Skip to content

Chapter 83

Chapter 83

Zumuncinmu A Yau Book One Complete Hausa Novels 1 1,197 words 0 views Progress saved
Download Book

kewaye da ita, a gigice ta ciro kurciyar da duk wata sai ta bata ruwa ta mayar ta rufe, tun da ta kwanta ciwo kusan watanni takwas bata kara bi takanta ba domin itama ba lafiyar gareta ba, girgiza kurciyar tayi tana kuka tana fadin *YARIMA ADAMU* wayyo Allah Kunzo a kurarren lokaci, nasan duk inda Yareema yake a yanzu to kasa ta rufe idonshi, wannan kurciyar rayuwar Yareema ce, Allah na tuba, wayyo ni Allah, haka ta dinga fadi hankali tashe, Da karfi ta saki mutum mutumin hanunta ya tarwatse a tsakar gidan, nan tabi kowane kai ta cire dabaibaiyin da aka mishi, runtse ido Sarki Tidjani yayi saboda juyawa da yaji kanshi nayi, dakyar Shareefah ta tallabe shi ya zauna a kasa ba tare da duban dattin gurin ba, itama hakan ce ta kasance da ita, saidai ita ta kasa fahimtar komai, sabanin Sarki Tidjani da komai ya shiga yawo a kanshi, yadda abubuwa suka faru ya dinga tunowa kamar yanzu ake yinsu, kusa dasu Hajja taje dan itama wani karfi taji a jikinta, burinta ta sanar dasu komai da suka sani da wanda basu da masaniya... "Nasan yanzu wasu abubuwan sun fara dawowa a kanku da kuma daukacin mutanen da suka san Yareema a Agadez, to saidai abin da baku sani ba shine dalilin da yasa ya kaurace muku ya tafi can wani guri inda babu wanda zai ganshi bare har yasa shi waiwayen gida, "Adamu Yallo... sarki ya dinga maimaitawa a bakinshi, fuskarshi yake kallo kamar yanzu suka rabu cikin lambun *Shehrah Agadez*, ina dan uwanshi ya tafi har tsawon wannan lokacin, yana kallon fitarshi daga lambun lokacin bakinshi yayi mishi nauyi ya kasa kiranshi bare har ya tambayeshi inda zashi, sai yau yaji tunanin ya dawo sabo dal game dashi, Da sauri ya maida idonshi kan Hajja yace "ina Adamu? Me ya sami Adamu? Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, me ya shiga kaina har na manta da dan uwa kuma aminina, Ya salam ya fadi hade da dafe kai.. "Ba laifinka bane Yallabai, Laifin namu ne, bakai ba ma kowa a garin Agadez a yau sai ya tambayin dalilin da yasa ya manta da Yareeman da suke matukar so fiye da sarkin Kanshi... har ke ma Shareefah, a karancin shekarunki zaki iya tunawa da *Yeeman ki* , *Yeeman Pappalinto* nan take mafarkinta ya dawo mata sabo, sunan Yeema take yawan fadi cikin mafarkinta, wani irin kuka ne ya kufce ma Shareefah ta dinga nanata sunan a ranta, tabbas ta tuno kuruciyarsu saboda mafarkinta bai rage mata komai ba, cikin kuka tace "Bani labarin Yeema nah! Bani labarin dalilin da yasa yayi nesa dani..... *TUNA BAYA.......* ********** Ranki ya dade kici abinci dan Allah, rashin cin abinci zai iya zame miki illa, kuma kin sani sarki bazai fasa abun da yayi niyya ba, cikin Kuka Fulani Ayyu tace "Hajjara yanzu anyi min adalci, ace sarki ya rasa da wacce zai hadani sai da *Kuyanga Rosalin* , kuyangar da na bawa yarda tasan sirrina fiye da kowa, tayaya zan iya kallon mutanen gari, wannan ai cin mutunci ne a gareni da masarauta baki daya, Gabanta Jakadiyya Hajjara ta dawo tace "ki kwantar da hankalinki, ki barshi yayi auren, zamu san yadda zamuyi da ita, da kalamai masu dadi Hajjara ta kwantar mata hankali har taci abinci.... Wata hudu bayan auren *sarki Abdallah Yallo* da Kuyangarshi mai kula da komai na alamuranshi *Rosalin Mujdaha* mahaifinta shine mai bawa sarki kariya, bayan rasuwar mahaifiyarta mahaifinta ya bawa sarki ita domin ta zama mai aikinsu ta jikinsu wacce zata kula dasu, garin binciken shi na rashin