Chapter 63
Chapter 63
str zuciyarshi da jikinshi na cike da fargaba da tsoron halinda martashi Rahma zata shiga in taji abinda ya samu d'an uwanta, ya rasa tudun dafawa, a fili yace. "Ya ilahi ya mujubbat da'awati ko taya zan sanarwa Rahma." sai kuma yayi sauri zaro woyarshi Ishaq ya kira, bayan sun gaisa yace. "Kun isa lfy,?." "Lafiya lau Alhamdulillahi." gyara zamanshi yayi tare da kallon k'ofar corridor d'in part d'in Raihana sannan yace. "Kun samu Dr Aliyu ko?." "Eh to gsky mun samu tarba daga wurin Doctors har uku to gsky ban sanan wanne ne Dr Aliyun ba a cikinsu." cikin sanyi yace. "Zakaga Dr Aliyu shima nakasasshene ai domin shima yanada matsalar spanal cord kuma shine big doctor a k'asarnan in dai a wannan fannin ne, uban gida nane kuma wa nane d'an kawuna." cikin jin dad'i Ishaqa yace. "Alhamdulillahi, hakan yayi kyau domin dama shi nakasa ai ba kasawa bace, kuma ya yi mana k'arin bayani kan mu kontar da hankalin mu, Alhamdulillahi kuwa tuni ya farfad'o kuma yana cikin haiyacin sa, so zuwa gobe da safe zasu fara bincikan adadin zurfin ciwon." lumshe ido Dr Adnan yayi kana yace. "To Allah ya kaimu, in sha Allah nima gobe zan taho please kuke kontarwa Ummi hankalinta." "In sha Allah ba matsala." cewar Ishaq. Kana daga nan sukayi sallama, shi kuwa Dr Adnan Dr Aliyu ya kira bayan sun gaisa yake mishi godiya tare da tambayar ya mai jikin, so shima Adnan ya samu d'an nitsuwa duk da cewa Dr Aliyu ya tabbatar mishi cewa Saifuddeen ya samu nakasar lakkar bayanshi. bayan sun gama woyar ne yana d'ago kanshi ya hangi Rahma tsaye bakin k'ofar kitchen ta kafeshi da ido gaba d'aya jikinta tsuma yakeyi tuni hawaye sun jik'a fuskarta, mutuwar zaune yayi domin tabbas yasan taji duk wayar da yayi dasu, dan sam hankalinshi bai bashi ko tana kitchen ba. Ita kuwa matsowa ta farayi a hankali take taku still jikinta na rawa, gabanshi ta tsaya tare da tirtsetsen cikinta, da sauri yasa hannu ya jawota jikinshi kan cinyarshi ya ajiyeta, suna fuskantar juna, murya na rawa tace. "Me kuma zaka boye min Ya Adnan me zaka boye min? gaya min me zaka boye min. wani abune kuma ke tinkarar rayuwarmu? meya samu d'an uwana? ina yake, waye zai nak'asa Saifuddeen ne ko Hayatuddeen gaya min wani hali Ummi ke ciki?." gaba d'aya ta birkice ta gigitashi da tambayoyinta yama rasa wanne d'aya zai amsa mata kuma tana k'ara tuno mishi fargabar da Ummi ke ciki. Kawai sai ya had'eta da k'irjinshi ya ruggumeta da k'arfi kana ya fara magna cikin dakiya yace. "Madadin kiyi mishi addu'a sai kiyi mishi kuka? kin san halin da yake shiga duk sanda yaga hawaye a kwaranya a idanunki, meyasa rauninki yake yawaita, da can baya da juri na sanki to meyasa bazaki ruggumi k'addaraba, ki godewa Allah a cikin dukkan lamarinki." tunda yace mata kin san baya son kukanki ta gane Saifuddeen ne, to wani zafin ya wuce inda hawaye yake fargabarta da nitsuwarta duk sun had'u sun hargitse sun danne hawayenta, sai tayi wani azabebben murmushi da yafi kuka zafi cikin sanyi tace. "Alhamdulillahi ala kulli halin, ya Allah ka fini sanin waye Saifuddeen ya Allah ka fini sani adadin mutanen da ya zame musu uwa uba yaya k'ana, ya Allah ka fini sanin rauninshi dana mahaifiyarmu ya haiyyu ya k'aiyyum ya zirjalali wal ikram ya Allah ka bashi lfy ka d'aga kafad'un shi." da sauri Dr Adnan yace. "Amin Amin, Ameeen ya rabbil izzati." daga nan yayi ta bata baki