Skip to content

Chapter 73

Chapter 73

Nakasa Ba Kasawa Bace Book One Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
Download Book

d'an saki ajiyan zuciya, yayinda Ishaq ma yayi murmushi dan yasan mgnar Dr Aliyu gskyace tunda yana tare da masu matsalar a members en k'ungiyarsu ta Jonaqwd Gombe state chapter. Cikin kula da farin cikinsu yaci gaba da yi musu bayanin yadda zasu kula da shi a matsayinsu na 'yan uwanshi cikin kauda kai yace. Akwai dabaru da ake ba su musammn domin auratayyarsu, ga wadan da ba su iya mikewa sukan sadu da iyalan nasu a zaune wasu kuma suna iya dogaro da kafafunsu amma ba za su iya mikewa gaba daya ba sai dai hakan bazai hanasu sarrafa matansuba, mu samman in sun samu cikekkiyar kula da magunguna da allurai. Jan hankalin ga drevars na gida dana haya, domin a Nigeria an tabbatar da kiyasin cewa 70% na masu larurar a sanadiyyar hadarin mota ne suka samu matsalar Saboda rashin kyawun hanyoyi da kuma sakaci da gangancin su kansu masu tukin. Sannan da yawan masu larurar ba su da wadataccen hali shiyasa ake buk'atan tallafin gwamnati. Wasu sukan samu cutar wajen wasanni irin na sports haka kwallon kafa, ko tseren Mota da masu irin tsalle-tsalle ko a shiga ruwa duka dai da kuma yin galla yayin d'aukan aure da matasa keyi masu machine da keke napep da kuma motoci dan haka ni dai Aysha Aliyu Garkuwa ina kira ga matasanmu please ku kula domin zama lfy yafi zama d'an sarki, duk duniya babu abinda ya kai lfy dad'i da tsada. Mutum yakan daina feeling wadan nan gaba daya a daidai inda larurar ta same shi Ba ma idan aka ce ana zafi irin yanzu da zafin ke fara shigowa hunturu na fita Da yawansu ba sa iya barci. Sai an rinka daukar ruwa ana kwara musu, in babu AC a inda suken. Idan anyi saurin d'aukar mataki *ana warkewa!* kamar yadda muke tsammanin Saifuddeen zai iya workewa. Amma complete injury shi ke kawo permanent damage. Saboda wasu kasusuwan spinal din ne ke danne ita lakar To irin wadan nam abin da suke bukata ayi surgery na gwanaye doctors domin gyara zaman kasusuwan. Akwai wadanda Kuma wasu gabobin za su ci gaba da aiki wasu kuma ba za su ci gaba ba har abada sabida ita lakar had'e take da k'wak'walwa A bangaren kimiyya kuma k'wak'walwa ita ce gaba da kowace organ na jikin dan Adam to idan ta sami matsala kusan kamar dukkan jikin Mutum ne ya samu. Musamman spinal cord injury din. Da k'wak'walwar ta taho se aka shigar da lakar shine yake zuwa har daf da mazaunan mutum ta baya, ana kiran wurin da *coccyx* wato kashin bindi nan ne inda ita lakar ta kare a jikin mutum tun daga k'wak'walwa, wanda kowa in ya danna tsakiyar mazaunen sa tasama k'adan zaiji wannan k'ashin bindin ko wanda ramarshi ta tsananta ana iya ganin alamarshi. To shiyasa ko duka! kamar yadda akayiwa Saifuddeen ko matsanan cin buguwa a wannn kashin bindin yakan iya haifar da matsalar. Kana a tare da ita lakar k'asan kasusuwa ne suka rufe ta domin ba da kariya a gareta wanda wanan hikima ce ta Ubangiji, domin duk abin da yake da matukar amfani da mahimmanci a jikin d'an Adam to bai barshi a waje a fili dole sai ka ga an samar masa *Garkuwa* wato protection. Kamar ita k'wak'walwa d'in sai aka sanyata cikin kokon kai Saboda mahimmancin ta. Gashi abu k'iris ke iya damaging dinta in ace wai a sarari take Shiyasa za kuga an dage an bugi mutum akai amma sai dai a tab'a kokon. Shiyasa kuma idan aka samu buguwa mai tsananin kai ke samun matsala Sanan sauran organs din jikin mutum kmar