Chapter 99
Chapter 99
d'in da zai hana keken weelchair gangarawa da wucewa a sauk'ak'e. Sosai aka gyara side d'in. A washe garin ranar Ahmad yasa aka kawo mishi gadon samfarin royal bed kana da kujeru suma royal d'in. Aka canza mishi AC bedroom aka dawo dashi parlour kana aka sa sabon AC a bedroom d'in. Hatta labulaye da carpet da blanket da beshid sabbin Ahmad yasa aka saka komai na d'akin lemon green and white ne sosai kalan ya haska d'akin, Kayayyaki sabbi dal-dal Ahmad ya sayo yazo ya jera mishi kananu na d'inkawa kuma shida kanshi ya fito da kekken d'inkin Hayatuddeen ya fara yayyarɗa mishi ɗinkunan zamani d'inka mishi. Sosai Ummi take cikin farin ciki. Adda Rahma kuwa a kwanakin kullum sai tazo. Yau kwana biyar kenan da fara tashin Saifuddeen, suna zaune shida Hayatuddeen wanda ya kira Ummi video call sai hira da dariya suke, nan Raliya ta amshi wayar ta nuna mishi yadda aka gyara mishi side d'in da zai zauna. Murmushi yayi cikin jin dad'i da begen komawa gidan Cikin ahlinsa. Shiko Hayatuddeen kai ya jinjina kana yace. "Oho wato abinma son kaine, da yake Hamma ne zai zauna a nan kalli yadda kuka wani gyara d'akin tamkar makwancin shugaban k'asa. Wato nine jaki in na ga dama in kwan a k'asa ko?." Cikin kewar sangartarsa tace. "Ohoho my autanmu kaima ai yanzu side naka tas yake in kana soma sama zaka koma, inda Hamma Saifuddeen yake da." Cikin jin dadi yace. "Wayyo Allah kice na zama alhajin sama." Dariya sukayi baki d'aya kana suka d'anci gaba da hira daga bisani suka salami juna. Yau mako biyu kenan cib da fara tashin Saifuddeen zaune, Kuma Alhamdulillahi tuni an gama mishi duk wani abinda ya dace na sallamarsa da shared'in duk bayan wata shida zaizo a duba jikinshi. Tuni Hayatuddeen ya gama musu dukkan shirin komawarsu da taimakon Dr Malik Khan. Nanda kwana biyu jirginsu zai d'aga zuwa Nigeria. A cikin asibitin. Saifuddeen na konce shi kuwa Hayatuddeen yana harhad'a duk wani abu nasu domin gobe da asuba jirginsu zai tashi. a hankali ya zubawa d'an uwan nashi idanu ganin yadda jikinshi ke rawa kar-kar- kar tamkar mazari idanunshi sunyi jazir, gaba d'aya jijiyoyin kanshi sunyi rud'u-rud'u wani irin zufane ya yanko mishi a take, da sauri ya matso gaban gadon cikin tsananin fargaba da tsoro murya a birkice Hayatuddeen yayi kanshi jiki na rawa. Sai ya kumayi dib ya tsaya wuri d'aya da yake ganin Hamman nashi na jujjuya mishi kai alamun karya matsoshi. Idanu ya zuba mishi cikin kad'uwa sai kuma ya rink'a kame jikinshi ganin Hamman nashi so yake ya durkusa, cikin ikon Allah kuma sai gashi a durkushe bisa tsakiyar gadon. Kusan a tare suke sauk'e numfashi, Dai-dai lokacin kuma Dr Anan da Dr Malik Khan suka shigo. Samunshi a haka yayi matuk'ar sasu farin ciki nan take suka k'ara gwadashi, kana suka dank'a mishi takardar sallama da sharad'in duk bayan watanni shida zaizo. Nan Dr Anan ya kara ink'anta mishi durkuson nasa. Washe gari bayan an idar da sallan Asuba Dr Malik Khan yazo ya d'aukesu, da kanshi ya Kaisu Hilton international Airport Mumbai. Bai bar airport d'inba saida yaga tashin jirginsu. Abuja Amina kuwa yau satinta biyu kenan tana neman Hayatuddeen bata samunshi a waya, gaba d'aya abin ya dameta, gashi yanzuma ta kira layin baya tafiya, kai ta rausayar kana tace. "Allah yasa dai lfy, sai anjima da yamma zan kuma gwadawa." Gombawa d'iban fari. Yau gidan Ummi a cike yake, Raihana mutanen kd ma tun jiya tazo da Affan d'inta. Adda Rahma kuwa itama yau sammako tayi. Hakama