Chapter 19
Chapter 19
so zasu buk'aci ruwa da kayan zak'i. cikin sa'a kuwa a safiyar yayi ciniki kusan na 3,500 sha d'aya dai-dai ya kuma komawa da nufin k'aro ruwan sai ya samu Baba Bello ya iso yazo wurin yana nemanshi, haka yasa ya ajiye botikinshi anan shagon su Kabir kana suka juya suka nufi dilan ledodin. Bayan an gama warewa Baba Bello adadin da yake amsa kullum, sai aka rubuta sunan Saifuddeen dasa hannun shi dana baba Bello kana akasa kud'in kayan da akabashi ganin yawan kayanne da yawan kud'in yasa Saifuddeen yiwa Dottijon alamun. "Kayan basuyi yawaba kuwa?." Murmushi Baba Bello yayi kana ya fara loda ledodin a k'aton kwalin dake bayan kekenshi, saida ya loda kusan rabin ledodin kana ya hau kekenshi sannan ya kalli Saifuddeen cikin yin kasa da murya yace. "Kada Ka damu ai zan had'aka da customers d'ina duka, kaga duka-duka kayan dubu hamsin nake amsa dama, nakan sa na ishirin da biyar, in fita inje in rarraba in ya k'are inzo in kuma kwasar rabin. Yanzu muje duk zamu rabashi sai mu dawo mu debi sauran." cikin gamsuwa ya gyad'a kai kana yabi bayanshi. tafiya kad'an suka isa shagon wani mai saida takalma bayan sun gaisa Dottijon nan ya d'ebo banduran leda takwai, ya bawa Saifuddeen kana ya juyo ya kalli mai shagon tare da cewa. "Alhaji bala ga Jikana ya fara kawo muku daga yau, insha Allah kullum zaike kawo muku kamar yadda nakeyi daku sai in Allah ya kaimu bayan salla." wanda aka kira da alhaji bala kuwa cikin kula ya irgo dubu 4 ya bawa Dottijon kana yace. "To baba Bello Allah ya kaimu bayan sallan, Allah ya sadamu da al'khairi." Amin Amin, yace kana suka shige shago na gaba nanma ya basu kaya suka bashi kud'i. haka dai sukayi tayi har suka gama wanda suka kwason kana suka koma suka kwaso sauran kashi d'ayan. Kai tsaye shagonsu Jabeer sukaje inda sukace a basu na dubu 5, nanfa Saifuddeen ya basu suka bashi kudin na jiya ya bawa baba bello, Jabeer nata musu tsiya wai. "Tab ku dai kam kun more dan ko bamu sayarba ku dai kun sayar." dariya sukayi kana sukaci gaba dan inda sabo sun saba da shek'iyancin Jabeer. daga nan suka zagaya har layin masu kayan kitchen nanma shagonsu Hisham suka saya, sai kuma suka mik'e babban layi har kan shagunan ba miskila, cikin sa'a suka sameshi shida kanshi bayan baba bello ya mishi bayanin Saifuddeen ya gamsu kana yace. "To Baba Bello Allah ya taimaka mana, yanzu ni daga gobe ya rink'a kawo min na 15k dan shaguna na babbar kasuwama za'a rink'a kai musu da na kasuwar mata da shagunan cikin unguwanni dan naku ledodinku suna da kyau, muna jin dad'insu." shiko Saifuddeen murmushi yakeyi yana ganin darajar mutumin sabida duk inda yaranshi sukayi awu sai ya amshi kwanon awun ya kamfata ya zuba a ledan wanda aka gamawa awun, yara sai godiya sukeyi. daga nan suka ci gaba da rabawa har layin masu kayan kolliya. Wasu na 5k wasu 4k wasu 3k wasuma na 1k wasu ma na 500 yayinda wasu 6k ko 7k kowa dai dai-dai cinikaiyarshi yake karb'a Koda suka gama sai suka tafi can dilan nasu, a hankali baba Bello yaja hannunshi suka d'an koma gefe, kana ya fito da kudin da suka tattaro ya had'a kansu, sannan ya irga inda ya samu kud'in dubu hamsin da shida ne da d'ari uku. Gyara zama yayi kana ya ware dubu hamtsin sannan ya kira d'aya daga cikin yaran shagon ya bashi kudin ya irga, sannan ya d'auko wani babban littafi yaja gud a kan sunan baba bellon tare da