Chapter 126
Chapter 126
dake nuna cewa Saifuddeen ɗin nasonta da duka zuciyarsa, tabbas yana matuƙar jin tausayin Saifuddeen domin kuwa shi tuni yajima da gano cewa Zaleeha ba matar aure bace, ba irinta Saifuddeen ke buƙata ba, Saifuddeen yana buƙatar kamilalliyar mace, nutsatstsiya, wacce ta yarda da ƙaddara tayi imani mai kyau ko akasinsa daga Allah Ne, amma ya zaiyi dolensa zai haƙura da ƙin Zaleeha da yake, sahoda yaga gaba ɗaya soyayyarta ta rufe idanun Saifudeen, ya fahimci cewa Saifuddeen Zaleeha kawai yake gani aciki da wajen idanunsa, saboda haka zaiyi ƙoƙari wajen manta abun da tayi musu, zai taya Saifuddeen ɗin ƙaunarta, nan yayiwa Saifuddeen ɗin Allah yasanya al'khairi, daga shagon nasu Warisu kaitsaye Saifuddeen shagonsa ya nufa, shida Ahmad masha Allah koda yaje yasamu nutane maƙil sun cika shagon, sayan kaya kawai suketayi, yayinda cikin shagon ke shaƙe da kaya tam na yara irin new designer ɗinnan masu kyau, Manyan Hajiyoyine keta business ɗinsu, wasu sayan dayawa sukazo wasu kuwa sayan ɗaɗɗaya , kasancewar shagon cike yake da mutane yasanya Saifuddeen baiwani zauna acikin shagon sosai ba ya tafi, Kaitsaye shagon Ba mishkila ya nufa, nan ya iske Ba mishkila yau shida kansa ne acikin shagon, ba ƙaramin farin ciki ba mishkila ya yiba dayaga Saifuddeen, nan yashiga tambayarsa jikinsa, inda ya amsa masa cewa "Dasauƙi sosai" Daga shagon ba mishkila shagon Alhaji Ishaq baban abokinsa wato Ibrahim ya nufa, sosai Alhaji Ishaq yaji daɗin ganin Saifuddeen, shima sun ɗan taɓa hira inda yayi masa ƙarin ya jiki, daga shagon Alhaji Ishaq shagon Alhaji Kabiru Saifuddeen ya nufa, nan fa shima Alhaji Kabirun yacika da murnar ganin Saifuddeen, kasancewar hakan alamace dake nuna cewa sauƙi ya samu ga Saifuddeen ɗin. Sosai Saifuddeen yaɗan jima acikin kasuwan yayinda ya tsaya yagabatar da sallan Magriba cikin masallacin dake gefen kasuwan, yana idarwa suka kama hanyar dawowa gida. Ahankali yake tuk'a kekensa haryakawo cikin falon na ummi inda ya iske Raliya, Hayatuddeen, da kuma Ummi wacce ke zaune akan kujera, Hayatuddeen na zaune aɗan gefe da ita yana latsa wayarsa, Raliya kuwa tsugune take agaban Ummin tana mammatsa mata ƙafa, murmushin dake kan fukar Ummi ne ya faɗaɗa sakamakon ganin yanda fuskar ɗan nata ke ɗauke da farin ciki, cikin kulawa tace. "Saifuddeen kadawo?" Kansa ya jinjina mata tare dayi mata alama, cikin body language ya sanar mata cewa daga kasuwa yake. Murmushin jin daɗi Ummi tayi tare da cewa. "Allah ya taimaka." Duban Raliya tayi cikin kulawa tace. "Bar matsamin ƙafannan haka jeki kawowa hamman naku ruwa mai ɗan sanyi yasha." "To." Raliya tace tare da miƙewa tsaye ta nufi hanyar kitchine ɗin dake cikin falon. Hayatuddeen ne ya ɗago kansa, inda ya kalli Hamman nasa, cikin tausasawa yace. "Hamma barka da dawo, dama kamar kasan naƙosa ka dawo wallahi." Murmushi Saifuddeen yayi tare dayi masa alaman meke faruwa? Gyara zama Hayatuddeen yayi cikin zumuɗin labarin dake cinsa yace. "Ina wannan kyakkyawar mawaƙiyan da muka haɗu da ita a jirgi, lokacin da zamu dawo Nigeria, Hamma ka tuna ta Asma'u Ahmad Matawalle?." Yaƙare maganan yana me tsatstsare Hamman nasa da ido. Ɗan jim Saifuddeen yayi tare da ɗan lumshe idanunsa, in few second ya hasasho fuskarta, duban Hayatuddeen yayi tare da gyaɗa masa kai alamar eh ya tunota. Gyara zama Hayatuddeen yayi tare da cewa. "Yauwa Hamma, wai kasan mene? tun ranan da takarb'i phone number na, kullum sai munyi chart, bata da wani labari sai naka, kullum maganarka take, shine yau tace nafaɗa maka wai tanasonka, zaka aureta?." Baki Ummi ta buɗe tana kallon Hayatuddeen, shikuwa Saifuddeen fuska ya yamutsa tare da tab'e baki, wai harshi wata y'ar jagaliya mace mai rawa da wak'a