goggo Dada da Aunty Mina. Farop da Adam sai tsalle suke yau Uncles nasu zasu dawo. Salisu ma ya kawo Salimanshi. Gida ya kacame da shirye-shiryen tarban Hamma Saifuddeen...! To AL'amarin Zaleeha fa ya girmama, Domin har Ruqquya saida aka mata dan duk an d'auka gamo tayi. Shi kuwa Baba Malam ya sani sarai babu wani gamo, ba iska a jikinta sai dai zallan iskanci inji Kakarsu da fad'i. Maryam Zahira kam su dai a dole Zaliha gamo tayi, Zeyada kuwa da Zakariyya da suke wurin Hajja Inna suma mgnar kakarsu suka bawa amanna Zaliha bata da wani iska sai zallan iskanci. Ya Ahmad d'inta kuwa wanda kwanan suka dawo Nigeria shida matarsa dan watansu bakwai a Istanbul. kasan cewarshi mai nitsuwa da hak'uri da k'aunar kannenshi suna dawowa da kwana d'aya ya taho gombe. Shiyasa yau gaba d'aya Baba Malam ya tarasu, ya jaddada musu cewar Zaleeha fa tanada sauran dama na mako biyu ta fidda miji cikin tarin masoyanta, in kuwa ta sake mako biyun nan ya cika bata tsaida gwaniba to tabbas shi zai mata zabi kuma tayi kuka da kanta. Koda aka tashi taron bayan Ya Ahmad d'in nata tabi suka shiga parlour Mamy gabanshi ta durk'usa cikin zubda k'walla tace. "Ya Ahmad ina sonshi, bayan shi babu wanda nakeso dan Allah ka bawa baba malam hak'uri ya rufa min asiri kada ya rabani dashi." Hannunta ya jawo ya ajiyeta gefenshi cikin nitsuwarsa yace. "Kin san a duniya bamu da kamar Baba Malam ko Zaleeha.?" Kai ta gyada mishi alamar eh, shi kuwa cikin sanyin yanayinshi yaci gaba da cewa. "Kin san wayeshi a wurina nida Maryam da Ziyada da Habu, bama iya jurar ganin b'acin ransa, bama iya lamuntan duk wani abu da zai tab'a mana daraja da mutuncin mahaifinmu, Zaleeha koda nace miki ina tare dake namiki k'arya, zancen gsky bayan Baba malam da Ya Ameenu nake babu yadda za'ayi kiyi ta zaman jiran gaibu, abinda ni ganima nake Al'janine , to tayaya zamu lamunci ki zauna zaman jiranshi. Kawai dolenki dollen dolene ki Zab'i d'aya daga cikin masoyanki. Ko Abdussalam ko Managernku ko Raveel ko kuma wannan abokin nawa Al'amin wanda yayi ta nace miki zuwanki Abuja last year. In kuma kinki tsaida gwani da kanki to wllahi Allah kenan Baba malam zai zaba miki cikin su." kife kanta tayi a kafadarshi tare da sakin nakasasshen kuka tare da cewa. "Na shiga uku ns, wlh ya Ahmad ina sonshi." shigowan Ya Ameenu ne yasa ta mik'e da sauri ta wuce side d'insu kai tsaye bedroom d'in Mama ta wuce bisa gado ta fad'a tana kuka. Cikin takaici Maman ta harareta tare jan dogon tsaki kana tace. "Shirmen banza kawai ni dai ina gaya miki wallahi ko bakya son Abdussalam sai ya aureki yaro d'an manya jikan sarakuna har zakiyi ta wainashi da me kika fishi kyau ko asali ko gata, ni dai ina gargad'inki kada ki bari Malam ya miki zaben tumun dare yadda yayiwa Maryam auren dole to bazan lamunci a miki hakaba, shiyasa gwara ki bar batun wancan aljanin da ya taimakeki ki rik'e Abdussalam yafi miki." wannan shine rana zafi inuwa k'una jin kalaman Mamane yasa ta mike ta koma d'akinta taci ga da koke-kokenta... Tafiya tayi nisa cikin sararin samaniya, kowa na harkan gabanshi, autan Ummu kuwa jinshi yake a takure. Hayatuddeen ne ya d'an juyo ya kalli kekyawar matashiyar dake gefenshi. Wacce duniyar Khanywood keji da ita wacce tauraronta ke harbawa a fagen rawa da wak'a. a hankali yace. "Asma'u Ahmad Matawalle," Sai ya kuma d'an juyawa ya kalleta a hankali yace. "Masha Allah. To Ashema tafi kyau a TV da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148