Chapter 11
Chapter 11
yi kenan ya zaga wannan layin ya zaga wancam layin, kana yana bin bakin shaguna yana kallon abubuwan dake ciki da yadda suke mu'amala da costumers insu, yana jin yunwa na k'ak'ularshi amman bai kulaba in lokacin salla yayi ya sayi pure water yayi al'wala yabi jam'in inda duk yaga ana haramar salla. Kafin magrib ya gaji lik'is. koda magrib ta kawo kai sai yaga anata rurrufe shaguna hakan yasa ya fita, bakin inda Salisu ya ajiyeshi, yana tsaye a wurin ya hango tsallaken titin anata Al'wala haka yasa shima yayi Al'wala kana ya tsallaka yaje akayi sallah dashi. yana dawowa Salisu na isawa, babu b'ata lokaci ya hau suka fara tafiya, sunzo dai-dai wani wurin masu tuwo-tuwo Salisu ya tsaya kana yacewa Saifuddeen. "Zo muje muci abinci kafin mu tafi naga alamun kamar ba abinda kaci." juyawa yayi kalli wurin da Salisu ya nuna mishi, baki ya tab'e kana ya girgiza mishi kai tare da nuna alamar kamar yana kekyamin abincin wurin. murmushi Salisu yayi dan tabbas yasan Saifuddeen mutunne mai tsananin tsabta da gayu kuma yanada kyakyani, dan yasan iya tsawon yarintansu bai tab'a ganin ya sayi koda ko kosai ko wani abuba cikin abubuwan da ake kawowa a yar majalisar k'ofar gidansu ba. So dan haka sai ya hau machine d'in yaja tafiya kad'an suka isa wurin mai shayi, kana yace. "To mu shiga nan kasha koda shayine." Still tab'e baki yayi tare da juya kai, alamun bazai shaba. ganin haka Sakisu ya kuma jan machine d'in, kai tsaye hanyar tashan Dukku ya nufa dashi, suna zuwa dai-dai bakin gate d'in Abba bakery yayi parking kana ya sauk'a sannan, yacewa Saifuddeen. "Zo muje nan ko zaka iya cin gashin wannan." a tare suka shiga inda daga mashigar wurin mai naman yake, ganin wurin fes komai a killacene yasa, Saifuddeen yarda ya zauna a wurin, naman d'ari biyar Salisu ya saya musu, kana ya shiga cikin asalin Abba bekery ya sayo musu yogurt k'ananun robabin guda biyu. nan sukaci duk da Saifuddeen bai wani ci mai yawaba yanka hud'u yaci bai kuma k'arawaba sai yogurt yasha. Tuni kafin lokacin an kira isha'i haka yasa sukayi sallan kafin suka nufi hanyar Dukku. Suna isa gida Ummi tai ta murna ganin ya dawo lfy kuma gashi babu alamun wahala, shi kuwa Saifuddeen yaki yace mata komai sabida gudun kada ta hanashi zuwa gobe. Washe garima kamar jiya suka shirya suka tafi bayan Umminshi tayi ta mishi addu'ar samun nasara. A inda Salisu ya ajiyeshi jiya yauma nan ya ajeshi, bayan yaja ya tafine shi kuma ya nufi bakin mashigar kasuwar, yauma kamar jiya saida yayi addu'a kafin ya shiga da k'afan dama. Kai tsaye layin masu kayan yara ya shiga a hankali yake bin shagunan daki-daki yana kallon yadda suke gudanar da kasuwancin su, mata masu ciki nata shege da fice, a hankali yake taku cikin nitsuwa. duk wanda ya ganshi sai ya k'ara juyawa ya kalleshi sabida bak'ak'en kayan da ya saka ba k'aramin haskashi sukayiba farinshi ya k'ara fitowa hancin nan har baki, uwa uba sumar kanshi tafi sawa ana kallonshi sabida duk wanda yaga sumar zai tunanin balarabe ne, fatar k'afafunshi da tafin hannunshi kuwa sunyi jazir, in ya taka k'afar tamkar jini zai tsillo. Dai dai bakin wani k'aton shago ya tsaya, yana tsayuwa kenan yaji an.....! By *NAKASA BA KASAWA BACE* *PAGE 4* NA *AYSHA ALIYU GARKUWA* πππππππππππππ Free page *Wannan page Ιin kuma nakunw Ζ΄an Hukuncin Allah fans two, ina al'fahari daku,* *Ga masu son saya turo katin Mtn na 300 ta nan 09097853276 ko ta asusuna 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa* Yaji