Chapter 77
Chapter 77
kyashin kashe mata dukkan dukiyarsu, yar da zata ayi aman kudi daga ko wani bangare, biki ne wanda nake shiryashi tun kafin yau, biki ne na garari....... Mrs Tijjani Shattimah...... [01/04 3:08 PM] fareedah: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 4⃣8⃣ By *Aysha Ya'u kurah* *Kaduna, Niger, Abuja, Nasarawa, direct,* wani dan saurayi ke tsaye jikin zungureriyar mota yana busa taba yana fadin sunan garuruwan da zasu, nan aka fara tururuwar shiga motar kowa na fadin inda zashi, cike da hanzari ta karaso gurin motar tana fadin kaduna, kallon motar saurayin yayi yace "Baba motar ta cika saidai Ko zaki hau baya kan kaya, "karfe nawa wata motar zata zo to, ta fadi cikin gatsali "keeee yane... kike min magana kamar wani danki, in zaki jira motar karfe shida na yamma ki jira in baki iya jira wareee, Cike da mamakin rashin ganin tsufanta tace "kai da uwarka baku da tsofaffi a gidanku ne, yaran yanzu sun fitsare kafarsu, basa ganin girman na gaba dasu, gaskiya anyi asarar haihuwa wallahi, ta karashe tana kokarin jan jakar gana most go dinta, "tare ta yayi da sauri ya busa ma fuskarta hayaki hade da cewa, wallahi bazan duba tsufanki ba zan yaga miki chuna, zigidir zan miki anan gurin kika sake sako sunan gyatuma ta, A fusace tace "nace kaci uwar ubanka, kaji min dan iskan yaro, ni nan da ka ganni bani da mutunci, zan iya yi maka mummuna illa in baka maida hankalinka ba, "ehhhhh yeeeeeeee, ya saki ihu hade da chukumar jakar Goggo yayi wurgi da ita, nan jakar ta yage kayan ciki suka firfito, wata katuwar kwalba wacce take nade a zani ta tarwatse ruwan cikin ya bata sauran kullin dake cikin wasu takardu, ďaga hannu yayi zai kai mata mari drivern motar yayi saurin rikeshi, "kyaleta GARO, barta ta shiga bayan boot din ta zauna, kallon Goggo yayi wacce ta tsurawa kayan da ta kwana tara a hanya tana nemansu, wani irin tukuki taji a zuciyarta tayi kukan kura ta kama wuyan Garo, Dagewa yayi iya karfinshi yayi wurgi da ita gefe hade da zaro zarbebiyar wuka mai kyalli, nan take Goggo ta maida hankalinta ta mike tana kukan wayancewa hade da cewa mutanen dake rike Garo "yanzu dan Allah in ba sauyin zamani ba wannan yaron banyi jika na uku dashi ba, "Na sha tara kikayi dani dan mai cin----- toshe mishi baki drivern yayi yace "yi hakuri Garo, nasan laifinta ne, ka barta ta shiga mota mu tafi, maida wukar yayi yana ta muzurai hade da hararar Goggo, sum sum ta wuce tana kallon jakar da ta sha wahala ta kashe makudan kudi dan samo su, "tuno kashedin da bokan yayi mata na ta kula da kayan domin a shekara sau daya ake samun sa'ar samunsu, wasu zafafan hawaye ta share zuciyarta a dagule ta nufi bayan motar inda kayan mutane suke, "tana zama taji kukan talotalo a cikin wani kwali a bayanta, Tagumi ta zuba saboda shiga wani yanayi da tayi, yanzu ya zatayi ta sake samun wannan sa'ar, bazata ta taba bari tayi wata daya da Anni da papy ba tare da ta illata su ba, so takeyi taga bayansu dukkansu, so takeyi ta mallaki zuciyar Baffa da gidanshi baki daya ita kadai kamar yadda tayi a baya, daga ita sai yarta da jikokinta, Tana cikin wannan tunanin mai cike da takaici drivern yace ta bashi kudi, "nawa ne? , jaka goma sha biyu, "jaka har goma sha biyu, abin na sat----- ganin Garo a bayanshi yasata saurin sauya maganar zuwa "abin har yayi sauki haka, fito da