Skip to content

Chapter 68

Chapter 68

Zumuncinmu A Yau Book One Complete Hausa Novels 1 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

kallo sosai, saida tayi mishi guga na musamman sannan ta ajiye, tana gama gyaran office din ta sake daukar hoton tana kallo, Hakanan taji mutumin cikin hoton ya shiga ranta, Sanye yake cikin babbar riga da hula, yayi kyau sosai, Tana kokarin ajiye hoton taji yace "my late Father " *Alhaji Haroun Yallo*, Ajiye hoton tayi da sauri tace sorry Sir, na gama yanzu zan wuce class, Bashi da niyyar matsa mata a makaranta sam, dan a yadda ya tsara a makaranta nuna mata rashin sani zaiyi kururu. amma ya zaiyi, soyayyarta ta hanashi katabus, Takowa yayi ya karaso inda take tsaye ya dauko hoton, "Wannan shine Mahaifina, rayuwar da mukayi dashi ba mai goguwa bace, kullum in ban tunashi a duk numfashin da nakeyi ba to tabbas zan tunashi a duk takun da zanyi a rayuwata, He is my best friend, Mutuwarshi ita ta kashe wasu sassa na farin cikin dake cikin zuciyata, mutuwa ce wacce yayi ta ba zato babu tsammani, Ajiye hoton yayi yace "Mutuwa wata abace wacce zafinta yafi dukkan zafin wutar dake cikin duniyar nan, zafin wuta na warkewa ya barka da tabo, amma mikin rashin makusanci kullum sabo yake zama, Mahaifina ya nuna min kauna har ranar da zaiyi tafiyar din din din, "A ranar da zai mutu ranar na dawo daga Canada, saboda kar ya daga hankalinmu shiyasa ya boye mana ciwonshi, ya dinga biye ma duk wata rigima tawa, Tare muka je aski, cikin rashin sanin yana ciwo nasa akayi mishi askin dukka kanshi dan ya zame min abin tsokana, haka nan badan yana so ba ya yarda akayi mishi, Daga gurin askim muka wuce yawo muna ta zaga gari muna ziyarar gidajen Abokanshi, Masallacin cikin gidan mu nan ne guri na karshe da muka tsaya, A daddafe ya idar da sallar magriba, jin irin numfashin da yake fitarwa ya sani tambayarshi ko baida lafiya ne, dariya ya kakaro hade da naushin cikina kamar yadda muka saba yace "in yana da ni ta ina ciwo zai samu muhalli a jikinshi, Nan take Muryar Taheer ta raunana, hawayen da suka cika idanuwanshi suka dinga tsere a tsakaninsu, ya cigaba da cewa "A sujjar karshe ta sallar isha'i karfin Abbana ya soma karewa, Gaba daya masallacin yayi shuru saboda jam'i da ake bi, numfarfashin Abbana kadai ake ji a ciki da wajen masallacin, gaggauta yin sallama liman yayi, kowa yayi kanshi saboda ganin har lokacin bai dago daga sujudi ba, kuma bai bar fitar da numfarfashi ba, Ko da aka dago shi ya gama fita cikin hayyacinshi, A lokacin wanda ya taba dandanar mutuwa zai fahimci inda Abbana ya dosa, Dagoshi nayi da karfi ina fadin ya tashi muje asibiti, Girgiza kai ya shiga yi yana fadamin "ka barni anan Taheer, ka barni anan, asibiti, ko gida, a yau basu da amfani a gareni, Murmushi yakeyi mai dauke da kuka yana fadin Taheer kayi hakuri, kayi hakuri abokina, na boye maka ciwo na saboda nasan ba na tashi bane, Naso sai ka koma makaranta zanyi tafiyar nan amma inaa lokacina yayi, ban isa kara kwana daya ba koda kuwa ina son kara shi, "Kukan da Taheer yakeyi a lokacin mai sautine dan bai taba fitar da wannan labarin da yayi mishi karan tsaye cikin rayuwarsa ba sai yau da a karo na biyu yake shirin rasa wacce yake tunanin dawowar farin ciki cikin rayuwarshi, Ita din ma Nadeeyah kukan takeyi na tausaya mishi da tausayawa kanta, domin ita ma tayi rashin dukka iyayenta, "Ban taba kawo mishi mutuwa ba saboda ban yarda zai tafi ya barni a wannan