Skip to content

Chapter 123

Chapter 123

Nakasa Ba Kasawa Bace Book One Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
Download Book

harsuka iso gaban tangamemen gate ɗin gidan, horn Sule driver yayi inda take maigadin gidansu Zaleehan ya wangale musu gate, acikin compound ɗin gidan Sule driver yayi parking motar, daidai lokacin Ya Aminu ya fito daga ɓangaren Mamy hango Saifuddeen dake ƙoƙarin fitowa amota da yayine yasanyashi ƙarasowa garesu. Da turarenta mai azababben ƙamshi ta feshe gaba ɗaya jikinta, wani ɗan siririn mayafi mai kalan kayanta ta yafa daga kan wuyanta zuwa ƙugunta, yanayin yanda dogon baƙin gashinta ya kwanto akan gefen wuyanta shi ya matuƙar ƙara ƙawata ado da kuma kyawunta, wani takalmi mai uban tsini ta sanya aƙafafunta, cikin takunta mai nuna tsantsar aji, ƙasaita, wayewa, da kuma jinkai tafito zuwa falo, nan ta iske Mama da kuma Zahira suna hira, duban tsab Mama tayi mata fuska shafe da toka tace. "Sai ina?." Zama tayi akan hannun kujera tare da ɗan turo bakinta gaba murya acushe tace. "Makay zanjeni yin shooping". Baki Mama ta taɓe tare da gyara zamanta ta fuskanci Zaleehan, fuskarnan tata sam babu alaman fara'a tace. "Ya kukayi da banzan gurgun da yazo wajenki jiyan?." Lokaci guda yanayin fuskar Zaleeha ta sauya kala domin tunowa da baƙin cikinsa da tayi, cikin bayyana tsantsar tsanarsa da tayi tace. "Na musu bana sonshi." Ƙwafa tayi tare da ɗan gyara zamanta tacigaba da cewa. "Wai harni wani banzan MUSAKI zaizo yace yana son ƴata hmm!." Murmushin jin daɗi Mama tayi tare da ci gaba cewa. "Ae ni banga laifinsa bama, dama ni tuncan wannan ɗan iskan aikin naki na Babu maraya ne, ko Nakasa ba kasawa bace ko mene yake da suna, sam ba ƙaunarsa nake ba, amma dayake ke uwar taurin kaine haka kike zuwa cikin nakasassu musakai kita washe haƙora kina naɗan muryarsu wai ke adole mai tausayi ƙaunarsu, to ai gashinan kin fara ganin sakamako tunda dai har Kurma kuma gurgu yasamu daman biyoki har gida da maganar soyayya. Hannu Ya Aminu ya bawa Saifuddeen suka gaisa amutumce, nan Ya Aminu dakansa yayiwa Saifuddeen jagora zuwa BQ, shikam har acikin ransa ya yaba da nutsuwa da kuma haiba haɗi da kwarjini irinta Saifuddeen, koda Ya Aminu yayi masa jagora zuwa BQ cewa yayi dashi bari ya ƙira masa Zaleehan, cikin body language Saifuddeen yace "To." Tare da yiwa Ya Aminu'n godiya. Ɗan ƙaramin bakinta taƙara cunowa gaba, tare da gallawa Zahira dake ta dariya ƙasa ƙasa najin cewa wai kurma kuma gurgu yazo wajen yayartata da ƙoƙon barar soyayya, baki Zaleeha ta buɗe don kaftawa ƙanwartata rashin mutumci shigowan Ya Aminu ne yasanyata saurin haɗiye maganan dake ranta, dan da tayi niyan aunawa mayataccen gurgun zagine, kana daganan saita ci mutumcin Zahira dakeyi mata dariya. Duban Zaleeha Aminu yayi fuskarnan tasa sam babu alaman annuri akanta, cikin tsare gida yace. "Ke Zaleeha kije kina da baƙo a Boys Quaters." Wani irin faɗuwa gaban Zaleeha yayi, cikin sarƙewar murya tace. "Ni...Ni kuma Ya Aminu?." Harara Ya Aminu ya watsa mata cikin yanayinsa na rashin fara'a agaresu yace. "Da akwai wata Zaleehan agidannan ne bayan ke? ko kuma aduk gidannan akwai ƙatuwar gantsamemiyar budurwa sama dake? Maza tashi kije Saifuddeen ne yana jiranki banason shashanci!." Idanu Zaleeha ta zaro, lokaci guda jikinta yasoma ɓari kamar mai aljanu, sam ta manta da cewa Ya Aminu ne agabanta cikin tsananin ɓacin rai tace. "What! Mayataccen gurgun nanne yaƙara dawowa, aikuwa saidai ya shekara don babu inda zanje!!". Taƙirasa maganan cikin rufewar ido. Cike da mamaki Ya Aminu ya matso inda take azafafe, cikin tsananin ɓacin rai yace "Me kikace? Maimaita nasakeji don banji da kyauba!". Shiru Zaleeha tayi tare