Chapter 6
Chapter 6
yi Anty Reemah tace "kyaleta kinji na nawa ne duka, cike da Jin kunya tace "na dari takwas da hamsin ne, sai na dari ribar Mai shago, Anty Reemah tayi murmushi tace duka dari tara da hamsin kenan ko, girgiza kai Nadiya tayi tace ki bani dari takwas kawai, dubu daya ta zaro a Jakarta tace to gashi ki dauki dari takwas na tuwon Madara canjin ki siyo takalmi ki cire wannan hadi da Bautan kinji yar kasuwa, rufe fuskarta tayi tana dariya tace nagode sosai Allah ya saka da alkhairi, Ameen anty Reemah tace ta mikewa Hinad tuwon madarar suka karasa cikin gidan tare da Musaddiq,, Hilal suka tarar a tsaye mamma na mishi hira yana fadin umm in na a'a ne yace um um, mamma na ganin su ta karaso tana musu oyoyo, a dadduma suka zauna ta kawo musu ruwa, duk ta rasa inda zata sa ranta saboda dadin yau nata yazo inda take, me za'a dafa muku tayi ta fada kamar zata fado kansu saboda murna, Anty Reemah tace wallhy a koshe muke mamma daga gurin partyn Musaddiq muke nace bari mu biyo mu gaisheki mu kuma yi miki sallama dan inaga jibi zan koma, Ayya mamma ta fadi tana Mai zaunawa kusa da ita, har zaki koma Antyn Yara, Reemah tace eh zamu koma tare da musaddiq na sama mishi makaranta a can,, Allah sarki musaddiq zaka bamu kewa ashe, to Allah yasa ka je ka fara a sa'a, Ameen musaddiq yace yana Sosa keya, da sauri ta dawo gidan da sabon silifas a kafarta da ledar madara da suga, ajiyewa tayi a kofar kitchen tace sannunku, mamma ta kalleta kallon tuhuma tace a Ina kika samo sabon takalmi? , canji ta ciro a cikin aljihunta ta mika ma mamma tace Anty ce ta siye duka ta kuma bani kudin takalmi, shine dan sakarci baki shigo kin fada min ba mamma ta fadi rai a bace, Anty Reemah tace "kiyi hakuri mamma ni nace tayi sauri ta siyo takalmi, mamma tayi murmushi tace to mun gode fa Allah ya saka da alkhairi, Ameen anty Reemah tace tana kallon Nadiya da ke rabe tana wasa da hijabinta, ni ko mamma wace makaranta Nadiya ke Zuwa? Mamma ta yi murmushi tace ta zana jarabawar aji shida zata cigaba da makarantar gaba in shaa Allah, to ai mamma naga har an kusa gama third term wace makaranta kuke neman mata? , mamma ta kalli gefen da Nadiya take tace makarantar kwana ta Queen Amina dake kakuri, to har yanzu bata samu bane? Reemah ta tambaya cike da damuwa, muna ta kokarin har hada abin da zata tafi dashi ne mamma ta fadi cike da Jin kunya, Anty Reemah tayi ajiyar zuciya tace mamma karatun diya mace nada matukar amfani, Dan Allah Kar ayi wasa da ita first term din nan da za mu shiga, ki bar batun queen Amina, zan ma abban Hilal magana zai sa a bata admission a fgc malali in shaa Allah, sannan ki turo min hafiz inason ganinshi gobe kafin muje gidan Baffa, Kasa rufe baki mamma tayi saboda murna, share hawayen farin ciki ta shiga yi tana kallon Nadiya dake ta dariya, kai gaskiya nagode Antyn yara, Allah ya biyaki da aljanna, nagode sosai, anty Reemah ta mike tana fadin haba mamma me akayi ai duk daya ne, Dan Allah ki daina min godiya, Godiya ta zama dole Reemah mamma ta fadi tana rike baki, kedai kawai Allah shine zai saka miki, Ameen anty Reemah tace ta fito da dubu biyar a jaka ta bawa Nadiya tace wannan na auta ne in ta tashi kice mata gashi inji ni kinji, Nadiya ta