Chapter 152
Chapter 152
zuciya wata nurse tayi taja zani ta rufeta ta kalli Mummy tace "Saidai hakuri, ta mutu!! Bazan mutu ba Goggo ta faďi a wahalce haďe da yayewa ta damki hannun nurse din, irin jinin da ya zuba a jikin Goggo ya isa dukkan karfinta ya kare, A tsorace Nurse din ta fincike hannunta taja da baya da sauri, dan minti ďaya baya tabbas taga mutuwa a tare da Goggo.. Sunan Mummy ta fara kira a hankali saboda duhu ya fara ziyartar ganinta, daga nesa Mummy ta amsa dan tsabar tsoron irin rayuwar da Goggo ta ďibo, gaba ďaya yanayinta ya canza daga farar bafulatana wacce tsufa ya tattare fatanta zuwa wani irin yanayi na ban tsoro, jinin dake zuba a jikinta gaba ďaya ya kafe dan babu ragowarshi a jikinta, karfaffiyar zuciyarta wacce rashin imani ya kesashar ita kadai ke aiki a jikinta... Babu wanda a dakin bai bata mutuwa ba saboda irin ukubar da tasha kuma take kan sha, a lokacin nan mutane da dama sun sake tsorata da Allah domin shine ke da ikon yin wannan abun al'ajabi,, Sake kiran sunan Mummy Goggo tayi a karo na uku, a ďarare ta matso kusa da ita tace "Gani, "Yanzu duk wannan azabar da nake ciki bazaki iya zuwa ki kiramin wani bokan ya fidda ni ba, duk abubuwan da nayi a baya saboda ku nayi shi, amma ni yanzu abu ďaya da zaki min in fita daga wannan azabar bazaki iya ba.... babu wanda ya fahimci abinda Goggon ke faďa sai Mummy domin ita kadai ce a gefenta, Cike da damuwa Mummy tace "Shin har yanzu baki saduda kin san Allah daya bane? Har yanzu kina tunanin akwai wanda ya isa ya hanaka yin aure bare ya hanaka mutuwa, lallai kuwa in dai wannan azabar da kika sha ta tsayin watanni bata nunar miki hanyar Allah ba babu wata azaba da zata maidaki daidai, Mutuwarki itace alheri ga dukkan yan uwa musulmi, domin ke ďin anno----- wata damka Goggo ta kai mata wacce idonta bai nunar mata gefen da ta kaita ba saboda duhun da ya fara rufesu, a hanzarce Mummy ta mike haďe da fincikewa wanda hakan yayi sanadiyyar kai Goggo kasa, zafin faďuwar ya sanyata sakin ihun karshe wanda daga shi bata sake cewa komai ba sai fisga da jikinta yakeyi yana dukan gadon.. A wannan lokacin mai daukar rai ya ziyarci tsohuwa Goggo wacce tayi kisan ban mamaki kuma take tsoron mutuwar kanta, a lokacin Goggo ta dandanin azabar da matattun da suka mutu a sanadinta suka dandana, babu rayuwar da bata tunano ba kafin ganinta ya dauke baki ďaya.... *(Kullu nafsin za'ikatul maut,, Duk mai rai sai ya dandani mutuwa)*... *Anzo a banza an koma a wofi...* Furucin wata tsohuwa ne doki kunnen Mummy dake zaune tana kuka tana jiran azo daukar gawar Goggo, Wani sabon kukan ne yazo mata tanata adduar nemawa mahaifiyarta sassaucin ubangiji, *(Allah ghafuru raheem*).... Mutuwar Goggo ta taba makusantanta, domin ko babu komai rai daraja gareshi duk ko irin bakin halin wannan ran.. A ranar da akayi sadakar uku Baffa yasa aka kwashe kayan Goggo aka kaiwa tsofaffin mabaratan bakin titi, kayan kudinta ne kadai ya bawa Goggo domin itace magajiyarta shi kuwa a bangarenshi yace baya bukatar komai nata domin ta fita a sahun matarshi kafin rai yayi halinsa... *********** Har gurin mota Daddy ya raka su Anty Saude domin hirar da ta jashi da shi ba wacce zasu katseta bace, Cike da damuwa ita ta katse hirar bayan ta ajiye jakarta a bayan mota, "Ya jikin Musaddiq? Hope da sauki, Hafeez ke faďa mana jiya