Skip to content

Chapter 90

Chapter 90

Zumuncinmu A Yau Book One Complete Hausa Novels 1 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

kar in yanke, "in ka yanke zaka hakura ai ta fadi itama tana dariyar, "har so kikeyi in yanke ko? "Kai ka fada nidai bance ba! "Kin ce mana, ya fadi a shagwabe kamar karamin yaro, dariya tayi hade da tattara dankalin ta juya mishi baya ta cigaba da aikinta, "An fada miki sakona?? Wani irin faduwar Gaba taji da ya jefo mata tambayar, bata samu bakin amsashi ba ta cigaba da aikinta hannunta na rawa, Gabanta ya dawo yasa hannu ya dago fuskarta, da sauri ta runtse idonta tace "wani sako? In abinci ne kasan yanzu zan gama, "uhm ga acici ko? To wannan sakon yafi cikina muhimmaci, Hilal bai fada miki komai ba? Ya karashe tambayar cike da kasalar da soyayyarta ta sakar mishi, turo baki tayi hade da ture hannunshi tace "ni bai fada min komai ba, hannu yasa a aljihu ya dauko waya ya fara latsata, da sauri ta daura hannunta kan wayar tace "Dan Allah yaya Musaddiq ka bar wannan maganar, yin soyayya ni da kai ba abu bane mai yiwuwa, "dalili?? Ya tambaya fuskarshi ta nuna alamun damuwa, rasa abun ce mishi tayi kawai tace "saboda inada wanda nake so, zoben dake makale a hannunta ta nuna mishi tace wannan zoben alkawari ne, kuma kasan babu kyau karya alkawari, Hannunta ya rike a hankali yana shafa zoben zuciyarshi kamar zata soye saboda azabar radadin da take yi, iya karfinshi yasa ya fincike zoben a hannunta, tana kallonshi ya sa hakori ya karyashi yayi wurgi dashi ta window, kallonta yayi da wani irin yanayin da bata taba gani a tare dashi ba yace "koma waye saidai yayi hakuri dan ba samunki zaiyi ba, ke tawa ce ni kadai, kin gane ko? Kasa tayi da kanta hawaye ya fara zubo mata tace "kayi hakuri, ina sonshi sos---- *Nadeeeyah....* ya fadi da karfi rai a bace kamar namijin gaske, sautin kukanta da yaji ne ya sa jikinshi mutuwa, hannu na rawa ya dago fuskarta ya fara share mata hawayen, "kiyi hakuri ki daina kuka, bazan iya jin bakinki ya furta san wani bayan ni ba, bazan jure ba, rage murya yayi yace "dan Allah ki soni ni kadai, kamar dada ingizo kukanta yayi saboda bata son ya matsa su shiga cikin matsala tare, ganin yayi mata tsawo sosai ya sanyashi rage tsawonshi daidai fuskarta, "Nadeeyah---- "dan Allah kayi hakuri ta katseshi cikin kuka, "wai dame zan hakura ne? ya za'ayi in hakura da abun da nake so, kin san bazai yiwuwu ba, ya karashe yana daura hannunshi a saman idonta, "ki daina min kuka, bana so, in ba so kikeyi inyi ba nima, kiyi hakuri kinji? ki manta dashi ga dan uwanki, kinsan nafi sonki, kuma kema kina sona, zaki fi kula dani, abinci na, komai na, "Ni bana sanka ta fadi tana goge fuska da hannunta, saboda shaukin so dake dibarshi baisan sanda ya hada jikinshi da nata ba ya kankameta hade cewa "zaki soni sosai, Fiye ma da kanki Ma... Fiye da komai a duniya... lumshe idanuwanshi yayi ya cigaba da fadin *I love yhu Nadeeyah, more than life it self......* Innalillahi wa inna ilaihir rajiun..... maimata Kalmar Mummy tayi sau uku tana tafa hannun cike da mamaki da takaici....... Mrs Tijjani Shattimah...... [05/04 10:42 PM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 5⃣4⃣ By *Aysha Ya'u kurah* Na shiga uku ni Zainab! yau me zan gani a cikin gidana, Da sauri Musaddiq ya mike har takalminshi daya na fita a kafarshi yace "me kika gani Mummy? "Ubanka na gani ta fadi a harzuke, abin da kukeyi kenan Musaddiq? yau ni na shiga uku na lalace, Oooh wato shiyasa kullum kike hanyar dakinshi da nufin tashinshi a bacci, ashe zuwa kikeyi ki koya mishi yadda mace da namiji suke jiyewa kansu dadi, yanzu Nadeeyah har kinyi girman da zaki koyawa namiji yadda zai dinga yi miki kiji dadi, *DANKARI!