karba ta shiga godiya hade da bayyana kyawawan hakoranta, har gurin Mota suka raka su suna ta godiya kamar bakin su zai tsinke, musaddiq mamma ta kalla tace "me kake so in kawo maka ka tafi dashi? , murmushi yayi yace koma meye mamma nagode, mamma tace to an gama dan albarka.. Hon Hilal yayi yace muje ko mum, bata bashi amsa ba sai ma harara da ta bishi dashi, mamma tayi dariya tace Hilal Allah ya kiyaye hanya ka gaida abbanka kaji, zaiji kawai Hilal yace ya tada motar sukayi gaba..... Mrs Tijjani Shattima...... [04/12 09:45] Meela Adeel: 8⃣ °ZUMUNCINMU A YAU ° By Aysha Ya'u Kurah Washe gari karfe 8 a gidan Anty Reemah tayi wa Hafiz, a kitchen ya sameta tare da Yan aikinta suna ta aikin abun karyawa, da fara'arta ta tarbeshi tasa ya wuce parlor, sai da ta kammala komai tasa shi ya karya sannan ta dawo gurinshi, Wace sana'a kakeyi? Tambayar da ta fara yi mishi kenan, kanshi a kasa yace "dako nakeyi da wheelbarrow, wheelbarrown naka ne? Ta sake jefo mishi tambaya, a'a ya fadi yana mai girgiza kanshi, haya nake daukowa duk yini dari uku nake bashi, Good anty Reemah tace tana gyara zamanta, Hafiz ka saurare ni da kyau kanaji ko, gyada kanshi yayi yace inajinki anty, da farko dai zanso insan sana'ar da kake sha'awar yi, ka ture batun dako, dan banga amfanin sa ba, sunne kai yayi yace walhy anty bani da wani idean sana'a yanzu sai dai in kika bani shawara bazanki dauka ba, ajiyar zuciya tayi tace "to akwai mijin kawata a railway station yana sana'ar fruits, zan mishi magana in hadashi da kai sannan zan baka jarin da zaka tsaya da kafafunka ka rike mahaifanka da yan uwanka, basu da kowa a duniya sai kai Hafiz, hakkinka ne ka kula dasu da ilimin su, nasan kana nema, rashin Jari ne ya taushe ka amma inada yakinin in na baka zaka kula da hakkinsu, Dan Allah Hafiz karka bari suyi kuka da kai ko ba dade ko ba jima na rokeka da Wanda bama gani amma shi yana ganin mu, mikewa daga zaunen da yake yayi ya durkusa yace wallhy zan rike amanar su in ban rike amanarsu ba tawa zan rike, nagode sosai anty Allah ya saka da mafificin alkhairi, Ameen anty Reemah ta fadi ta dauki wayarta ta kira Hajiya Maryam, sun dade suna magana sannan sukayi sallama, tace "gobe in shaa Allah zaka fara Zuwa ka koyi yanda sana'ar take, zan turo maka kudin a account dinka, in baka dashi ka bude dan gara in baka su a hannunka, Allah yasa ka fara a sa'a, Ameen ya Allah nagode kwarai Allah ya kara daukaka, Ameen ameen Hafiz ban kuma ce ka fadawa kowa ba, ka rike shi sirri a tsakanin mu, angama anty babu wanda zaiji in shaa Allah, nan suka dan taba hira har kusan goma yayi mata sallama ya tafi cike da farin ciki.... Duk nuku nukunki sai kinje Nadiya, Baffa mahaifina ne duk abin da yake min badan baya sona bane tunda shi ya kawoni duniya, Nadiya da bata da mafita tace "zanje mamma rigar ce taki shigana, zama ta shige ki ne matso in zage miki zip, matsawa tayi badan ranta yaso ba mamma taja mata rigar ta shige tsaf kamar a jikinta aka dinka, gashi ya shige maza daura dankwali muje, dankwalin ta daura ta yafa gyale duk ranta a jagule, ta tsani wulakancin su Badariyya, tasan Sam haduwarsu ba Mai dadi bace kullum suka hadu sai sun tozarta ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156