Skip to content

Chapter 113

Chapter 113

Zumuncinmu A Yau Book One Complete Hausa Novels 1 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

talatin ce ta kaishi airport din saboda gudun da yayi, gaisawa sukayi Hilal ya faďa motar suka nufi hanyar gidan Musaddiq.... Wani lungu Nadeeyah ta zauna a nesa da layinsu kusa da 3stars luxury Hotel taci kukanta ma'ishi, wanda har ya saukar mata da zazzabi, wayarta da zata kira Papy ma sun kwace mata, haka suka tasota a gaba ba ko sisi tare da sharadin kar ta nemi Daddy tunda ba ubanta bane shi, akwatinta ta dauka lokacin gari yayi duhu ta fara tafiya tana neman abun hawan da zai taimaketa ya kaita tashar da zata samu a kaita Gombe.... "Kusan fifty seven million Momma, but zasu cire 5m na workers sai 5m a each shareholders na gwamnati, yanzu ina driving ne kuma is late gobe da safe zanje bank inyi transferring zuwa acc dina, hope kina kula da kanki?, gyara kwanciyarta tayi cike da jindadi tace "sosai ma, ga kuma wasu kudin sun shigo na sake kula da kaina da kai, Allah dai ya jikan Abbanka, "Ameen Momma, na kusa karasawa masauki in shaa Allah, su Aman ma sun shigo lagos gobe zamu taho tare, "To Mashaa Allah, sai kun zo Allah yayi maka albarka, take care, "In shaa Allah bye.. Ajiye wayar yayi ya cigaba da tuki hankali kwance, yana karya sharp bend din da zai sadashi da hotel din ya fara latsa hon saboda ganin mace na tafiya a saitin inda yake bata waige bare taga abunda ke bayanta, Duk irin kokarin da yayi brake din ya taku ya kasa dan ya kure da yawa, sai da yayi mata mummunan buguwa ya daki ginin gabanta kaďan sannan motar ta tsaya, kwantar da kanshi kan sitiyari yayi yana maida numfashi sannan ne hankalinshi ya dawo inda mutane ke ihu suna tururuwa, buďe motar yayi ya fito a gigice ya nufi inda ya buge matar, dakyar ya iya kutsawa yana faďin ku taimakeni in kaita asibiti dan Allah, sam bai kula da fuskar ba shidai ya kinkimeta iya karfinshi ya nufi motar da wani mutum ya bude da niyyar taimakawa..... Subhanallah.... me ya faru a can gurin? Hilal ya faďi haďe da lekowa ta window, wani saurayi ya tambaya abinda ke faruwa, "Wallahi wani ne ya yayi accident har ya buge wata yarinya, kaii abun ba kyau yarinyar ta bugu, dakyar in zata rayu, "Ayya, Hilal ya faďi haďe da maida kanshi cikin motar, Allah ya kyauta gaba, muje Zubair, jan motar Zubair yayi suna addu'ar Allah ya tsare dukkan musulmin duniya.... Mrs Tijjani Shattima.... [25/04 9:12 PM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 6⃣3⃣ By *Aysha Ya'u kurah* Ohhh Musaddiq... pick my call, Abbati ya faďi haďe da buga hannunshi jikin siyitiyari... Wayar Raudha dake cikin motarshi ya gani bayan ya idar da Sallar magriba, abubuwan da ya gani a wayar su suka razana shi matuka, "How can some1 be so selfish, meye laifin Nadeeyah da suke shirin tarwatsa rayuwarta haka, dama tun jiya da daddare yaga take takenta, in aka kirata a waya sai tace text me, duk iya hangenshi bai hango abinda suke kullawa har ya kai haka ba, in har Raudha zata iya kulla irin wannan abun ga ďan uwanta da matarshi wacce itama ta zamto yar uwa a gareta, to wa zatayi sparing, wani irin kyamarta yake ji a cikin zuciyarshi, bazai taba son 'yayanshi su kasance tare da ita da wannan mugun halin nata ba, da yaga Musaddiq baida niyyar daukar wayarshi sai ya kira wani abokinshi akan su ajiye mishi ticket din zuwa katsina, gara ya dauke 'yayanshi ya maida su gurin iyayenshi, ita kuma Raudha ya riga