Chapter 2
Chapter 2
sauran yayunshi tuni ya meda hankalin kan hadda da sauran littafai da ake musu a isilamiyarsu. Saifuddeen yana ta murnar zai tafi JSS two wata rana kwatsam ya tashi da wani irin azabebben zazzabi mai tsananin zafi, kwana yayi yana firgita, da safe kuwa yana tashi sai mura ba tari amman yanzu yanzu hancinshi na zubda ruwa kana hancin yayi jazazir hakama idanunshi, ganin haka Ummi ta kama hannunshi taje ta nunawa wata makociyarsu tsohuwa iya shatu kakar Salisu abokin Saifuddeen, tana nuna mata jikin Saifuddeen d'in. Tana gani tace k'end'ace bak'on daurane zata fito mishi ga kuma azabebben zazzab'in sank'arau daya rufeshi, haka yasa ta nemi tsink'aro da gero ta barzasu ta jik'ashi da ruwa sannan ta kurba sai ta fesa mishi a jikinshi, cikin ikon Allah kafin dare duk Sun feso sun fito birjink a jikinshi har cikin tafin k'afafunshi zazzabin sank'arau kuma tamkar zai hallakashi. Koda dare yayi Ummi ta d'aukeshi suka koma side inta, abu kamar mafarki koda gari ya waye sai aka samu jikin Saifuddeen yayi sumut duk bak'on dauran nan ya b'ace ya koma cikin jikinshi ya k'ume yaro sai karkarwa yakeyi dan zafin zazzabi ga kuma sank'arau da ya hanashi sukuni wanda har cikin kunnenshi yakeji yana bada sautin dummmm, ba irin mgnanin da ba'a bashi amman sunk'i su kuma fitowa a lokacin kuma ba'a wani damu da batun asibitiba ko riga kafinshi ba'a fiye yiba a garin. haka dai Saifuddeen yayi ta shan wahalar sheretuwannan da zazzafan zazzab'in sank'arau daga k'arshe yayi sanadin kuram tashi. Wannan al'amari ba k'aramin girgiza family ensu yayiba don Saifuddeen yarone mai shiga rai, gashi da nitsuwa da al'kunya iyaye da da 'yam suna matuk'ar sonshi ran da aka gane Saifuddeen ya zama kurma a ranar anga tashin hankalin Bello Abba kenan hakama Nuruddeen daya dawo makaranta aka gaya mishi, kuka yayi tayi dan duk k'annenshi yafi k'aunar Saifuddeen Hayatuddeen kuwa lokacin shekaranshi 4 so baisan meke faruwa ba yakan dai yi kuka in yaga suna kuka. A Daren ranar jikin Abba ya tashi a wannan ranar ne karo na forko da ya rink'a ihu tamkar yaro k'arami. K'arfe biyu dai-dai na dere ya kama hannun Saifuddeen dake bacci ya mik'ar dashi, kana ya jashi suka fito haka ya rink'a janshi koro-koro duk inda suka samu masallaci sai ya sashi suyi Al'wala suyi nafila raka biyu kana suci gaba da tafiya. Saida akayi sallan asuba sannan suka dawo gida, nanma dan yaga Saifuddeen d'in yanata kuka. Suna dawowa Ummi ta jawo d'anta ta ruggumeshi cikin kuka take tambayarshi ina sukaje, baki ya bud'e da nufin ya kuma gwada yin mgna amman ina ya kasa, hakan ya sashi kife kanshi jikin gini yana wani irin gurnanin azabebben kukan da duk mai imani sai ya tausaya mishi babu mai sanin zafi da kun'an da yakeji a ranshi sai wanda ya tab'a shiga irin wannan halin ace an haifeka lfy ranatsaka nakasa ta sameka, so yake ya bud'i baki ya yiwa Umminshi bayanin yadda yakeji amman ina Allah bai bashi damar hakanba ganin ya kuma kife kanshi jikin ginin ya sake zazzafan shesshek'an kukane yasa Yayanshi mik'ewa ya nufi inda yake. Da Sauri Nuruddeen ya kamoshi, hannu yasa ya tallabe kanshi cikin tsananin kuka da tausayawa k'anin nashi murya na rawa yace. "Saifuddeen...!!! BY *NAKASA BA KASAWA BACE* *PAGE 2* NA *AYSHA ALIYU GARKUWA* πππππππππππππ _Ga masu buΖatar biyan kuΙin karanta wannan littafi na Nakasa ba kasawa bace.