Chapter 25
Chapter 25
sai taje." kai ta jinjina kana tace. "Shi na fara gayawa kasan ai bazai hanaba yace taje ba matsala." gyara zamanshi yayi ya kalli Rahma data zuba musu ido, sai kuma tayi maza ta rufe ido wai ita bacci takeyi. Jin sautin murmushin sane ya sata tashi zaune kana tace. "Yoh tun d'azu na farka sai naga kamar hirran sirri uwa da d'an lelenta sukeyi shine nayi likimo ai, kai kuma da yake ka shahara da body language ko kallonka akeyi jikinka ke gaya maka kawai sai naga ka zuba min wannan fararen idanun naka." dariya suka d'anyi baki d'aya kana ta zauna sukaci gaba da hira, inda itace ta amshi kud'in ta cusasu a asusun babban goggonin milo. Daga nan sukaci gaba da hirarsu tasu ta rayuwarsu sai shad'aya suka shiga. Shi kam Saifuddeen saida yayi wonka sannan ya yayi al'wala kana yazo ya shafa mai tare da fesa turare wanda wannan al'adar rayuwarsa ce domin Saifuddeen mutunne mai tsananin tsabta sam baya son k'azanta ko kad'a shiyasa yakeda kenkeyani over. Washe gari kamar kullum yayi suka tafi gombe da kafin bakwai na safema sun isa, baccinshi ya d'anyi na awa d'aya da rabi kana daya tashi yayi walahan shi kamar yadda ya saba, sannan ya shiga cikin kasuwa ya fara rarraba ledodinshi ana bashi kud'in na jiya yana bada wani, cikin awa hud'u da kad'an ya gama rabawa ya had'a kud'insu 60k sannan ya ware ribanshi dubu bakwai da d'ari biyu, yaso yayi ragin d'ari bibbiyun saman to kuma sai ya shawarci Jabeer sai yake ce mishi kada ya rage dan kar ya zama yayi azarb'ab'i a kasuwar ledan tunda du du du a wata d'aya ne zaiyi sana'ar kar yayiwa baba Bella shisshigi to da wannan shawarar ya hak'ura. Daga shagonsu Jabeer wucewa yayi yaje ya amso omo aifa nan ya samu sa'an shiga layin masu wonki da guga sukayi ta kwasan sabulun kamaru da omon ranar ribar 2k ya samu a omon ma, da zai koma ya saya musu naman miya da kuma fruits. ******** Rayuwa ta ja yau da gobe asarar mai rai, kwanaki sun tafi tuni azumi ya shigi jikin al'ummar annabi anyi dibi-dibin goma na marmari gashi har an shiga goma na wuya inji hausawa da fad'i. Cikin izinin Allah an gama na wuyan ma yau, gobe dai na d'okin sallah za'a fara. Iyaye da yan uwa da masu wadata dama talaka kowa na hidimar d'inkunan sallah. Saifuddeen ya k'ara sabawa da mutane sosai ko ta ina an sanshi a kasuwar sabida dalilai uku sana'arsa ta yawoce dole yana ratsa ko wanne lungu, sannan shi kurmane da hakane duk wanda ya had'u dashi baya manceshi kana shi mai gsky da amanane da yawan ibada to sai Allah ya sanya soyayyarsa a zuk'atan bani adam. Uwa uba Allah ya yalwata mishi surarshi da kyau mai d'aukar hankali yana da muhibba, kima, daraja, kamala, haiba, da cikar zati, so wadannan abubuwan sukasa ya sanu tako ina. Alhamdulillahi kasuwarshi kuwa sai son barka dashi dama Ummi da Rahma sai godewa Allah suke suna k'arawa sabida sune kad'ai suka san kullum sai yasa dubu buyer a asusunshi, sauran na saman kuma da balance d'in machine dasu sukeyi buk'atun yau da kullum, ribar omo kuma yaci gaba da zurawa a asusun ribar pure water. Abota tsakanin shi da Jabeer da Hisham da Kabir kuwa sai gaba-gaba sun shak'u sosai yanzu ya saba da wani yaron shagon Alhaji ishaq Ibrahim shima yaron yana sonshi, sosai hakama wani shagon ba miskila Bello sun saba over amman shi ya girmi Saifuddeen sosai so da yake Saifuddeen ya gaya mishi sunan Abbanshi gareshi shiyasa yana