Skip to content

Chapter 87

Chapter 87

Nakasa Ba Kasawa Bace Book One Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
Download Book

cewa. "Yauwa Bappa Ali yanzu mu fita, dan ba'a son yawanta surutu a kanshi." Ahmad ne ya motso jikin gadon hannunshi yasa ya shafa fuskar Saifuddeen cikin sanyin lafazi yace. "In sha Allah zaka samu lfy in Allah ya yarda zamu jure ko wanne wuya zamu kuma dage da addu'a in sha Allah zaka samu lfy." sai kuma yayi sauri ya juya ya fita dan jin hawayenshi na zubowa. Da sauri Bappa Ali yabi bayanshi, a wannan wurin suka zauna, shi kuwa Hayatuddeen a hankali ya bud'e baki cikin sanyi ya kamo hannun Hamman nashi murya can k'asa yace. "Ummi tace in gaidaka da jiki, Adda Raihana ma tace in gaidaka." sam baya iya motsa komai na jikinshi shiyasa sai da ido yake musu mgn, yana son ya d'ago tafin hannunshi ya sharewa Hayatuddeen hawayenshi dake kwaranyowa amman bazai iyaba, hakan ne ya sashi rumtse ido yana mai jin ciwo a duk wani sashi na jikinshi, ganin haka yasa Dr Adnan yaja Hayatuddeen suka fira. Bayan fitarsu da kamar 23 minutes su Dr Acash suka fito suma. Dr Malik yace yana son ganin su da yamma. to sukace sannan duk suka nufi masauk'insu. Zaune suke a parlour kowa da abinda ke ranshi, Dr Adnan ne yayi gyaran murya cikin sanyin sauti yace. "Bappa Ali munyi yawa anan dole wasunmu su hanzarta komawa gida Nigeria dan zamanmu zai k'ara tada hankalin Ummi, amman in wasu sun koma sun gaya mata jikin da sauk'i zatafi samun nitsuwa." gyara zama Bappa Alin yayi tare da cewa. "Hankali na ya tashi da yanayin jikin Saifuddeen, bana son inyi nesa dashi." sai dai ko in Ahmad da Hayatuddeen ne zasu koma." cikin sauri fuska cike da rauni Hayatuddeen yace. "Bappa Ali in tafi in bar Hamma na kenan?." shi kuwa Ahmad kai ya jujjuya tare da cewa. "Kayi hak'uri kawu Ali, komarka nada mahimmanci dan Ummi zatafi gamsuwa da kalamanka, sannan kasuwancinmu yafi buk'atarka akan ni, kuma kaga shima Ya Adnan ya kusa komawa, in mun tafi yazo shima ya tafi sauran kai d'aya, bazaka iya d'awainiyar ba, amman yanzu in kaje ka kwantar musu da hankalin bazai jimaba shima ya Adnan zai komo ya kuma kontar musu hankali ni da Hayatuddeen kuwa zamu kula da komai in munga sauk'in jiki sai nima in koma sai su Ummin suzo su dubashi." shiru sukayi baki d'aya dan jin ta bakin bappa Ali. Cikin gamsuwa yace to ba matsala in sha Allah cikin satin nan zan wuce. sosai Dr Adnan yaji dad'in hakan. Da yamma Dr Adnan da Bappa Ali suka shirya suka koma cikin asibitin kai tsaye office d'in Dr Malik Khan suka wuce. Nan suka samu Dr Acash ma a nan bayan sun gaisane Dr Acash ya gyara zamanshi tare da fuskantarsu da kyau cikin nitsuwa yace. "Jikin Saifuddeen dai da sauk'i sosai, amman akwai buk'atar k'arin kula da jinyarshi, in da hali nanda wata biyu zuwa uku akwai buk'atar canji asibiti daga nan New Delhi za'a maidaku Mumbai zuwa babban asibitin. Orthopedic hospital zanyi k'ok'arin hadaku da d'aya daga cikin manyan doctors d'in. Physiotherapist domin sune suk'eda gwarewa da k'ok'arin farfad'o da aikin lakar jiki ga wad'anda akayiwa aiki dama wanda ba'a samu damar yi musu aikin ba. To shiyasa nake son turaku garesu in munyi sa'a zai samu sauk'i cikin k'ank'anin lokaci tunda an mishi surgery sannan an sama mishi kular likitocin fisiyo to muna da k'arfin guiwar samun sauk'inshi." cikin gamsuwa Dr Adnan yace. "Ba matsala in dai hakan ya kamata ayi duk abinda ya dace kawai." shima bappa Ali cikin gamsuwa ya gyad'a kai, sai kuma suka nitsu jin Dr Malik Khan na cewa. "Alhamdulillahi ko yanzu