ya gama yanke hukuncin da zai zartar akanta, duk wanda yace tukunyar wani bazata tafasa ba to tasa ko huruwa bazata yi ba, kafin Musaddiq ya saki Nadeeyah shi zai rigashi sakinta, may be ta shiga hankalinta, Shi laifin Daddy ma yake gani, ya za'ayi ya bar 'yaya haka sakaka babu kwaba ba komai, har mahaiifiyarsu nada ikon zuwa a haďu a bata rayuwar wata da ita, "tirrr.. ya zama dole ya rabu da 'yar mace domin dama mugun hakuri yakeyi da ita.... Tada motarshi yayi ya nufi gidan Musaddiq dan ya sameshi ya fita hakkinshi akan abun da ya sani kafin hak'an su ya cimma ruwa.... *its too late....* Da..dd..y......, ya faďi cikin shashshekar kuka haďe da zuwan wani kukan mai karfin gaske... Gaban Daddy ne ya faďi ya mike daga kan daddumar da yake haďe da fita a masallacin gaba daya, "Me ya faru Saaaadiq, Musaddiq bai bashi amsa ba sai kukan da yake tayi karamar yaron goye, kuka ne mai cin zuciya wanda ya karya zuciyar Daddy ya sanya shi neman guri a dakalin masallacin ya zauna, saida ya barshi yayi kukan sosai ba tare da ya katseshi ba sannan yace "Bana san sakarcin banza, ya isheni haka, i have heard enough, faďa min abin da yake damunka? "Nadeeyah... sun raba ni da Nadeeyah.. Mummy da su Anty Radiya sun rabamu Daddy, na saketa da bakina Daddy, dan Allah Daddy ka dawo min da ita, i can't live... i can't... ya karashe cikin kuka mai tsanani... "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun kawai Daddy yake faďi cikin zuciyarshi, ko a mafarki bai taba kawo abun da zai kai Mummy lagos kenan ba, duk tunaninshi bai kai nan ba, tunaninshi kawai taje ta zuga danta ya auri wacce take so ne, ya barta tayi kidanta ne in maganar tazo gurinshi tunda shine wakili ya barta ta taka rawarta, Ajiyar zuciya yayi yace "Kar ka bar Nadeeyah ta je ko ina, ku shirya gobe tun safe taho gida, nasan matakin da zan dauka... "Sun koreta Daddy, ban san inda zan ganta ba, na duba ko ina ban ganta ba.. Duk da Daddy bai iya fushi da Musaddiq, a wannan lokacin saida yayi mishi gigitacciyar tsawa haďe da mishi kashedin lallai duk inda take ya nemota, in ba haka ba wallahi sai yayi mummunan saba mishi, kalmar da Daddy ya faďa mishi a karshe ita ta sake assasasa hawayen idonshi, "YOU A LOOSER, U DOS'NT DESERVE A SPECIAL SOUL LIKE NADEEYAH.... Yana jiyo kalaman da Daddy ke faďa mishi wanda yasan shima ba'a cikin hayyacinshi yake faďinsu, bai iya furta mishi komai ba dan yasan ya tafka babban kuskuren da ya cancanci fin wannan zagin... Kasa tashi a gurin Daddy yayi har aka gama wa'azin bayan sallar isha'i wanda suke saurara a kullum, mutanen dake fitowa a cikin masallacin ma daidai yake kallonsu, yana ganin kamar duk matsalolin duniya a gidanshi aka tarasu, bai san lokacin da hawaye ke bin idonshi ba, "Yaso Suwaiba saboda komai nata ya zamo abun so ga kowani da namiji, yana ganin rashinta shine mafarin shigar rayuwarshi cikin kowani irin kalubale... Ya nemawa danshi auren yar da yake jin sonta fiye da 'yayan da ya haifa a cikinsa, saboda danshi ya samu zuri'a daga gareta kuma rayuwarshi ta inganta, sun rabashi da ita, same mutanen da dalilinsu ya hanashi samun abun da yakeso a baya sune dai har yanzu dalilinsu zai kuma hana danshi abun da yake so, *Tarihi ya maimaita kanshi*... Hukuncin da zuciyarshi ta gamsu dashi shi ya yanke ba tare da duba tsufa da tarin yaran da suka tara dashi ba, dakyar ya iya mikewa

Table of Contents

Chapters

156 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156