Ζowa a buΙe take, turo katin mtn na 300 kacal ta wannan layin 09097853276. Ko kuma ka/kiyi transfer ta bank account na 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ka/kiyi screenshot shaidar biyanki ki turo min, sabida kids samu damar karantawa koda na gama free page_ "Saifuddeen magana kake son kayi ne?." cikin tsananin kukan ya rink'a gyad'awa Nuruddeen kai. Duk da k'arfin hali irin na Ummi tuni kuka takeyi dan tausayin d'an nata wanda yaci sunan babanta. shi kuwa Nuruddeen cikin mamaki ya kalli k'anin nashi cikin kad'uwa yace. "Kana ji nane idan nayi Mgna kana gane me nake cewa ne?." kanshi ya jujjuya kana ya zame hannunwan Nuruddeen daga rik'on da ya mishi sannan ya tsuguna a gaban Nuruddeen d'in tafin hannunshi yasa ya lailaiye yashin tsakiyar gidan nasu kana yasa yatsarshi ma nuniya ya fara rubutu da harshen fullanci yace. "Ya Nuruddeen bana jin kuma naji na kasa yin mgna, cikin mak'ok'orona kamar an cusheshi kunnuwana sunyi dim bana jin komai, Amman da ina ganin bakinku ina gane abunda kuke fad'a." sai ya kuma d'ago kanshi ya kalli Nuruddeen daya rusuna yana karantar rubutun yana kuka tamkar an musu mutuwa, hannu yasa ya share hawayen fuskar Nuruddeen d'in kana yaci gaba da rubutu da harshen hausa yace. "Ya Nuruddeen ku nema min mgni mana, insamu irink'a Magna kamar kowa, ku kaini a bud'e min kunnena mana in rink'a jin muryar Ummi na da naku ku rink'a hira dani." Ruggumoshi Nuruddeen yayi tare da sakin kuka murya na rawa yace. "In sha Allah zan nema maka mgni Saifuddeen zan tattare dukkan buk'atun rayuwata zan jinginesu zan gina taka rayuwar, don gobenka tayi kyau." Sai ya kuma tsaidashi tare da matsawa baya suna fuskatar juna yace. "Saifuddeen kana gane abinda nike fad'i maka?." kai ya gyad'a mishi, da sauri alamun eh yana ganewa, ganin haka Nuruddeen yayi wani murmushi da yafi kuka ciwo a zuciya tare da cewa. "Saifuddeen kayi murmushi kamar yadda nayi." ba musu yayi murmushin da har saida dimples enshi duka uku suka lotsa biyu na kumatun gefe dama da gefe hagu d'aya kuma na tsakiyar d'an gemunshi, murmushin ya kuma fad'ad'awa ganin itama Ummi tana murmushi still su duka hawaye na kwaranya a idanunsu, Abba kuwa tuni ya mik'e bisa taburmar dake tsakiyar gidan da yake konciyan zafine, kwanan woje akeyi, kuma har yayi baccin da ya kwana bayiba. Shi kuwa Nuruddeen hannunshi ya d'aura kan k'ahon zuciyarshi kana ya fara mgna yana murmushi still hawaye na zuba yake cewa. "Saifuddeen *Babu nakasasshe sai rago*, kasa a ranka ita. Nakasa ba kasawa bace, in sha Allah ni d'an uwanka Nuruddeen zan baka dukkan kulawa zaka rayu kamar ko wanne mai ji da gani da mgna, kada ka kareya shi nakasa baiwace ta Allah wonda yakewa wanda yakeso, lokuta da dama bahaushe na karin mgnar da kan zama izina misali inda suke cewa, wani hanin ga Allah baiwane." sai ya kuma sharte hawayenshi kana yaci gaba da cewa. "Zan nema maka mgni iya raina da mutuwa, amman kasa a ranka mgni baya canza k'addarar mutun, kasa aranka wani hanin ga Allah baiwace. Kasa a ranka Allah yayi maka rahamar tsare maka harshenka daga sobon Allah ne kasa aranka Allah ya tsare maka kunnenka daga jin zantuka na haram ne da aikata sabon Allah, kamar yadda haka abin yake ga makaho Allah ya tsare mishi idanunshi daga ganin Haram, Saifuddeen zan yi iya iyiwana kan ciwonka dana mahaifinmu har sai dai in yafi k'arfina." tuni Rahma da Raihana suketa kuka, Hayatuddeen ma dake gefen Ummi kuka yakeyi ganin yayunshi na kukan. Kuka sosai Ummi takeyi dan tausayin Nuruddeen yaro k'arami Allah ya jarab ceshi ya d'ora mishi nauyin jinyar uba da k'ani bugu da k'ari shike ciyar dasu, domin sam Abba baya iya noma makaranshi sai su murdeshi haka yasa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148