Chapter 3
Chapter 3
shima Nuruddeen baima iya nomanba, kasan cewar su Abba sun gaji tarin filaye a wurin babansu wanda shima babansu a wurin babanshi ya gada, to nauyin rayuwarsu ya ta'allaqa da su bada jinginan filayen ana noma ana basu yan wasu kud'ad'e da zasu iya ciyar dasu. To amman da yake larurar jinya ta shiga sai ya zama kud'in basu isarsu, wasuma in sun karb'i gonakin basa basu kud'in jinginar wasu kuma suyi ta bayarwa har kud'in yafi k'arfin yadda zasu iya maida musu su bare su amshi gonarsu dole sunaji suna gani gonakinsu suke fin k'arfinsu, uwa uba ga Bappa Ali k'anin Abba irin mutanennan masu saude-saide. Shiyasa tun bayan rasuwan iyayensu motsi kadan sai ya saida gona. Yaje yayi tabin masu magani wai zai nemawa Abba mgnin jikinshi wai ko Allah zaisa ya rabu da makaranshi, kwana kad'an abu yayi sanyi in ya sake tashi sai yafi na baya. bud'e ido Ummi tayi jin abinda Nuruddeen yake fad'i, rubutun gaban Saifuddeen ta zubawa ido inda yake cewa. "Ya Nurudeen makaranta nafa ya zanyi inyi karatu? banaji bana iya Magna, gashi next week zamu fara exams, isilamiya ma an kusa ayi musabak'a Ya Nuruddeen ta ina zanyi karatu ta yaya zan bada hadda?." wannan tambayar tashi itace tasa kukan Nuruddeen k'aruwa yana kuka yake cewa. "Zakayi karatu Saifuddeen, in sha Allah zakayi karatu boko da Arabic, in Allah ya yarda nakasarka bazata zama tawaya ba." kai ya gyad'a alamun gamsuwa kana ya koma bayan Abbanshi ya konta time to time hawaye na zubo mishi yana sharewa, a haka yayi bacci kasan cewar basuyi bacci ba daren jiya yawo suka kwana sunayi. Allah sarki Nuruddeen daga wannan ranar, ya fara fafutukar nemawa Saifudddeen mgni amman ina, k'addara ta rigayi fata, domin wannan abune da muka sani a k'asar hausa, some times k'enda tana sanadin makanta, kuramta gurguntaka, koma tab'uwar hankali gaba d'aya wa Al'ummarmu musamman in lokacin zafi akayishi. Kamar dai yadda ta kasance akan Saifuddeen. Haka dai rayuwa tai ta tafiya yau fari gobe summa, a cikin wannan yanayin aka aura da Rahma tunda ta gama Secondary school inta, inda aka aura mata Sadik dan abokin abbansu Hamisu. Shi kuwa Saifuddeen, ya bar zuwa makaranta dan ko yaje malaman basu wani meda hankali kanshi, kuma gashi babu makarantar nakasassu a Dukkun, sai dai yana zuwa islamiya, kuma Alhamdulillahi malam suna matuk'ar kula dashi, a wannan lokacin akwai wani babban malami su abokin Malam Ashiru ne wanda shida kanshi yake ware Saifuddeen ya koyar dashi, yakan bashi hadda ya kuma, iya in yazo sai ya zauna dashi ya bashi takardu ya rubuta mishi abinda ya koyar dashi kuma Alhamdulillahi da kai yake kawo komai yadda ya kamata, wasu lokutanma har shike karb'ar haddan na k'asa dashi kuma duk k'ank'antar batan da akayi Saifuddeen zai gane har yayiwa yaran gyara ta hanyar rubuta musu komai. kusan shekara biyu da faruwar abun kenan wanda tuni Saifuddeen yana da haddan izu 37 a kanshi yana kuma karanta littatafai na addini sosai kamar Hadisai, tauhit, Nahawa, kulasatul nurul yak'in, da kuma tajweed dan yama fi maida hankali kan tajwweed a cewar shine zai taimakawa karatunshi ya gane kurenshi da kanshi ya gyarawa kanshi, kana sosai yake bibiyar littafan koyan larabci. Zuwa wanna lokacin ya saba da kuramtarshi, Nuruddeen kuwa har yau yana nema mishi mgnin. Ranar wata Jummu'a da dare Nuruddeen shida Abba da Bappa Ali suna zaune suna hira kamar yadda suka saba gyara zama Nuruddeen yayi kana ya sunkuyar da kanshi sannan ya kuma d'agowa ya kallesu, cikin sanyin murya yace. "Bappa Ali, ya batun karatun Saifuddeen ne? kunyi shiru bakuce komai ba, kuma