Skip to content

Chapter 153

Chapter 153

Zumuncinmu A Yau Book One Complete Hausa Novels 1 1,198 words 0 views Progress saved
Download Book

tsuguna can nesa dashi tace "Ina kwana Daddy, " Lafiya kalau Nadeeyah, ke kuma haka akeyi, kullum ina son muyi magana sai kiyi bacci baki jirana in dawo, baki kyauta min ba, gashi yau saura kwana huďu kadai ki tafi, yanzu dai kije ki shirya kizo muje ki zabi abinda kike so.. Hawayen dake kwance cikin fararen idonta ne suka sauko kan kumatunta, "Daddy bana bukatar komai ta faďi cikin rawar murya.. Cike da zolaya yace "Nasani Nadeeyah, amma ai a matsayina na uba duk da ban kai matsayin kuďin su Taheer ba ai bana kai ki haka ba, sai a goranta mana, tashi maza ki shirya.. "Sautin kukanta ne ya fara karaďe cikin falon wanda ya dauki hankalin Hilal dake saukowa kasa.. "A'a Kuka kuma Nadeeyah, ki daina kuka dan Allah kar ki karya min zuciya, wasa nake miki, tashi kije ciki zamuje da Reemah.. "Dan Allah Daddy kuyi hakuri, wallahi na rasa yadda zanyi, ina cikin tsaka mai wuya..... ta karashe cikin tsananin kuka.. Tasowa Daddy yayi ya isa gareta, a hankali ya dagota ya shiga share mata hawaye, "Allah shi zai fidda ki, nasani baki da laifi dan baki isa ki ketare kaddararki ba, duk abinda Allah ya rubuta akanki babu wanda ya isa ya gogeshi, Musaddiq ko baki aureshi ba yana nan dai a matsayin jininki babu wanda ya isa ya raba, rabuwa da Taheer kuma samm babu adalci domin bazan fifita son ďana akan na wani ba, shima ďa ne, kuma yana da zuciya a kirjinshi, ki kwantar da hankalinki ki barwa Allah lamuranki shi ne mai saukakawa... Ajiyar zuciya tayi mai karfi zatayi magana muryar Junior ya katseta.. A tare suka waigo suka kalleshi Daddy ya saki murmushi haďe da cewa "Aboki, kaine a gidan da safe? Ina Daddynka? Jin ya ambaci sunan Daddy yasa shi waigawa dan tare suka tako har kofar parlon, "Daddy, Daddy.. ya fara kwala kiran sunan Taheer wanda ya riga yayi nisa, "Dama kawoshi yayi ya zauna a gidan dan ya saba dasu, sai kuma abinda kunnuwanshi suka jiye mishi abin da ya sanyashi cikin tsananin tausayi da kuma sake ganin girma da kimar Daddy.. Kuka sosai Junior ya farayi dan ya fito baiga motar Taheer ba, Hilal da ya gama sauraron su Daddy shi ya fito wajen yana lallabashi haďe da yi mishi alkawarin maidashi in yayi wanka, da kyar ya yarda amma har lokacin bai bar kuka ba... Cike da kuluwa Nadeeyah ta kama hannunshi ta nufi ďaki dashi tayi mishi tsawar da ya sake sanyashi cikin wani gigitaccen kuka, "Tsanar da kikayi wa ubanshi ce ke neman shafarshi, Husna ta faďi tana janyoshi jikinta, ga mamakinta sai ya turata baya ya koma jikin Nadeeyah ya kankameta yana cigaba da kukan, Kukanshi da kalaman Husnah su suka sake dugunzuma zuciyarta, nan take ta turashi gefe ta faďa bayi tana kuka mai sosa zuciya, tana jiyo ihun kukanshi yana faďin "bazai sake yin kuka ba Dan Allah ta buďe mishi kofa, duk yadda Husna taso kamashi kasawa tayi haka Anty Reemah da Maleekah, duk wanda ya tabashi sai ya turasu ya cigaba da ihun sunanta, Hilal ne kaďai ya iya calming dinshi ya daukeshi suka fita daga dakin, Sama suka nufa yana rarrashinshi haďe da yi mishi alkawura kala kala... Gaban mudubin da babu glass suka samu Musaddiq zaune da towel a jikinshi alamun yanzu ya fito wanka.. a kunne Hilal ya raďawa Junior cewa "Go nd say sorry to ur Twinny, kasan bashi da lafiya, he will feel better in dai yaji sorry daga bakinka.. Da sauri ya sauka ya isa kusa dashi yace "Sorry Twinny, hw is body? Hope u are