data gama nunawa duniya sirrin jikinta babu hijabi zatace tanaso, bama wannan ba shi ayanda yakejinsa, ayanzu babu wata mace da zaiso, So d'ayane tak kuma Zaleeha yakeyiwa shi, sam bayajin cewa wata mace zata samu matsuguni ko muhallin zama, koda ko abaki-bakin zuciyarsa ne, d'an madaidaicin glass cup ɗin da cikinsa ke d'auke da lemon exotic, wanda Raihana ke mik'o masa ya amsa, da kad'an-kad'an yake sipping exotic juice d'in, saida yasha kusan rabin cup d'in kafun ya ajiye, ahankali yatuƙa kekensa inda ya k'arasa har gaban Ummi, hannayensa ya d'aura akan nata tare da langwab'ar dakai. Murmushi Ummi tayi don hakan da yayi yasa ta fahimci cewa magana me mahimmanci yakeso suyi. Cikin sakin fuska Ummi tace. "Faɗi duk abun dake ranka Saifuddeen ni me mara maka baya ce akoda yaushe." Murmushin jin daɗi yayi inda ya ciro wayarsa daga cikin al'jihun rigarsa, duk wani abun dake cikin rai da zuciyarsa haɗi da duk wani ƙudirinsa saida ya rubuce shi cikin text message, miƙawa Ummi wayar yayi inda ya sunkuyar da kansa ƙasa, karɓan wayar Ummi tayi cikin nutsuwa ta shiga karanta abun da Saifuddeen ɗin ya rubuta, wata irin sassanyar ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe alokacin da ta gama karanta saƙon nasa, murmushine ya bayyana akan fuskarta take kuma sai ga hawaye sun cika idanunta, sosai rauninta ke ƙoƙarin fallasa sirrin zuciyarta, hannayenta tasanya ta ɗago haɓarsa, cikin son ƙarfafa masa guiwa ta shafi gefen fuskarsa, cikin yanayi na tausasa murya tace. "Dama nasani ɗana bazai taɓa zama rago ba, haƙiƙa kai ɗin jarumine, haka kuma babu wata ƴa mace da zata so yin asararka." Ɗan numfasawa tayi tare da sauƙe ajiyar zuciya akaro na barkatai. "Nayi matuƙar farin ciki Saifuddeen, haƙiƙa ganin aurenka yana ɗaya daga cikin burukan rayuwata, Allah Ubangiji yasanyawa tarayyarku albarka!." Ummi tafaɗi haka cikin tsananin farin ciki, sosai takeson abun da Saifuddeen ɗin ke so, saboda farin cikinsa itama shine nata. Cikin samun nutsuwar zuciya Saifuddeen ya ɗaura kansa bisa kafaɗan mahaifiyar tasa, cike da ƙaunarta yayi mata alaman godiya, ahankali tashiga shafa kansa, tana mejin farin ciki aranta, lallai dole ta-tayashi wajen ganin ta ƙawata bikin ɗan nata. Hayatuddeen da Raihana kuwa idanu kawai suka zuba musu, aƙalla Saifududdeen yaɗauki kusan 4 minute kansa na bisa kafaɗan Ummi, kafun daga bisani ya janye, cikin nuna alamun gajiya ajikinsa yace da Ummin nasa zaije yaɗan watsa ruwa. "To." Ummi ta amsa inda tace dashi Hayatuddeen zai kawo masa abinci. Hayatuddeen naganin wucewar Hamman nasa ɗaki ya zaburo, cikin tsananin gulman dake cinsa yace. "Ummi wani abu ya farune naga kunata farin ciki keda Hamma?". Murmushi Ummi tayi tare da cewa. "Banason gulma fa Hayatuddeen." Baki Hayatuddeen ya turo gaba. Raliya ce ta gyara zama tare da cewa. "Ummi ai ba Hayatuddeen kaɗai bama nima ina son ji, dan Allah Ummi menene, ko akan maganan aurensa ne?" Dariyan yaran nata ne ya kamata, cikin kulawa tace. "Yarinyar da Hammanku yakeso ta amince dashi, harma ta bashi daman turo magabatansa don atsaida maganan aure, yanzu haka mahaifinta ya amince, mu kawai ake jira mukai lefe da sadaki asaka ranar aure!." Wani irin ihun daɗi Hayatuddeen yayi tare da miƙewa tsaye, cikin tsananin farinciki yace. "Yessss!! Lokacin yazo!." Raliya ma tashi tsaye tayi cike da murna tabawa Hayatuddeen hannu suka tafa, cikin jin daɗi da farin ciki tace. "Masha Allah, ae kuwa za ayi biki irin wanda ba'a taɓa yiban zaton mai nakasa zai yishiba acikin garin Gombe." Sake tafawa da Hayatuddeen sukayi cikin jin daɗi Hayatuddeen yace. "Yanzune jama'ar cikin garin Gombe zasu san cewa akwai manyan yara masu tasowa, na
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148