tun kwanaki naketa binku a saida gona d'aya, a saya min machine, tunda na iya na koya a mashidin abokina Adnan, tunda akwai makarantar kurame a cikin Gombe, kullum da safe sai in tafi dashi in kaishi makaranta ni kuma na wuni yin acabana, in zan dawo da yamma in d'aukoshi mu dawo tare, kunga baiyi nesa damuba kuma zai samu ilimi, kana mun sauk'e hakkinshi daya rataya kanmu, kuma mun cire mishi nakasar zuciya, kana mun ink'anta rayuwarshi, sannan zai samu k'arin fasaha da basira ta yadda zai k'ara samun experience, sannan mu rabashi da barace." shiru yayi ganin duk sun zuba mishi ido, su kuwa yabawa sukeyi da shawararshi domin sun san gsky ya fad'i. hakan yasa Bappa Ali gyara zama tare da cewa. "In sha Allah hakan za'ayi Allah yayi maka al'barka Seyo da yake haka suke kiranshi *Seyoji ko Seyo duk d'aya ne* kakmar fillancine da take nufin FARIN CIKI a hausave. murmushin jin dad'i Nuruddeen yayi kana ya kalli Abbansu da yake zubda hawayen tausayinsu yace. "Abba kada kayi kuka, in sha Allah watarana muma zamuyi farin ciki, Allah zai sauqaqa mana zafafan k'addarorinmu ih zuwa dad'ad'aan k'adarori domin dukkan tsanani yana tare da sauk'i, ku dai kuyita mana addu'a." cikin sanyin murya Abba yace. "Allah yasa haka Seyo na Allah ya al'barkaci rayuwarka ya baka damar rik'e k'annenka." Amin Amin ya rabbil izzati. Suka amsa a tare. Tofa daga wannan ranar akasa wata yar madaidaiciyar gonarsu a kasuwa cikin ikon Allah a wata d'aya akayi cinikinta aka basu kudin. A ranar da aka basu kud'i a ranar Bappa Ali ya shiga cikin birnin gombe ya sayowa Nuruddeen mashin d'in bajat sabuwa dal, kana daga ranar suka fara cuku-cukun nemawa Saifuddeen gurbin karatu a makarantar kurame ta Gombe. Special education Gombe state, cikin sa'a aka sama mishi takardar shaidar ya zama d'alibinsu zai ci gaba daga JSS two, kasancewar da sa hannun Malam Ashiru abokin Abbansu kuma Saifuddeen kanshi na ja sosai domin nakasarsama kamar k'ara zaburar dashi tayi. Daga wannan ranar kullu yaumin fisha'i. Nuruddeen zaiyi sammakon baro Dukku tare da Saifuddeen suna shiga gombe ya kaishi makaranta kana shi kuma ya shiga cikin gari yayi ta kabo-kabonshi tun baisan anguwaninba har yazo ya saba ya goge ya zama idon gari, sai sun karya suke tahowa kana shabiyu nayi zai kaiwa Saifuddeen abinci duk da ana basu abinci a makarantar kasan cewar sashinta boarding school ne kana kuma akwai yan jeka ka dawo in har iyayenka zasu iya d'aukar dawainiyarka. A ranar forko Saifuddeen ya had'u da abokinshi Is'haq makaho wanda suka shak'u sosai har yan uwan is'haq sun san Saifuddeen da Yayanshi Nuruddeen, hakama Nuruddeen yasan yan uwan is'haq dan har gidansu yana zuwa, dan in an bada hutu Saufuddeen kan biyo Seyo gombe ya kawowa abokinshi ziyara su wuni suna hira da yake shi Is'haq iyayenshi a gombe suke cikin anguwar Fada, shi Is'haq makahone kuma shima k'enda ce sila makantan shi dan ya bawa Saifuddeen lbri suna hira ta hanyar is'haq yayi Magna shi kuma Saifuddeen ya rubuta mishi amsa a wayarshi da yake iyayen is'haq sunada yar wadata sun saya mishi waya. Haka rayuwa tai ta tafiya mashin d'innan ba k'aramin rufa asirinsu Ummi yayiba, suna samun komai a wadace, shi kam Nuruddeen ya jingine batun nashi karatun dama dukkan buk'atun rayuwarshi burinshi ya gina rayuwar Saifuddeen. Tuni rayuwa ta mik'e, sai dai kullum jikin Abba na yawan tashi, Rahma ta haifin d'anta na fari mai suna Faruq, har ta kuma haifi na biyu mai suna Adam. Tuni Saifuddeen ya tafi SS 3 shida abokinshi Is'haq da wasu sauran
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148