ashe bai ji dadi ba kwana biyu, Cike da basarwa Daddy yace "Alhamdulillah, jiki kam da sauki sosai, dan har ya fita ma yau.. "To mashaa Allah Anty Saude tace cike da farin ciki, jikanka dai yana neman haddasa min fitina, daga yaga zamu fita zai fara kuka saidai a barshi a gida, yanzu dai na barsu da Taheer zasu zo zuwa anjima suyi muku gaisuwa sai yayi dabara ya barshi can gurin Nadeeyah, "Murmushin dattaku Daddy yayi wanda ya tuno mata da samartakarshi yace "Babu komai, nasan rashin sabo ne, wata rana ba zaiso ya bar gidana ba, "In shaa Allah Anty Saude ta faďi tana dariya, motar ta shiga tana faďin "Kyan alkawari dai Kyari, ina nan ina jiranka,, Baki da matsala, in shaa Allahu gobe zanzo ai ni na faďa.. ya faďi cike da jaddadawa... "To saika zo bari mu wuce Allah ya kara hakuri, Ameen Daddy ya faďi haďe da rufe kofar motar... A tare motar su shigo cikin katafaren gidan, sai da kowacce tayi parking a mazauninta sannan suka fito rike da kaya niki niki.. Cike da ladabi Kamal ya gaisheta bayan ta sakko daga cikin motar, Amsawa tayi hannunta nakan kayan tace "Har kun dawo? Allah yasa dai bakuyi shirme a list dinnan ba, Girgiza kai Taheer yayi cike da gajiya yace "komai muyi momma, muje ciki ki gani, My dear kawo ledar nan ya karashe yana duban Junior dake rike da leda yana ja, "Noo Daddy, muje kaima naka akwai nauyi, daya daga cikin mai musu aiki ne ya karaso ya karbi dukkan kayan harda na hannun junior, sai a lokacin suka saki ajiyar zuciya suka wuce ciki ko wanne na dauke da gajiyar kasuwa data zaban kaya.. Buďe kayayyakin Shareefah takeyi tana duban Anty Saude dake cire warwarayen hannunta tana kallon kanta a mudubi, "Kaya Machaa Allah Saude, yanzu abu kadan ya rage a gama, sai kuma su *plaķiù'oòl..* Nasa Raahilar masu gari ta siyo ta taho dasu, naso ayi bikin nan a can Agadez saboda a nuna su ga dangi kuma ayi biki kashi biyu, na Yareemah mai jiran gado da kuma daurin auren tunda abun duk phàmèè ne, to Taheer ya hana yace dole ayi shi anan, amma ki faďa mishi daga an daura zamu wuce can sai ayi biki domin bazai yiwu bikin yazo min a yar karo ba alhali dukkansu nawa ne, dole a buga tambura agadez ta dauki bikin jinina, shakikai na wadanda zan bugi kirji ince su din nawa ne... Warwaron karshe Anty Saude ta zare ta dawo kusa da Shareefah, "Karki damu yar uwa, yin bikin a nan ya zama dole, bayan an daura sai kiyi yadda kike so babu wanda zai hana, kwana nawa ya rage, kedai kisa a fara shirye shirye a can kafin isowarmu.. Wannan ba matsala bane, biki kam za'ayi shi wanda ba'a taba yin irinshi ba a tarihi.. Shareefah ta faďi zuciyarta cike fal da murna... ********** Tsakurar indomien dake gabanta takeyi a hankali tana kaita baki, tunanin abubuwa da dama sun cika zuciyarta, ga tausayin halin da Musaddiq yake ciki ga kuma tausayin Taheer wanda ya sallamar da dukkan hope dinshi a kanta, tsaki tayi a hankali ta ture indomien gefe dan dama cinta takeyi badan daďi ba sai dan yunwar dake neman yi mata illah... "Nadeeyah in kin gama Daddy yace kizo.. kafin ta juyo ta ba Husnah amsa har ta bacewa ganinta, ruwa kaďan ta kurba ta gyara gyalen dake daure a kanta ta nufi parlon kamar wacce kwai ya fashewa a ciki... Cikin dariyar karfin hali Daddy yace "Amarya taho nan ki zauna mana, Cike da karyewar zuciya ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156