rubuta bama binshi ko asi, sai bayan salla in ya dawo. Sai kuma yasa sunan Saifuddeen k'asan na Baba bello tare da rubuta . "Munada kayan dubu hamsin a wurinshi." sai ya kuma basu littafin sukasa hannu shima yasa hannu daga nan ya koma bakin aikinshi. Su kuwa su Saifuddeen cikin nitsuwa Baba bello ya kalleshi tare da bashi 2k sannan yace. "Kaga wannan ribanane na jiya, ladan yawon da nasha yi cikin rana, kuma kaima zaka iya samun haka a kullum koma fiye da hakan cikin duk kayan dubu goma ina samun ribar dubu d'aya da dari biyu, wani lokacin in naga kasuwa bata gudu duk bandir din dubu goma sai inbi dubu d'aya rak kaga kenan duk fakitin dubu d'aya ina bin nera d'ari d'aya kacal ne, kuma Alhamdulillahi a cinikin da nikeyi dubu hamsin kullum ina samun dubu shida ko biyar in na rage farashi na, ta iya yiwuwa kai ka samu fiye da haka tunda kai yanzu ana hidiman cinikaiyan salla, dole masu shaguna suna k'ara sayan leda, kaga misali yanzu ba mishkila daga sayan na dubu 5 yanzu yace gobe na dubu 15 zaka kai mishi, kaga Alhamdulillahi kasuwa ta fara a sa'a, dan haka kai gobe kayan dubu 60 zaka amsa, yanzu zan gayawa shi Alhajin in dai ka buk'aci k'ari to ayi maka." cikin jin dad'i da tsananin mamaki Saifuddeen yake kallonshi domin jin k'udurar ubangiji. Mutun nawa ke raina kasuwar leda rashin sanin al'barkan dake cikinta ne yasa haka da yawa raina riba ke wahal da matasanmu da ganin sunfi k'arfin sana'a kaza sai kaza ko a a su sunyi karatu sunfii k'arfin talla a kasuwa sai zaman office. cikin kurmanci yayiwa baba bello godiya tare fatan al'khairi. Shi kuwa Baba bello 2k d'in ya kuma bashi tare da cewa. "Amshi wannan ka sayawa Mamanka sugar ka kai mata taci al'barkacin sana'ata." Da sauri ya girgiza kanshi alamun a a bazai amsaba ai ya gama mishi komai ma daya bashi aron sana'arshi ba tare daya mishi hasadan abinda zai samuba. Shiko Dottijon cikin girma da isa yace. "Bana son musu a tsakaninmu da mahaifinka ne ya baka zaka k'i amsane? niko da ace Allah yasa inada d'a da na bashi ai bazaik'i amsaba sai daima yace in k'ara mishi dan haka maza karb'i kud'innan." cikin tsananin ganin darajar Dottijon yasa hannu ya amshi 2k d'in kana ya mishi godiya. Shi kuwa Baba bello, ubangidan nasu yayiwa bayanin kan ba mmki Saifuddeen ya nemi k'arin leda. cikin mutuntaka ogan nasu yace. "Ba matsala aimu haka mukeso." daga nan ya sallamesu, kana ya yafito Saifuddeen sannan ya hau kekenshi, yana janta a hankali kana Saifuddeen na binshi a baya har sukaje bakin titi, cikin kula ya bawa Saifuddeen hannu da sauri Saifuddeen ya bashi nashi hannun sai kuma ya zuba mishi ido jin ya rik'e mishi hannun cikin bada shawara yace. "Ita sana'a bata yiwa mutun yawa, kaga shi leda cikin awa uku duk zaka gama kaiwa kostomominka ka kuma tattara kud'i har ka biya kana ka zare ribarka. To in dai ka gama da wuri to zakafa iya saida ruwanka d'in in kaga alamun zai saidu, in kuma Kaga bazai saiduba tofa kada ka zauna banza ka samu sana'ar da zaka had'a dana ledan kafin bayan sallan ka komawa ruwan." Cikin gamsuwa ya jinjina kai alamun in sha Allah hakan zaiyi. shi kuwa Dottijon ya jima yana mishi nasiha da rik'o da amana da tattali, sannan daga bisani sukayi sallama shi dottijon ya kama hanyar gidanshi kana shi kuma Saifuddeen ya koma cikin kasuwa ya d'auki bitikinshi ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148