lokacin ba, kin saurararshi nayi muka daukeshi dan kaishi asibiti, ina tuno sanda ya shafa fuskata muna gab da fita daga masallacin yace "Taheer kaki yarda ko? Dole ka yard---a d------a wann---- nan ya fara kakari har yafi karfin wadanda suka rikeshi, ka-- kula da--- kanka da-- da-- mahaifiyarka, damke hannuna yayi har lokacin idonshi bai gama rufewa yana tayi min murmushin da ya saba, "A wannan ranar ne na ga abun da ake kira damuwa karara, a wannan bakar ranar naga kaddarar rabuwa da abin da kakeso, a wannan daren mahaifina ya mutu tare da duk wani kuzari nawa.. Tun daga ranar na manta farin ciki da yadda akeyinshi, babu abin da ke burgeni a duniyar nan bare har yasani farin ciki, Rabuwa da Abbana.... ya ilahi!! nan da nan Nadeeyah ta rikice saboda yadda yake kuka kamar ana zare ranshi, kuka sosai yakeyi wanda bai samu damar yinshi ba ranar da ya rasa mahaifinshi, Abubuwan da suka cunkushe mishi ya fitar yau yake kokawa a kansu, shakuwar da yayi da mahaifinshi ta wuce ta ďa da uba, ta zamo shakuwar jini da hanta, a ko da yaushe ya rufe idonshi murmushinshi kadai yake gani, bai taba karo da bacin ranshi ba sai dai farin cikin shi, Gabanshi ta tsuguna itama kukan yaci karfinta tace "Uncle kayi hakuri, sau tari abubuwan da muke so basu cika kasancewa tare damu ba, jarabawar mu kenan, gara kai kana da wacce in ka juya zakaji dadi, ni fa babu uwa babu uba, babu yan uwan uba da zan kirasu nawa saidai na uwa, ka godewa Allah domin not all are fortunate, Duk abinda kaga Allah ya dauke maka to yana da dalilin yin hakan, ta yiwu in ya bar mana su wata rana saboda azabar ciwo mu gwammaci tafiyarsu akan tsayuwarsu cikin ciwon da mu kanmu bamu isa mu magance musu ba, nasan yadda kakeji domin nima ina jinshi ko ma ince fiye da naka, Dan Allah a duk lokacin da ka tunashi ka dinga fadin *innalillahi wa inna ilaihir rajiun* sannan kayi mishi addu'a domin yafi bukatarta a yanzu.... Wata irin nutsuwa ce ta saukar mishi wanda tun kafin rasuwar Abbanshi rabon da ya shiga irin ta, share hawayen idonshi yayi ya dago ya kalleta, Sai a lokacin yake tambayar kanshi dalilin dayasa har ya fada mata damuwar da ya dade yana dakonta, Tabbas zuciyarshi ta gamsu ita ce wacce zai samu nutsuwa da ita, kalamanta sunyi matukar sanyaya mishi zuciya, jin zuciyarshi yake wasai kamar an sauke mishi duk wani nauyin da zuciyarshi ke dauke da shi, Tsugunawa yayi kamar yadda tayi yace "is ok, kukan ya isa haka, ni nasa ki kuka, ni kuma na daina ke kin ki dainawa, sorry kinji, tashi ki zauna... Mikewa tayi tace "zan tafi class ne, kujera ya ja mata yace "kice wa ya saki kuka? Ajiyar zuciya tayi mai karfi sannan ta zauna, Ji yakeyi kamar ya rungumeta ya hanata wannan kukan da yasan irin ciwonshi, "nace ya isa ko nima so kikeyi in cigaba, kinsan in na fara nawa biyu zan hada, da na rashin mahaifi da kuma rashin farin cikin rayuwata, ya karashe fadi a raunane cikin damuwa, Share hawayenta tayi kamar me shagwaba tace "na daina, "Kina sona Umm Nadeeyah? Yadda ya jefo mata tambayar ta sanyata saurin dauke kanta daga kallonshi, "ummm bani amsa plss, nd "who is Musaddiq? Ya karashe yana janyo kujera... "Yaya Musaddiq? Ta fadi tana kallonshi, gyada kai yayi yace "yes waye shi, meye alakarku? "Babu komai, he is my cousin, "nd husband to be, Taheer ya karashe yana kallon cikin idonta, A razane tace "whatt, ba gaskiya bane, kaga

Table of Contents

Chapters

156 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156