haihuwa Rosalin ta fado ciki har malaminshi ya fada mishi alherin da ke tattare da aurenta, bai damu da kalubalen da ya fuskanta daga yan uwa da matarshi ba aka sanya rana, har Allah yasa ta zamo matarshi, kyakykyawar gaske ce doguwa sambal, ga biyayya da hakuri, hakan yasa yake matukar kaunarta, babu irin asirin da Fulani Ayyu batayi ba dan taga bayanta amma Allah cikin ikonsa duk ta tsallake, saboda tsoron Fulani da Rosalin keyi hakan yasa bata fita ko nan da can, duk abin da zai hadasu tana neman hanyar kaucewa saboda bata san tashin hankali, mugun hakuri gareta ga kawaici da sanin ya kamata, Babu wanda keda masaniyar tana dauke da ciki domin tsakaninta da bayinta yar kallon fuska ce, ko mikewa a gabansu batayi, A ranar da cikinta ya cika wata tara ranar akayi haihuwa a gidan, wazirin sarki wanda ya zamo kani ga sarki, a gurin barka ne kowa ya fahimci ciki gareta, ranar Fulani mutuwa ne kadai batayi ba, gaba daya kansu ya kulle ita da Hajjara suka rasa ta inda zata bullowa al'amarin.. Ranar suna Yaro yaci sunan *TIDJANI*, A daren ranar sunan Rosalin ta tashi da nakuda, sarki da kanshi ya sa aka kira unguwar zoman gidan ta karbi haihuwar, yana daga bakin kofa yaji kukan jinjiri, wani irin kuka ya fashe dashi na murna wanda yaki dauke mishi har saida yaji dumin danshi a jikinshi, nan gaba daya gari ya dauka Sarki Abdallah Yallo ya samu magaji....., kwana goma akayi ana buduri a garin, gidan kuwa zama yayi kamar gidan gala, domin cike yake tun safe har washe gari, babu abin da akeyi sai ciye ciye da raye raye, ko ina ka zaga cikin garin farin ciki ke dauke a fuskar kowa saboda sarki ya zamo mai kyautatawa a garesu.... Shekarar Yareemah Adamu bakwai rikonshi ya koma gurin Fulani Ayyu da tayi sanadiyyar mutuwar Rosalin da karamin ciki bayan barin da ta dinga yi, sarki yayi kuka yayi bakin cikin mutuwar Rosalin mace mai matukar nuna kula a gareshi.... Duk yadda Ayyu takai ga son kuntatawa Yareemah Adamu hakan yaki yiwuwa saboda sarki yana sanya ido sosai akanshi, sai kuma matar waziri mahaifiyar Tidjani wacce yake yini a gurinta bacci kadai ke maidashi gida gurin mahaifinshi, Albarkacin Adamu Allah ya azurta Fulani da samun ciki a lokacin da ta fidda rai, saidai kashh tayi matukar bakin cikin ganin ya mace ta haifa, haka nan tayi ta dakon kiyayyar Adamu a ranta, shi kuma Allah ya daura mishi kaunar yarta Shareefah haka itama Shareefan, ko ina zasu tare suke zuwa... Yana shekara goma sha shida sarki ya fara barin mishi kujera yana ganin yadda yake gudanar da al'amuran sarauta, Adalin sarki Abdallah, ashe a lokacinshi bai kwatanta adalci kamar yadda Adamu ke kwatantawa yanzu ba, Izza ta mulki da kasaita gaba daya sun tabbata a jikin Adamu, wani irin farin jini Allah yayi mishi wanda ya sanya ko ina a garin ake maganarshi da yabonshi, A rana in baiyi abun alkhairi sau goma ba to zaiyi fin goman, gaba daya kowa a garin ya tabbata cikin walwala saboda zuwan Yareemah Adamu.... *Mummunan Kaddara* Ranar da ya cika shekara Ashirin ciff, ranar kaddara mummuna ta afka mishi, a ranar al'amura marasa dadi suka faru a cikin garin agadez.... *Yadda Abun ya faru* Cikin farin ciki Sarki ke sanarwa da fulani Ayyu ya game shirin komai na hutawa ya barwa Yareemah kujerarshi, sannan ya fada mata an kawo mishi yaran sarakunan da zai aura mishi saboda cikar kamalar sarki, nan ta nuna mishi farin cikinta sosai harda cewa zata tayashi zabe a cikin matan.. Tana barin gurinshi zuciyarta

Table of Contents

Chapters

156 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156