An d'an matso kusa dashi har jikin wanda ya matso kusa da shid'in na gogan nashi jikin hakan ya sashi juyowa a hankali ya d'an kalli matashin da bazai zarta sa'anshi ba, ganin d'an saurayin yana murmushi ya sashi d'an murmusawa, shi kuwa saurayin cikin fara'a ya mik'a mishi hannu ganin haka shima Saifuddeen ya bashi hannu, fuska cike da fara matashin ya fara mgna cikin bagwariyar larabcin, dan a zatonsa Saifuddeen balarabene, sosai Saifuddeen ya zuba mishi ido tare da mmki dan ya gane zaton saurayin, haka yasashi k'ara tsurawa bakin matashin ido lokacin daya kuma ci gaba da mgna cikin larabcin shuwa'arab yace. "Barka da zuwa, shigo daga ciki, me kake so?." kai kawai Saifuddeen yake jujjuya mishi alamun a a ba abinda zai saya, shi kuwa saurayin murmishi ya kumayi dan a zatonsa Saifuddeen baya gane irin nashi larabcin ne haka ya sashi juya harshe eh zuwa hausa yece. "Kai wannan balarabe ba dai kyauba Masha Allah, ko me kakeso ne oho." wani dake cikin shagon ne yace. "Jabeer wai me yake sone, jiya mafa na ganshi a bakin shagon Alhaj ishaq." murmushi wanda aka kira da Jabeer yayi kana yace. "Ai bai gane larabcina." cikin zuba mishi ido wancan din yace. "To yaje gaba wala Allah a samu mai iya mishi irin yarenshi." daga nan ya juya yaci gaba da sabgogin jera kayayyakin. Shi kuwa Saifuddeen gane abinda suka cene ya sashi juyawa ya ci gaba da tafiya. daga nan yayi ta bulayi har azahar koda yaga ana al'wala shima ya zaro goma ya sai pure water yayi al'wala kana ya nufi inda ya hango ana jam'i yana zuwa ana tada ik'a. Bayan an idar da salla ya d'an jima a zaune yana addu'oi saida yaga an fara nannad'e taburman sai ya mik'e yaci gaba da yawatawa. kanshi ya kule ya rasa ya zaiyi dan sam cikin kasuwar babu mai kula kowa kowa sabgar gabanshi keyi, kana duk bakin shagon da yaje ya tsaya sai ai ta mishi gwarancin larabci, duk da yana ganewa to amman dame zai basu amsa tunda shi kurmane, haka yasa ake zaton bai gane larabcin ne tunda yawanci yan koyone ke gwada iyawarsu. jin ya gaji da yawone yasashi shiga layin masu kayan kitchen nan ya samu inuwa dai dai bakin wani babban shago ya tsaya bencin dake gefe yaja ya zauna, yana kallon yadda ma'aikatan keta cinikaiya da masu sayyya kasan cewar ramadan ya kusa baifi wata biyu ya rageba shiyasa kasuwan masu kayan kitchen ke gudu, sabida mata kan sabunta ababen aiki dan samun yalwatuwarsu. d'aya daga cikin yaran shagon ne ya kalleshi da kyau kana yace. "Mai gida Allah yasa dai kana jin hausa?." da sauri ya gyad'a mishi kai alamar. "Eh inaji." shi kuwa murmushi yayi sannan yace. "To me kakeso?." da sauri ya jujjuya mishi kai alamar. "Ba abinda nakeso." gane abinda yake nufi yasa yaron shagon yace. "Hutawa kakeyi kenan?." still kai ya gyad'a mishi alamar eh. ganin kamar baison mgnane yasa yaron ya shareshi yaci gaba da sabgoginshi. Shiko Saifuddeen gyara zamanshi yayi tare jingina da jikin k'ofar shagon. mata nata shiga da fita, sai ya kuma tsargu ganin yadda aketa kallonshi, har ya mik'e zai tafi sai ya kuma tsayawa ganin wani kekyawan Dottijo fari k'al dashi dake bisa keke bayan keken wani k'aton kwaline dake cike da lododi manya-manya irin k'atti sosai d'innan wanda in kayi sayayya mai yawa ake saka maka kayanka ciki, sai kuma tsaka-tsakiya sai yan saffa-saffa sai k'anana kana sai masu layi-layin nan sai kuma k'ananu irin mai gida ya kasa d'inna. hannu ya mik'a ganin wannan kekyawan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148