Skip to content

Chapter 26

Chapter 26

Nakasa Ba Kasawa Bace Book One Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

wota mata kuma lokacin biyar saura aifa yace kawai su tafi gida, to dama shima Salisu ya gaji kawai sai suka kama hanyar dukku. Suna isa gida Hayatuddeen da Faruq suka tarbeshi, da murnarsu bayan ya ajiye ledidin yayiwa Ummi alamun tayi musu ferfesun zabbin da asuba suci ko da biredi da tea ai kam Raihana murna ta rink'a wai zata huta yin miyan asuba. Shi kuwa gefen Rahma ya zauna sai ya kuma manna kanshi a kafad'arta cikin nuna tsantsar alamun gajiya domin Saifuddeen yana da tsoron wahala to kuma Allah ya jarab ceshi da ita, cikin tausayawa ta shafa fuskarshi dan gaba d'aya jikinshi rawa yakeyi, cikin tausayawa tace. "D'an uwana sannu yau azumin da wuya anyi rana." ido ya lumshe yana mai jin azabebben k'ishi, a hankali ta kalli Ummi da tuni idonta sun cicciko da hawaye, sai ta kuma kalli Raihana cikin sanyin murya tace. "Raihana kai mishi ruwan wonka." da sauri ta mik'e duk da tana jin wahalan azumi amman tasan dole ya fita shan zafin rana, a randar tab'onsu ta d'iba saida ta cika mishi botiki sannan ta kai mishi bayan gida wanda yana wonke stab dan shi kad'ai ke amfani da bayan gidan tunda Nuruddeen da Abba suka rasu Hayatuddeen har yanzu bayan gidansu Ummi yake zuwa. Tana kai ruwan taje ta d'auko mishi kondon sosonshi ta kai mishi sannan tace. "Hamma na kai ruwan." kai kawai ya iya gyad'a mata kana ya k'ara lafewa jikin Adda Rahmanshi, jin hannun Ummi a kan gishinsa ne ya sashi d'ago kai ya zuba mata idanu, ganin alamun zatayi kuka sai ya yunk'ura ya mik'e jiki na rawa, cikin sanyi tace. "Babana baka da lfy ko." kai ya jujjuya mata a hankali kana yasa hannunshi kan cikinshi da yake a d'akale bafa irin d'akalellen cikin maceba a a irin nasu na maza, sai ya kuma nuna mata mak'oshin sa alum k'ishi yakeji, cikin kula tace. "Je kayi wonka zakaji sanyi Babana." Kai ya gyad'a mata sannan ya juya a hankali ya shiga kayan da zai sa ya d'auka sannan ya shiga bandakin, yana shiga ya zare kayan jikinshi duka sannan yaje ya zauna bisa dutsen wonkan da yaketa shek'i da yake a inuwa yake baiyi zafiba, surarshi ya k'arewa kallo idon ya zuba kan mararshi a ranshi yace. "Hmmm yau kam kaji haza bayan baccinma har b'uya kayi ka koma cikin cikina ko?." sai kuma ya fara watsa ruwan. To Alhamdulillahi da yayi wonkan ya ji dama-dama gashi yana fitowa ana kiran salla, al'wala yayi wanda tuni Ummi na gabanshi rik'e da dabino da surki mai d'umi, dabinon ya amsa addu'a yayi kafin yaci guda uku, da sauri ya jujjuya kanshi alamun shi bazai sha surkinba. infa da sabo Ummi ta saba don haka yake ba komai yake ciba kuma zai tace maka yana jin yunwa kana kawo mishi abinci in ya tsakuri kad'an sai ya cire hannu wai ya k'oshi. da sauri Hayatuddeen ya mik'o mishi pilet d'in su kankana to nan ya amshi fork a hannun Raihana sannan ya fara sokawa jikin kankanan da Rahma ta zuba mishi madara da sugar kad'an sabida ta sanshi da son zak'i, ido kawai Ummi ta lumshe tana kallonshi sai yana tuno mata k'uruciyar Abbanshi, bai shanye rabinshi bama yayi wani sassanyan gyatsa tare da mik'ewa wai ya k'oshi kenan, jin ana tada kabbarane yasa Ummi bata hanashi fitaba, shi kuwa kama hannun Hayatuddeen yayi suka fita zuwa masallacin. Suma su Ummi sukayi haramar yin sallan. Bayan an idar da salla, suna fitowa, Mudassir, Warisu, Salisu. Suka nufi cikin