kiran Saifuddeen da Bingel am d'ana kenan. Rayuwa ta mik'a d'aura kwalin ledodi a kafad'a da Saifuddeen yake yawan yi sai ya d'an canza mishi salon tafiya sai ya d'an karkace ka d'an mu samman ta samanshi karkacewar da bafa zaka ganeba sai in ka zuba mishi ido sosai baranma in ka sanshi kafin ya fara tallan ledan ne zaka gane hakan sosai, wannan 'yar karkacewar sai ta zama wani abu da yake jan hankalin mutane a gareshi domin daga saman wuyanshi zakaga time to time yana tonk'oshe wuyarshi irin yadda manyan sara kuna keyi sabida nauyin rawani da k'asaita, da yawa kuma cewa sukeyi kyanshi ne yasa yake hakan wai a zatonsu rigimace da izza, sabida in dai ka kalli yadda yake tafiya to sai kayi zaton d'an sarkine ko matashin d'awisu domin dama a nitse yake sai tafiyarshi da tsarinshi suka koma tamkar na jarumI R.K na seris film d'in Madubalah wanda aka tab'a nunawa a Bollywood in ka ganshi sai kayi zaton tsantsar izzace da gadara da tak'ama kasan cewarsa karma ba ko yaushe yake mgna ba sai wasu suke zaton miskilanci ne. Yakan je gidansu Is'haq time to time musamman in yaji zafi ya matsa mishi sai ya ajiye omonshi yaje yayi wonka ya canza kayan inda zaisa na is'haq sabida bashi da shamaki a gidansu is'haq so yawan tsabtarshi yasa kawai wasu ke masa kallon tabbas rigimace tunda gashi a wuni d'aya a kasuwa sai a ganshi da kaya kala biyu, in yaje gidansu is'haq yakan amshi wayar step mother in is'haq din su gaisa ta hanyar rubutawa juna text. Kullum duk bayan kwana uku zai sayi wakenshi mudu shida geroma haka sannan sugar mudu d'aya da rabi sai mai k'aramin galam da dabino mudu d'aya. Umminshi ta dama koko ta toya kosan a kai masallacin k'ofar gidansu. Yau jumma'a kana ana tsula zafin rana kowa ido yayi zuru-zuru sabida k'ishi da yunwa mazauna inuwama suna shan zafin azumin bare masu k'ananan sana'o'i irin Saifuddeen mai sai da leda da yan dako da yan garuwa da masu gonjo da kafintocin sama da kuma 'yan acab'a da direbobi. Gashi yau shine azumi na 20, Sosai Saifuddeen ke azabar jin k'ishi hakane yasa k'arfe hud'u dai-dai ya maida omo inda yauma ya samu riba sosai, dama ya gama had'a ribar leda wanda yanzu masu sayan sun d'an k'ara sabida karatowan salla yasa cini kaiya k'aruwa. Shagon ba miskila yaje yana isa Bello ya kalleshi cikin kula yace. "Bingel yau ba omon ne?." cikin gajiya ya lumshe ido tare da sharte zufar da yakeji da hankicib d'inshi cikin gajiya ya lumshe ido tare da mishi alamun akwai ya gajine yasa ya maida. cikin kalato yawu Bello yace. "Gsky kam bingel am azumin yau yanada dad'i." murmushi sukayi baki d'aya kana Saifuddeen ya nunawa Bella d'anyar shinkafa da fulawa da sugar da geron sai yaga kuma kamar bai fahimtaba hanne yasa shi zaro biro ya rubuta mishi cewa yana son d'anyar shinkafa da fulawa da sugar. cikin kula ya auna mishi kana ya bashi kud'inshi shi kuma ya bashi ledodin daya zuba shinkafar a ciki. Karb'a yayi sannan ya wuce ya sayo mai dasu yis, dan yana son a rink'a had'awa da masa a sadakan da ake kaiwa masallacin. Sai kuma ya sai kayan marmarin daya saba saya, sannan yaje layin masu nama, zabbi ya saya guda uku aka yanka aka fige aka gyarasu. sannan ya fito bakin inda Salisu zai sameshi nan ya irga sauran kud'in inda ya samu ya shigesu sosai yau dubu uku zaisa a asusunshi, yana zama ba jimawa Salisu yazo sauk'e
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148