da sunkuyar da kanta ƙasa, wani irin tafarfasa ranta keyi mata, ji take kamar ta kurma wani uban ihu ko zatasamu salama acikin rai da zuciyarta. Jin tayi shiru batace komai bane yasanya Ya Aminu daka mata tsawa cikin faɗa yace "Kintashi kinjene ko saina ɓaɓɓallaki anan wajen shashashar yarinya da batasan ciwon kanta ba!!." Jikin Zaleeha narawa ta-tashi da sauri har ƙafafunta na harɗewa haka ta nufi hanyar fita daga falon tuni wasu irin hawayen baƙin ciki sun cika idanunta, fuuuu haka Ya Aminu ya fice daga cikin falon, tsuka mai ƙarfi Mama tayi cikin baƙin ciki da takaicin Mijin ƴartata Maryam wato Ya Aminu tace. "Wallahi indai akan Zaleeha ne babu wanda ya isa yayi mata dole, idan kuwa har dolennema za a mata tofa lallai saidai in akan Abdussalam, amma wallahi babu wani matsiyacin gurgu daya isa nahaifi ƴa kuma ya aure ta." ƙwafa Mama tayi tare da cewa. "Duk zanyi maganinku ne ae dani kuke zancen!." Zaleeha kuwa ko gabanta bata gani da kyau saboda tsabar hawayen da suka cika idanunta, wani irin ɗaci na ɓacin rai takeji a maƙoshinta, cikin ranta wata irin wutar masifa ne ke cinta, yayinda wutan tsanarsa ke ƙara ruruwa acikin zuciyarta, tana kawowa bakin ƙofan da zai sadata da babban falon BQ ɗin ta tsaya cak, ƙoƙarin shanye hawayen dake cikin idanunta tayi, da wani irin ƙarfi ta bugi ƙofan falon, cikin takunta mai ɗauke da isa da kuma tsantsar rashin mutumci ta kutso kanta cikin falon. Idanunsu ne suka sarƙe acikin najuna domin dama tuntuni idanunsa akan ƙofar shigowa falon suke. Wata uwar harara mai ɗauke da tsantsar tsana, Zaleeha ta watsa masa, cikin takunta dake nuna tsantsar rashin mutumcin da takeji dashi ta ƙaraso cikin falon, ƙwas-ƙwas haka sautin takun takalminta ke amsa gaba ɗaya ilahirin falon, sam idanunta ya rufe da tsana, haɗi da masifar dake cinta arai, cike da son ƙuntata masa ta tsaya kusa dashi tare da sanya hannayenta ta kama ƙugunta, amasifance tace. "Waikai wani irin maye ne? ina tunanin tun a jiya nasanar dakai cewa bana sonka na tsaneka!". ɗan shiru tayi tare da dubansa sama da ƙasa da sauri ta janye idanunta daga nashi dan wani irin bugu da zuciyarta keyi a duk sanda suka had'a ido, tabbas yayi kyau sosai acikin idanunta amma masifane kawai ke ɗawainia da ita, cikin gatsali tace. "Oho wato kazone don ka nunamin naci da kafiya irintaku ta kurame ko? to bari kaji duk bala'in nacinka bazan taɓa sonka ba, na tsaneka wallahi natsani ganin fuskarka, waima shin kai bakasan cewa kai nakasashshshe bane? gurgu, kurma, sannan kuma maye" ɗan numfasawa tayi tare da sake matsowa kusa dashi cikin son ƙunsa masa baƙinciki tace. "Kakalleni da kyau koda a iya fuskata aka tsaya kai kasan niba matar yara bace, bare kuma irinka wanda bazai taɓa amfanata da komai ba, ginannen taɓo mai kama da dutsi!". Taƙare maganar tana jujjuya masa idanu tare da murguɗa baki, wai ita ala dole hakan masifa takeyi. Tunda tashigo cikin falon yake kallonta har kawo yanzu, wani irin sanyine yaji yana ratsa zuciyarsa, sosai abubuwan Zaleehan ke bashi dariya, duk acikin abubuwan da ta faɗa babu ɗaya wanda bai fahimci me tace ba sai dai ya gane tana tsoron kwayar idanunshi, acikin ransa yace. "Ginannen taɓo ko, hmmm zakisha mmki!." Ƙawataccen murmushine ya bayyana akan fuskarsa, cikin tsananin takaici Zaleeha ke kallonsa, zuwa yanzu kam yakaita bango don yagama ƙureta ahatsale tace. "Kayi dariya zama kayi kuka da waƴannan fitinannun idanun naka masu kama dana zuri'ar mayu, wallahi-wallahi, idan baka rabu dani ba nice nan ajalinka, me yasa bazaka gane cewa na tsaneka bane? Meyasa bazaka kalli wutar tsanarka dake ruruwa

Table of Contents

Chapters

148 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148