukaji damka a bayansu, waigowa sukayi dan ganin mai ganinsu a wannan lokacin da suka san sunyi komai dan bacewa ganin mutanen gidan, Yareemah Suhail suka gani gefenshi kuma duk wasu kulli da sukayi ne wanda ya warwaresu ya sanya musu wuta, Dariya sosai yayi yace "kun taba jin labarin wanda ya shigo gidannan ya fita shi kadai, shafa kanshi yayi ya cigaba da cewa "Badariyya nasan da hatsabibancinki kika zo, sai kuma kika kara da na Marakisiyya, da nice ke zanyi biyayya domin cikin biyayyar wata rana in da rabo ina iya kaiki gida ki ga yan uwanki har kiyi musu sati in kinaso, amma tunda kin biyewa wannan hatsabibiyar sai kuyi ta zama da taurin kanku, duk ranar da kuka ga kun amince da zaman gidan nan sai kuyi biyayya, in kuna da rabo sai kuga na kaiku gida dan ziyara, yana kaiwa nan yayi wurgi dasu cikin wani dakin da basu san da zamanshi a gidan ba.. Kukan jini ne kadai Badariyya batayi ba dan ta ga koshi ya rikide ya zame mata kwanan yunwa, tayi shirin komawa ta shiga Musaddiq sosai har ta kai ga aurenshi hankali kwance ba tare da kowa ya zargeta ba... Taci kuka sosai har saida faďa mai karfi ya kacame musu ita da Marakisiyya, faďan da ya sanya zubewar hakoran Badariyya na gaba, dan Sosai Marakisiyya tafi karfinta..... *6months later...* ******* Radiya.. bani dubu biyu zan baki gobe in Reemah ta turo min, Buďe baki Radiya tayi tace "ina na gansu Mummy, nawa nake binki? kusan 30k fa, ina zanga dubu biyu yanzu, Raudha dake kwance akan kujera tace "Ki bata mana, jiya fa kika siyar da zobenki, meye a ciki dan kin bata, kika san abunda zatayi dashi... To munafuka, da na siyar da zoben baki faďa mata abun da nayi dashi ba, saida zoben kaďai kika iya faďa mata, ni fa na gaji da wannan rayuwar, duk wani abu nawa ya kare, kullum ni kenan cikin bada kudi sai kace wata banki, na gaji wallahi ta mike fuuuu tayi cikin daki.... Share zufa Mummy tayi haďe ficewa daga dakin tana mamakin hali irin na Radiya, kwallar da ta fito a idanunta ta share haďe da yin tagumi tana tunanin a wani hali Musaddiq yake yanzu, rabon ta da ta sashi a ido tun daren da suka fita nemo Nadeeyah, ko sau ďaya bai taba tunanin nemanta ba, ta sani ta bata mishi matuka, a yanzu dana sani takeyi sosai na biye wa san zuciyarta da tayi, kawayenta da a da suke like mata kaff dinsu sun guje ta saboda halin da take ciki, Nairah dari yanzu mugun sha'awa take bata, ga Baffa ya dauke Anni ya maida ita gidan da Papy ya siya saboda ya dinga sauka in yazo, ko ganinshi basa yi a gidan saboda a cewarshi basa girmama matarshi, Daddy kuwa ko ta kirashi bata samu dan ya sanyata a black list, samm bata samunshi, koda text tayi mishi saidai ya dawo mata dan ko kusa baya isa gurinshi... Shigowar Rilwanu da kayan abinci shi ya katse mata tunanin da takeyi, da murnarta ta mike tace "Wadannan kayan daga ina? "Alhj karami ne ya zo shi ya sauke su, yana waje nasan yanzu zai shigo, Hijab ta dauko da sauri jiki na rawa ta fita tarbo Papy... Kuka wiwi ta dinga mishi tana neman gafararshi, rike mata hannu yayi yace "Haba, wallahi ban taba rike ki ba, we are all humans, we make mistakes, ni waye da bazan yafe miki ba, komai ya wuce wallahi, ina Goggo? Hmmm ta tafi kauye tun shekaran jiya, "Nace
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156