feeln better? A hankali ya maida dubanshi gareshi ya tallabo fuskarshi yace "Yes twinny, hw are u? "Nt fine, Mamma shoutd at me nd she is crying.. ya faďi kamar zai sake yin wani kukan,, Raunanniyar zuciyarshi wacce ake lallabawa ta fara mishi zugi, nan take idanuwanshi saka kawo ruwa, burinshi bai wuce ace in ya rufe idonshi ya farka ya ganshi a kabari ba, ya tsani rayuwar gaba ďayanta, Tunda ya taso a duniyar nan baisan mecece rayuwar duniya ba, shiyasa ya ke kiran Nadeeyah da rayuwarshi baki ďaya, itace duniyarshi, Daddy ya kasa fahimtarshi, kowa ya zuba ido yana ganin za'a rabashi da rayuwarshi.. hannun Hilal yaji a kafadarshi wanda ya sanya hawayen karasa saukowa kamar an ingizo su, "Hilal babu wanda zai iya taimaka min a cikinku, haka zaku zuba ido--- toshe mishi baki Hilal yayi yace "Bamu isa mu shiga hurumin ubangiji ba Kyari, ka fahimci hakan, dan Allah kayi tawakkali, kaddara babu yadda bata zuwarma bawa, Rungume junior yayi saboda jin hannunshi yana share mishi hawaye, "Please Hilal take care of my son bayan raina, wallahi bazan rayu ba, Dogon tsaki Hilal yaja haďe da raba junior da jikinshi yace "Sai ka kashe kanka tunda rayuwarka a hannunka take.. Muje kasa kaji takwara, ur twinny is crazy ya karashe haďe da jan hannun junior sukayi waje... Maida kai Musaddiq yayi ya kwanta yana rusa kukan da tunda aka haifeshi bai tunanin ya taba yinshi, duk yadda yaso yin karfi da zuciyarshi kamar yadda Daddy ya bukata ya kasa saboda zuciyar ta raunana matuka da kaunar Nadeeyah, Ya Allah Ka sàssauta min, haka ya dinga faďi yana juyi akan gadonshi.... ******* Alkawari dai Kyari, gashi har karfe biyar baka ba labarinka, Yadda take maganar ya sanya Shareefah kureta da ido domin ta dade bata ga yar uwarta cikin wannan yanayin ba, "Kiyi hakuri Saudatu, in shaa Allahu zanzo zuwa anjima, ina nan sane ban manta ba, Daddy ya bata amsa yana mai duban agogon hannunshi domin ganin lokaci... "To ina nan dai ina zuba ido, nasan dai baka saba alkawari bansani ba ko ka koya kasan shekarun da yawa, Dariya suka saki a tare saboda yasan tabbas tsokanarshi takeyi, "In ma na koya bazan so in gwada miki shi ba, domin an daďe ba'a hadu ba, ya kamata a barwa juna memories masu daďi bayan rabuwa, ina nan zuwa, just a second plss inada baki zan kiraki, bai jira jin amsarta ba ya kashe wayar ya cigaba da duba abubuwan da aka kawo mishi... *BAYAN RABUWA* Shi ta dinga maimaitawa a cikin ranta, yana tunanin rabuwa da ita kenan bayan shekarun da suka dauka basuga juna ba, har yanzu Mukhtar baya tunaninta kamar yadda tayi a baya da kuma yanzu da ganinshi ya tado mata matacciyar soyayyarshi.... *Flash back a gurguje* _Shekaru da dama da suka wuce Allah ya jarabci Anty Saude da Soyayyar abokin makocinsu kuma malaminta wanda yake mata lesson Uncle Abubakar, a duk lokacin da uncle Abu yazo yi mata lesson Kyari kan je gidansu yayi ta tsokanarta musamman in akazo kan mathematics, tun abun na bata haushi har ya rikiďe ya koma birgeta, in yana tsokanarta sai ta biye mishi suyi tayi har lokacin tashi lesson yayi ba'a tabuka mata wani abun arziki ba, in Kyari yayi tafiya babu zancen karatu ta dinga damun uncle Abu kenan tana tambayarshi ranar da zai dawo, kasancewarsu dukkansu 'yayan masu kudin lokacin sai ya zamana tasu tazo daya musamman ta bangaren Anty Saude, ita duk a tunaninta soyayya ce ke kawo Kyari (kamar yadda taji uncle Abu na cewa) gurinta,

Table of Contents

Chapters

156 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156