gidansu Saifuddeen kai tsaye a babbar taburmar da Ummi ta saba shimfid'a musu suka zauna. Rahma mace ta mik'e a hankali ta fara jero musu abin motsa baki, kankana da ayaba da dabinon suka fara ci, sunaci suna hira Rahma kuwa ita da kanta ta matso gefensu zama tayi tare da yi musu harara sannan ta jawo kulan dake gabanta cikin fidda numfashi tace. "Daga yau bazan sake biye mukuba, kun sani yi muku yambos wallahi ba k'aramar wuya na shaba kirba doyan nan wuya gareshi, gashi Raihana k'in tayani tayi wai ai nike biye muku." Saminu da yanzu ya shigo tare da Saifuddeen ne ya harari Raihana tare da cewa. "Yan ubanci zatayi mana shareta Adda Rahma ran salla ke kad'ai zamu bawa barka da salla." tab'e baki Raihana tayi tare da cewa. "Kada ku bani mana ni dama ban rok'aba." Muddassir ne yayi d'an gyaran murya kana ya kalleta cikin tsuke fuska da bada umarni yace. "Ni bazanma ci wannan yambos d'inba, yanzu ki d'an soya min dankali." tura baki tayi tare da mik'ewa tana cewa. "Ni wlh na gaji kuma yunwa nakeji." Ummi ce ta d'anyi dariya kana tace. "Zo Raihana taho nan ga dankalin dama na soyawa Bappa Alinku na kuma d'iba musu zoki basu nasan Mudassir so yake ya wahal min dake." da sauri Saminu yace. "To ni kuma indomi nakeso mai ruwa-ruwa yaji yaji da al'basa." dariya sukayi baki d'aya dan sun san bazata iya musa mishiba, sai kuma suka zuba musu ido jin tana ce mishi. "Yanzu ne kakeso ko sai kun taso daga tabsir ne zan maka?." ido ya lumshe kana ya zuba mata ido cikin sanyi yace. "Ki huta sai mun dawo zamuyi aikin tare." Ummi kam kauda ido tayi Warisu kuwa da Salisu tuni suketa hirarsu, Mudassir kuma tuni ya zuba musu yambos d'in har ya fara ci Adda Rahma kuma tea tai ta had'a musu, nan suka fara ci sunaci suna hira. Shi kuwa Saifuddeen gefen Ummin shi ya rab'a a hankali ya konta tare da d'ora kanshi a cinyarta, gyara zamanta tayi dan yaji dad'in konciyar, kanshi ta d'an shafa cikin ido ta zuba mishi ganin sosai fa ya rame hancin shi zuwet har bisa baki idanunshi sun k'ara fitowa, farinshi ya k'ara baiyana cikin kula ta kalleshi ganin ita yake kallo tace. "Tashi mana Babana kaje kaci abinci da yan uwanka ai zakafi jin dad'in cin." sanin in bai ciba hankalin ta bazai konta bane ya sashi yunk'urawa ya tashi zaune sannan ya amshi cup d'in da Adda Rahma ta cika da zazzafan tea mai k'auri sai k'amshi yake, gyara zamanshi yayi kana ya mik'awa Warisu hannunshi alamun ya bashi abinda suke ci d'in, ganin Warisu zai kwatso mishi da yawane ya sashi nuna mishi yatsa d'aya alamun guda d'aya zai bashi, kauda kai wWrisu yayi kana ya mik'o mishi guda biyu, fuska ya d'an had'e dan shi cikinshi ya cika da ruwan da yaketa sha, ya kuma san Ummi zata sashi dole ya cinye biyun da ya sako mishi, haka kuwa akayi dole ta sashi yaci sannan ta samishi soyayyan dankalin turawa, nanma yanaci yana d'an korawa da tea d'in a haka dai yaci kad'an. Jin an fara kiran sallan isha yasa suka mik'e duka dan yin al'wala, dai-dai lokacin kuma Ahmad ya shigo shida Raliyya, da sauri Rahma tace. "Ke Raliyya meya kawoki a daren nan?." kai ta d'an rausayar tare da gaida su Saifuddeen sannan ta zauna gaban Ummi cikin sanyi tace. "Kai Adda Rahma ai nida Ya Ahmad ne muka zo nayi kewanku ne especially Hamma Saifuddeen, shiyasa nace yau mu taho tare kuma tare zamu koma." Cikin fad'a Saifuddeen ya mata

Table of Contents

Chapters

148 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148