lalitarta tayi ta bashi kudin ciff, irin kallon da Garo ke mata yasata saurin sunkuyar da kanta, shaff ta manta da yar posan kudinta a gefe, tana jin motar ta fara tafiya, ta dago kanta, tunane tunane ta shiga yi marasa dadi har bacci yayi gaba da da ita.... Mikakkiyar tafiya sukayi ta tsawon awa 8 saboda ana yi ana tsayawa Sallah da cin abinci, Suna daidai *kawo* suka fara shelar kowa ya hada kan kayanshi domin yanzu yan kaduna zasu sauka, Goggo da bacci yayi gaba da ita sam bata san sunayi ba, haka drivern baisan kaduna tace ba, da yake yan kadunan basu da yawa ko minti biyar basuyi ba suka daga zuwa garin gaba da zasu, saboda tsabar baccin gajiya ko kuma ince hakki, saida suka kai bus stop din tafiyarsu da Goggo, Nan drivern ya tasheta a gajiye dan bacci yakeji matuka, a firgice ta tashi tana laluben poss dinta tana fadin har munzo Kawo? Wani kawon? drivern ya tambayeta cike da kosawa, "Kawo ta kaduna ďan nan, tsaki yaja yace "dan Allah Baba fito kar in miki rashin kunya, fitowa tayi cikin rashin fahimta tace "ban gane ba, ina ne nan, rufe boot din yayi yace "je ki tambayi wadancan, ya nuna wasu gungun mashaya a gurin ya wuce yana mika hade da wakar dan kwairo ta "mai dakin gabas, Zaman dirshan Goggo tayi a garin da bata san ko ina ne ba, saboda baccin da ta tika idonta ya soye sam bata jin shi, ga muguwar yunwa tana ji, ga bakin cikin satan da akayi mata, Tashar cike take da mashayan da basu da aiki sai na shaye shaye duk minti, mayafinta ta cire tayi matashi dashi, ta rasa yadda zata fassara irin hau din da hauta a wannan rana, saboda tsabar takaici har sambatun bacin rai takeyi, ga tsabar ciwon kai da ya sata a gaba, Wani mai butar shayi ne ya gifta tayi saurin kwala mishi kira, dawowa yayi da sauri dan a tunaninshi siya zatayi, "sannu ďan albarka, nan wani gari ne dan Allah? "Tashar Akwanga! bakisan a Nasarawa kike ba, wani kululu Goggo taji ya taso mata, nan take hawaye ya wanke fuskarta, da yaron yaga ba siya zatayi ba yayi saurin mikewa ya nufi gurin wadanda suka kirashi, kuka mai hade da majina Goggo tayi shi a daren ranar, maimakon ta saduda tasan hakki ne ya fara dawainiya da ita sai ta kara kullatar bayin Allahn da zata sake ninka zunubbansu akanta.... Motar dake tashi da asuba zuwa kaduna tabi tanata roko su sata ko a sama ne, tana cikin wannan magiyar taji muryar da ko a mafarki taji ta zata ganeta, "Rilwanu ta fadi bakinta kamar gonar auduga, daga ina kake? Nuna mahaifinshi yayi yace daga Benue muke zamu wuce kaduna, wannan Mahaifina ne, kamar yadda na fada miki zan dawo dashi kaduna in nema mishi magani, da yake a cikin duhun subahi ne sai basu samu damar ganin fuskar juna ba, nan dai Goggo ta shiga aljihun kaskastaccen bawan gidanta Rilwanu...... Firgai firgai ta shigo gidan yunwa kamar zata kasheta, a lokacin har masu ginin sunzo, da masu gyara mata daki da masu karasa ginin da ake buga kwano, goge idanuwanta tayi dakyau ta fara dubawa ko ba gidanta ta shigo ba, dakin waje shi ya tabbatar mata da gidan ta shigo, zagaye dakunan tayi hade da fadawa dakinta, wani irin ja baya tayi cikin firgicin rashin ganin ko tsinke a dakinta sai ma hake haken kasa da akeyi ana sa tiles masu kyalli, nan take yunwar da takeji tayi murabus a cikinta ta fara fadin, "uban waya saku fasa min daki, ina
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156