da nuna mata ciwon baiyi tsanani ba. Amman duk da haka daren wannan ranar itama sam bata rumtsaba. Raihana kuwa har dare Allah baisa ta tuno da Affan ba domin tunda suka dawo data haura sama d'akin Saifuddeen kuka tayi tayi, sai bayan sallan isha da Amira 'yar Alhaji Kabiru ta dawo mata da shi itama haka ta kwana yiwa d'an uwanta addu'a. A can Abuja kuwa, tunda asuba matar ya Rabi'u Aunty Mami ta tasa yar aikinta gaba suka shiga kitchen, dan Ishaq ya gaya mata da sanyin safiya zasu koma asibitin. bayan ta gama komai ne ta d'auki na su Ishaq da yayanshi da Hayatudddeen ta kai musu bisa dinning table dake nan men parlour nasu, inda tunda suka dawo masallaci suna nan zaune suna tattauna matsalar inda shi Hayatuddeen yake cewa shi yafi son a fita woje da Hamma Saifuddeen nashi yaci gaba da cewa. "Ance Jermaine itace k'asar da tafi shahara da kwarewa ta fannin wannan ciwon, ni kam da zan samu mu fita dashi." ya k'arishe mgnar yana mai kallon Ishaq da yanayin neman izini. Cikin tausayawa Ya Rabi'u yace. "Ba matsala ! Hayatuddeen in sha Allah tun da Dr Aliyu yasa hannu kan lamarin so ko can Jermaine aka kaishi iya abinda yace zasu ce, kana nasan zaiyi duk abinda ya dace in kuma yaga fitar da shid'in nema maslaha to tabbas, nasan zai bada dama a fitar dashi, kuma zai shige mana gaba yadda komai zaizo da sauk'i. Yanzu ku matso muyi breakfast saimu hanzarta zuwa, tunda ya shaida mana kwana zai a asibitin kana da safe zai dubashi kafin ya tafi gida." cikin lumshe ido irin na marasa gani Ishaq ya d'an shafa kan Hayatuddeen tare da cewa. "Zo muje kaci abinci in sha Allah Saifuddeen zai samu lfy." haka dai sukayi ta bawa juna k'arfin guiwa. Ummi kuwa sam ta gaza samun sukuni, abinda ta sanine bazata iya cin abinciba, amman ganin yadda Mami ta matsa akan dole taci abinci yasa tace. "Bani tea kawai in sha." cikin jin dad'i Mami tace. "Yauwa Ummi gwara kici wani abu kafin ku tafi domin, bamu san yaushe zaku dawoba, kuma shima zama da yunwa cutane." amsar cup d'in tayi tare da cewa. "Sannu Mami Allah ya saka." Amin tace tare da mik'ewa ta fida dan ta bata wuri, tasan in tana nan ba sha zatayi zabida sabida poolaku irin na al'ummar Dukku. ita kam Ummi ji take tea d'in tamkar da mad'aci aka tafashi ba sugar ba. Haka dai ta d'an sha rabi nai, kana ta kimtsa ta fito dan Hayatuddeen ya kirata akan tazo su tafi, tare da Ya Rabi'u da Aunty Mamin suka tafi, ita Ummi da Aunty Mami suna motar ya Rabi'u shiko Hayatuddeen key d'in mota ya Rabi'u ya bashi kana suka taho shida Ishaq. Shi kuwa Ahmad Abban Farida kenan, yana gama kimtsawa ya kira Hayatuddeen cikin sa'a ya d'aga bayan sun gaisa ne yake cewa. "Hayatuddeen wanne asibiti kuke ne?." cikin sanyi yace. "Ya Ahmad kazo ne?." da sauri yace. "Eh nazo kuma ban san inda kukeba." meda hankalinshi yayi bisa tuk'in da yake kana yace. "Kana ina yanzu inzo in d'aukeka?." masauk'in da yake ya gaya mishi hakan yasa ya juya akalar motarshi ya nufi Royal Hotel, a harabar hotel d'in suka sameshi, ba tare da b'ata lokaci ba ya shiga kana suka juya suka tafi. Su Ummi kuwa suna isaya Ya Rabi'u ya nemi ganin Dr Aliyu nurses en suka ce mishi ya d'an jira nanda 20 minutes. dan yanzu yana woyane, haka yasa suka zauna a yar farfajiyar gaban office enshi, bayan kamar 15 minutes su Hayatuddeen ma suka iso tare da Ahmad nan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148