* lallai wannan abun babba ne, "Wai Mummy me ya faru ne? babu abin da mukayi fa, kawai ina taya---- zan ci maka mutunci in ka sake yi min magana, wallahi kana cewa takk zan kwada maka mari, sakarai wanda bai san inda yake mishi ciwo ba, maza ka biyoni.... kallon Nadeeyah dake tsaye tana share hawaye tayi tace "To munafuka maza ki wuce daki ki jirayi hukuncin da zan miki, yar iska mara mutunci, Rai a bace Musaddiq yace "ki daina zaginta Mummy, me tayi miki da zafi har haka kike kiranta da munanan kalamai, haba.... "Bance karka sake samin baki ba, zo ka fita ka wuce sama gani nan zuwa, Saida ya bari Nadeeyah ta fita sannan shima ya fita ya haye sama yana kunkuni dan shi samm baiga abin da sukayi ba..... "Ashe yarannan Iskancinsu sukeyi, wallahi da wani ne yazo ya bani labarin cewa yaga Musaddiq da mace a yadda na gansu wallahi bazan yarda ba, dan rashin kunya a cikin gida, ita kuma dan ta gama zama yar iska harda kankame wuyanshi.... *Zainab....* Daddy ya daka mata tsawa da karfi dan yaga tana neman wuce gona da iri, shuru tayi tana hucin bacin ran kalaman da ta jiyo danta da ta gama shirin kece raini dashi yana fadawa Nadeeyah, Nadeeyar Adamu mai gadi! da sauri ta runtse idonta dan wallahi tuno abun ma mugun taba zuciyarta yakeyi, kallon Musaddiq Daddy yayi fuska babu alamun wasa yace "ka fada min gaskiya, menene tsakaninka da Nadeeyah? Nasan ko kai zaka iya rungumar mace Nadeeyah bazata taba kusantar namiji ba saboda i have full faith in Suwaiba's upbringing, Shin me mahaifiyarka ta gani wanda ya sanyata yin wannan tunanin, kamar jira yakeyi mahaifinshi ya kai aya yace "Daddy dan Allah ka aura min Nadeeyah, wallahi ina santa sosai, "Bakin cikin kiran Sunan Suwaiba da Daddy yayi da kuma na kalaman Musaddiq su suka hadu suka dugunzuma zuciyar Mummy ta sakar mishi wata irin kazamtaciyar ashariya, kallo daya Daddy yayi mata tayi saurin dauke kai idanuwanta sunyi jaa saboda bacin rai, Maida hankalinshi gurin danshi yayi Zuciyarshi fess saboda dama abin da yake ma danshi addu'a kenan, "ka nemi soyayyarta? Daddy ya tambayeshi cikin sakin fuska, "Eh Daddy, ita ma tana sona, "Karya kakeyi wallahi, inaji tana cewa bata sanka, Yadda Mummy tayi maganar ya sanya Daddy dauke kai dan dariya ta kusa kufce mishi, jiya bata barshi ya runtsa ba saboda labarin Faida yar gidan *Hon Danjuma Diriss*, ta matukar cin burin bikin, shi kuwa a gurinshi sam bayasan danshi yayi auren *MATAUL HAYAT*, irin su Nadeeya ya dade yana fata, sai gashi Allah ya kawo mishi cikin sauki, waya ya daga ya kira number Husnah yace suzo tare da Nadeeyah, Mummy najin haka ta dauko wayarta ta tura text din gargadi zuwa ga Nadeeyah, A lokacin da ta tura text din a lokacin Nadeeyah da Husnah sun kusa taka step din karshe..... Cikin hikima Daddy yayi musu Nasiha ya nuna musu muhimmancin aure at early age, sannan ya kalli Nadeeyah yace "Nadeeyah kina da wanda kike so? Aure zan muku ke da Husnah... A kunyace taja hijab dinta ta kasa hada ido dashi, ya za'ayi ta iya furta bata san danshi na cikinshi, Daddy, Hilal, Anty Reemah, Musaddiq, Anty Raly, uwa uba Husnah da bata banbanta kanta da ita, duk a cikin zuriar

Table of Contents

Chapters

156 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156