Skip to content

Chapter 16

Chapter 16

Zumuncinmu A Yau Book One Complete Hausa Novels 1 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

ya mutu to fa bazai dawo ba, kuma taga yadda akayi wa babanta haka akama mamanta, domin kafin a fitar da gawarshi saida aka kaita kanshi, wani irin kuka ta saki hade dayin wurgi da sweets din da Hafeez ya sai mata bata sha su a makaranta ba, Mamma ki tashi, dan Allah ki tashi, wallahi bazamu sake barinki kiyi kuka ba, ga yaya Hafeez ma zance kar ya sake tafiya ya barmu, dan Allah ki tashi, hannun wacce tayi mata wanka ta kamo tace "dan Allah ki tasheta, kice tayi hakuri karta tafi yanda Baba ya tafi, wallahi muna santa ni da Anty Nadeeyah, kowa baya santa, tasani mu kadai ne muke santa, rungumeta Husnah tayi hawaye na bin idanuwanta, ta dauketa ta fitar da ita a dakin dakyar,, babu wanda bai zubda hawaye a gidan ba.. Bayan an gama shiryata kowa yayi mata addu'ar samun dacewa da rahama.. Baffa na zaune a kofar gida, idon nan nashi kamar gauta, jikinshi babu inda baya rawa, dakyar aka dagashi ya shiga dan yiwa diyarshi addu'a, ki yafe min suwaiba, ki yafe min, ubangiji Allah yayi ma abin da kika bari albarka, na cutar dake matuka, tun kuruciyarki har kawo yau, kuka sosai yakeyi kamar karamin yaro, tabbas mutuwa tayi mishi gaggawa, ina hankalinshi yake lokacin da yake azabtar da marainiyar Allah, babu abin da yasani nata tun tasowarta, bashi da masaniyar damuwarta, duk rashi irin nata bata taba gajiyawa gurin kyautata musu shi da matarshi ba, wani irin kunci yakeji a cikin ranshi da ya tuno bai taba barinta ta samu abinda take so ba, kallon gefenshi yayi ya hango Daddy tsaye shima hawayen ne ke zubar mishi babu kakkautawa, dukkansu biyun abubuwa masu zafi suke tunowa da faruwarsu shekaru da dama da suka shude, share hawaye Daddy yayi ya fita daga dakin zuciyarshi a karye... ************ ****Kalli sararin samaniya ki fada min abun da kika gani, sauke idonta tayi bayan ta kalla, tace "Naga abubuwa da yawa, wasu taurari masu kayatar da duhun daren samaniya, saidai Mamma, ga wani tauraro can, yafi kowanne haske, ga kuma wasu masu haskawa biyu a kewaye dashi, sannan ga wasu can sun disashe su biyu ba'a ko iya hangosu, murmushi Mamma tayi ta dafa Nadeeyah tace "Tauraron da yafi ko wanne haske 'Kece Nadeeyah', sannan biyun dake kewaye dake bani da masaniyarsu, amma tabbas alkhairai ne masu karfi da yalwa a kewaye dake, sannan sai biyun da suka disashe----- sai tayi shuru tana kara kallon sama, tace "bar batun biyun nan Nadeeyah Allah kadai ya barwa kanshi sani, saidai a gefen tauraronki baki hangen wani wanda yake turo kai karfi da yaji yana san doke hasken naki, da sauri Nadeeyah ta kalli sama, a firgice ta maida kanta kasa tace "waiii Mamma wannan hasken mai cutarwa ne, bazan iya jurar kallanshi ba.. Jajircewa zakiyi Nadeeyah, daurewa zakiyi ki fuskance shi domin bashi kadai bane, hango wani yana fasowa a dayan gefen, duk sun kewaye taurarin dake kewaye dake da haskensu, waigawa tayi cike da zumudi da murnar jin maganar mahaifinta, Baba dama baka mutu ba? kaga yadda kayi kyau kuwa, hannuwanta ya kama yace "Tafiya ce ta kamani ta gaggawa, kinga mahaifiyarki bata iya jure zaman, ta biyoni, saidai dawowar mu ba mai yiwuwa bace, domin tafiyar ta din din ce, lokacin da zakiyi wannan tafiyar baiyi ba, yanzu lokaci ne na hakuri da jajircewa, in kina son nasara sai kin jure, in kina san zuciyarki tayi haske sai kinyi hakuri, "Amma fa ba hakurin da zai cutar dake ba, cewar mamma tana