irin su zuciya, koda, hanta, hunhu, ai idan kuka duba ko da a jikin dabba da aka yanka ne, za ka ga duk a boye suke ai?." ya karishe mgnar da zuba musu ido tare da lamun tambaya da son jin amsarsu da zata nuna tabbas hakane. Su kuwa a tare sukace. "Tabbas wannan haka yake." murmushi yayi cikin jin dad'in suna fahimtar mgnarsa yaci gaba da cewa. "Bari in shaa Allah zan nuna muka wasu hotunan jikin Saifuddeen d'in da muka d'auka, domin yadda za ku k'ara fahimtar yadda case din spinal cord injury ke faruwa Lamarin tsakanin k'wak'walwa ne da ita lakar sai kuma *nerves* kamar ace wasu nauin wayoyin lantarki, da suka zagaye dukkan sassan jikin d'an Adam to katsewar connection tsakannin nerves din da k'wak'walwa shi ke sanya har Mutum ya daina jin feeling a wasu gabobi na jikinsa." sai ya kuma nisa alamun yazo k'arshen bayanin da zai musu, wanda zasu iya fahimta a matsayinsu na wata rana wani zai iya neman taimakonsu, mik'a ya d'anyi kana yace. " Yauwa sai maganr kud'in keken hawansu wanda ya kamata ku sama mishi kana a sarrafa mishi abin magna a jikinshi. Kana duk da kasancewarmu nan orthopedic hospital ne, amman zanfiso ku fitar dashi k'asar woje in har fa kunada damar fiddanshin. domin can sun fimu kayan aiki daci gaban kimiya." Cikin sauk'e ajiyan zuciya Ishaq ya gyara zamanshi fahimtar Dr ya gama bayanin da zai musu, cikin yak'ini da niyar tallafawa abokin nashi yace. "To ba matsala Dr mun gode matuk'a da kulawarka garemu da k'arin bayani da kayi mana, yanzu abinda muke son sani, wacce k'asace ta fi shahara da gwarewa da iya aikin masu larurar, muna son taimakonka domin in sha Allah zamu fitar dashi in Allah ya yarda zamuyi iya yinmu." muskutawa Dr Aliyu yayi alamun ya d'an gaji da zaman kana yace. "Yauwa batun k'asar da ta fi shahara wajen aikinsu na san akwai kasar India akwai Singapore da U.S. lokacin dana samu nawa hatsarin ni Singapore aka fiddani, kuma Alhamdulillahi gashi na samu sauk'i tunda ni kafin a kaini bana iya tashi zane, amman tunda akamin aiki na samu sauk'i har nayi aure har matata ta haihu." cikin sauri Hayatuddeen da Ahmad suka had'a baki wurin cewa. "To shima d'in a kaishi Singapore d'in kawai." kai ya girgiza musu kana yace. "Shawara in kun amince a kaishi India, domin acan nayi karatu kana inada abokai biyu wadanda suna cikin manyan likitocin da duniya keji dasu a wannan fannin, so kuma zan iya muku hanyar ganisu a sauk'ak'e, sai daifa fiddashi india d'in zaifi tsada, amman kuma zaifi samun kulawa ya kuka gani?." ya karishe mgnar yana kallon Ummi da Dr Adnan cikin gamsuwa da k'arfin zuciya Ummi. Ta bud'i baki da nufin zatace a kaishi india, sai kuma tayi shiru tana kallon Ishaq da ya gyara zamanshi kana yace. "Ba matsala zamu kaishi india d'in ka fara yi mana hanyar had'uwa da Doctors d'in insha Allah kud'i bazai zama matsala ba." hakama Ahmad yace shima, Dr Adnan ma kuwa yayi na'am da hakan, Ummi kuwa addu'a ta rinka yi musu tare da godiya da sanya musu al'barka. daga nan suka tattauna abinda duk ya dace kana suka tashi suka fit. su kuwa Doctors d'in suka fara shirin bashi taimakon gaggawa kafin a gama cuku-cukun fitar dashi India d'in. A can room d'in da Saifuddeen ke kwance kuwa, fuska ya tsuke tare watsawa Amina wani zazzafan kallon dayasa, ta had'iye regowar mgnar da tayi niyar ce mishi mai k'aton joysti...! BY *GARKUWAR FULANI* 8/18/20, 7:52 PM - Ummi

Table of Contents

Chapters

148 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148