muna ganin alamun sauk'i sosai a jikinshi alamun aikin da akayi mishi yayi kyau to amman yana da kyau ku kaishi Mumbai d'in domin acan zai samu duk abinda ya dace a sauk'ak'e, likitocin zasu rink'a kula dashi sosai dan canma asibitin mune, munfi zama a canma nan duk wata sa huɗu muke zuwa muyi aiki, so a can akwai. Orthopedic surgeon likitocin da suka k'ware a fannin k'ashi, ga kuma neurosurgeon da suka kware fannin k'wak'walwa, to suke kula da masu larurar. So zai samu wadacecciyar kulawa da treatment mai kyau da ink'anci, da taimaka musu wurin movement motsa jiki da da kuma yin exercise a rink'a strengthen muscles d'in manual therapy. koyar dashi duk wani abinda ya dace tare da bashi shawarwari yadda zai kula da kanshi bayan an sallamesh. Sai dai kam akwai cin kud'i amman in sha Allah zai samu lfy." cikin gamsuwa Bappa Ali ya kalli Doctors d'in tare da cewa. "Ba matsala aiyi duk abinda ya dace fatana samun lafiyar d'an d'an uwan na." murmushi Dr Malik Khan yayi tare da cewa. "To Alhamdulillahi yanzu dai muna bashi Drugs masu rage mishi symptoms d'in ciwon sosai, kuma Alhamdulillahi yana jin dad'insu, so yana gama shansu zamu yi muku transfer zuwa can d'in." sosai Dr Malik Khan ya musu cikekken bayanin da zai sama musu nitsuwa har saida yaga hankalin su ya kwanta sannan ya sallamesu suka fita suka tafi. Daga ranar ba'a sake barinsu sun ganshiba sai bayan kwana hud'u wanda kuma a ranar ne Bappa Ali zai koma gida Nigeria. Da sanyin safiya suka nufi cikin asibitin bisa jagorancin Dr Malik Khan suka samu suka shiga suka ganshi, kuma Alhamdulillahi sosai suka samu nitsuwa dan sunga alamun d'an sauk'i a jikinshi, suna fitowa Bappa Ali ya shiga taxi ya nufi airport k'arfe sha d'aya dai-dai jirginsu ya tashi. Su kuma kai tsaye masauk'insu suka koma. Bappa Ali kuwa komawarshi ya samawa Ummi nitsuwa sosai dan ya kontar mata hankali ya b'oye mata batun sauyin asibiti ya samu kuma ya hanata tafiyar yafi son sai sun koma Mumbai d'in taje. Warisu da Mudassir da Bello kuwa suna kula da kasuwancinsu yadda ya kamata. Bappa Ali ya dawo da kwana biyar Salisu yaje India ya duba jikin abokin nashi kwana biyar yayi ya dawo gida Nigeria shima ya k'ara kontarwa Ummi hankalinta sosai. Sai dai sunyiwa Ishaq bayanin komai, yaso yaje sai suka hanashi a kan ya bari sai sun koma Mumbai d'in sai yaje da Ummin dan dole ya hak'ura. *** Yau watan su Saifuddeen d'aya da kwana goma kwanansu arba'in kenan a can, kuma yau ne zasu wuce Mumbai tare da jagorancin Dr Acash prasat. K'arfe biyar dai-dai jirginsu yayi sauk'an ank'ulu a babban filin shige da ficen. Hilton Mumbai international Airport. Daga nan Airport d'in kai tsaye asibiti suka wuce. *Nanavati super speciality hospital*. Shine sunan dake liƙe asaman asibitin da akayiwa su Saifuddeen transfer. Asibitine da haɗuwarsa ya zarce misali don ya ƙawatu sosai, komai na cikinsa gwanin burgewa ne, ko ina kakai dubanka zakaganshi ya ƙawatar gwanin ban sha'awa, don sosai haɗuwarsa ya zarce na garin New Delhi. Mutane ne keta hada-hadan shiga da fice daga cikin asibitin. Koda suka ƙaraso cikin asibitin ɗaki na musamman aka samawa Saifuddeen tare da taimakon Dr Acash prasat, Dr.Adnan da Ahmad ne suka ɗaga Saifuddeen daga kan weelchair ɗin da suka turosa akai, kan faffaɗan gadon dake cikin ɗakin wanda yaji lallausan katifa suka shimfiɗesa, ahankali ya maida kyawawan idanunsa ya rufe tare da ɗan sauƙe ajiyar zuciya. Kafaɗansa Dr.Adnan ya ɗan dafa a hankali, jin an

Table of Contents

Chapters

148 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148