murmushi tana shigewa jikin mijinta, akwai hakuri me cutarwa ne Suwaiba, murmushi tayi tace "akwai mana, hakurin da kana ji kana gani a taka ka a wuce, wannan hakurin ka iya fasa zuciya, manzon Allah s.a.w yace "in bazaka iya hakurin abun da akayi maka ba ka rama daidai yadda akayi maka,, "kwarai haka yake, Baba ya fadi sannan ya cigaba cewa "ke din me nasara ce, zaki daukaka fiye da tunanin mai tunani, saidai kinsan dukkan ma'abocin daukaka yana tare da kalubale, amma ki sani kuma kisa a ranki, a ko yaushe Allah swt yana tare dake, karki yada Addu'a domin ita din garkuwa ce ga mu'imini... lokacin tafiyarmu yayi, ki kula da dukkan rayuwarki da ta yar uwarki, sannan kiyi hakuri da dan uwanki, domin shi din mai rauni ne, Nadeeyah tayi saurin cewa "zan biku Mamma, murmushi mai sanyin kyau sukayi mata, suka hade baki cikin murya me kamar amsa kuwwa, sukace "wannan tafiyar ta musamman ce, lokacin yinta a gareki baiyi ba Nadeeyah, Tafiya suka fara yi Nadeeyah na binsu tana kuka tana fadin karku tafi ku barni, tun tana hangensu har haske ya kara kewaye gurin, tsayawa tayi hade da runtse ido tana kiran sunayensu hade da shashshekar kuka... Hannun da taji kan kuncinta mai sanyin kamshi ne ya soma farkar da ita, a hankali ta bude idonta ta saukesu kan Hinad da itama kukan takeyi.. "Sorry Nadeeyah, kiyita karanta innalillahi wa inna ilaihir rajiun, i know it hurts but bamu da yadda zamuyi, addu'a itace tafi dacewa dasu a wannan lokacin, Allahn da ya halicce su ya fimu sansu.. kawar da kai Nadeeyah tayi tana tunano hirarsu ta cikin mafarkinta, "kunyi tafiya mai nisa Mamma, tafiya mai dadi a gareku in shaa Allah, sannan mai radadi a garemu, hawayen idonta bai bar ambaliya ba ta cigaba da maganar zucin da takeyi, yanzu yaya rayuwarmu zata kasance, shikenan bamu da wani sauran gata... "Gatan kowa Allah ne Kanwata, babu wani gata mai daraja, dadi, da dadadawa irin na ubangiji, in Allah ya baiwa bawa gata, to babu wanda ya isa ya tauye ko ya kwace mishi, mika lamarinki gurin ubangiji, kuma kiyi tawakkali kisan shi ne kadai maiyi... saida ya kai aya Nadeeyah ta dago ta kalli gefen da yake, tabbas zancen da takeyi a zuci ne ya fito har ya iske kunnuwanshi, shi din ma tsaye yake idon nan nashi yayi jawur kamar gauta, wani hawayen ya share sannan ya karaso jikin gadon da take, zama yayi gefenta yace "ya jikin naki, runtse ido tayi ta amsa da sauki, Allah ya baki lafiya da hakuri hade da juriya, "Ameen yaya Musaddiq, Hinad fadi tana share mata sauran hawayen dake gefen kunnenta.. Ina Zainab take yaya Musaddiq? Kafin Musaddiq yayi magana sukaji an murda kofar, Hafeezu ne ya fara shigowa sai su Anty Reemah, Hilal ne karshen shigowa shi da zainab, hannunta rike da ledojin kayan kwalama, fuskar nan tata tayi jawur, tana ganin Nadeeyah ta saki ledar ta karasa ta fada jikinta tana kuka, mikewa Nadeeyah tayi a hankali sannan ta janye daga kusa da musaddiq, ta dago kan zainab tace "menene, me aka miki? Anti Nadeeyah mamma ma ta mutu, ta tafi gurin baba, sun dauketa sun fita da ita, shikenan bazamu sake ganinta ba, dariya Nadeeyah tayi tace "inji wa yace miki, mamma bata mutu ba, kinsan tace miki zata je Agadaz rannan ko? Eh zainab tace tana me kallon Nadeeyah, to can ta tafi, kina gani sun shiryata ta hau jirgi tana jin dadinta ke kuma kina nan kina kuka, oya share hawayenki ki ji abin da mamma tace in fada miki dazu kafin ta tafi, da sauri ta share hawayenta

Table of Contents

Chapters

156 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156