Chapter 32
Chapter 32
shinkafa da miyar ganye wanda miyar asubane to da yake miyar da d'an yawa shiyasa ta tuk'a musu tuwo, a zatonta bazasu wani ciba amman kuma sai gashi sun cinye tas yau harda Saifuddeen da yake abinda yake sone Warisu ne ya d'anci kad'an. Bayan sun gama cine Ahmad ya firfito musu da d'inku nansu baki d'aya, sosai sukayi mmkin yadda ya gama d'inkunan cikin k'ank'anin lokaci kuma d'inkunan sunyi kyau sosai da salon tsarin d'inkunan wannan shekarun. Nan Saifuddeen ya bawa kowa nashi, duk sukayi godiya dama tuni Saminu ya kawo musu takalmansu da huluna Salisu kuma ya kawo musu ogogunansu. Daga nan duk sukayi sallama suka tafi sai Ahmad da yace yau nan zai kwana, to bayan su Mudassir sun tafine Bappa Ali da Aunty Nina ma sukazo yiwa Saifuddeen godiya nan sukaci gaba da hira, a nanne Saifuddeen yace dasu, Hayatuddeen zai rink'a zuwa wurin Ahmad ya rink'a koya mishi d'inki, to kuma duk sunyi na'am da hakan daga nan suka d'an tab'a hira sannan duk sukayi saida safe suka watse. Washe gari kamar kullum suna isa ya d'an shiga massalaci yayi baccin awa d'aya da rabi yana tashi yayi al'wala yayi walahanshi, yana fitowa kai tsaye layin da zai sadashi da kantin kori ya shiga, yana isa d'ab da kantin korin ya tsaya a bakin shagon Malam Habu mai saida mayukan shafa da turatuka powder da dai sauran kayan kolliya na mata, Sadiq na ganinshi cikin fara'a yace. "Barka da isowa Balarabe." murmushi yayi tare da mishi alamun bafulatani dai daga nan suka d'an gaggaisa da mutanen layin sannan ya isa dilansu na ledan yana zuwa aka bashi kamar kullum sannan ya fara zazzagayawa ya rabawa kowa. Koda ya gama sai ya d'auko omonshi nan yayi ta zagayawa sosai kuwa yau ya sayar koda ya gaji ya koma shagon Malam Habu ya zauna yana d'an hutawa dan yana son yaje gidansu Ishaq to ya kuma yanaga kada yaje ya samu basu isoba da wannan tunanin ya bari sai gobe yaje, cikin body language ya tambayi Malam Habu ko yasa inda gidan Baba Bella yake?." kai ya jujjuya alamun gsky bai saniba to amman sai ya bashi shawaran yaje ya tambayi Alhaji Aliyu dilansu na ledodin kenan dan yana kyautata zaton shi zai san unguwar da Dottijon yake, nan yake cewa Malam Habu ya mantane Alhaji Aliyu baya k'asar ya tafi umrah, to nan yace ya tambayi yan shagonshi wata k'il zasu sani, toh fa abu kamar da wasa ya tambayi duk mutanen da yake zaton zasu san gidan Dottijon nan baba Bello amman duk sai kowa yace ko unguwar da yakema basu saniba yayinda wasuma sai suke mmki da ce mishi ba yace kai jikanshi bane to ya za'ayi kai jikanshi baka san gidanshi ba sai mu. Shi kuwa Saifuddeen ribarshi na yau na omo dana leda harda riban omon jiya ya had'an kud'in 10k da nufin zai yiwa Baba bello ihsanin yayi hidiman salla, to kuma gashi ya rasa wanda yasan gidan, dole haka ya hak'ura sannan ya bawa malam Habu ajiyan wannan 10k d'in dan ya rigada yayi niyar wannan kud'in Dottijon zai bamawa. K'arfe biyar nayi Salisu yazo suka tafi Dukku. Washe gari kuwa ta kama ranar ne ishirin da tara ga watan Ramadan wonda ana zaton ganin watan salla yau ko gobe dan haka da zai fita tafiya gombe sai ya harhad'a duk sauran kud'ad'en da yake adanawa ya sasu a aljihu ya tafi dasu. To koda ya gama rarraba ledodinshi kamar kullun ya saro omonshi yayi ta yawatawa har aka k'arfe uku saura kwata bayan ya had'a ribarshi ya wuce ya maida omonshi daya rage, daga nan ya wuce shagon Alhaji Kabiru wanda ake saida duk wani kayan d'and'anon miya kama daga Magi, raico, onga gishiri kafi Mai, Manja, fulawa, madara, sugar, sufageti, macaroni, indomi. da dai sauransu suna bada sari suna saida kad'an-kad'an kuma suma shine ke saida musu ledodin da suke zubawa kostomominsu kaya in sunyi sayayya. Sun saba sosai da Alhaji Kabiru dan shima yanada d'anshi kurma shiyasa yake tsananin son Saifuddeen, yana isa bak'in k'aton shagon nasu ya zaro pepar da biro ya rubuta musu duk abinda yakeso, nan Alhaji Kabiru ya amsa da kanshi ya ware mishi duk abinda ya lissafa bayan ya gama sasu a leda cikin nitsuwarshi yace. "Masha Allah Saifuddeen Allah yasa Isma'il d'ina ya zama mai nagarta kamarka, kalli yanzu wasu manyan magidan tama basuyi azamar cefenen sallaba amman gashi kai tuni ka gama komai abinka." kai ya d'an sunkuyar tare da gyara hannun riganshi sannan ya d'ago kanshi tare da yin murmushi cikin girmamawa ya amshi ledan da yake mik'o mishi sannan ya bashi kud'inshi tare da mishi godiya da sallama sannan ya juya ya tafi. Layin masu yankan kaji yaje nanma ya sashi zabbinshi guda biyar ya bada kudi kana yace musu in sun gyarasu su sa mishi su cikin firij sai k'arfe shida da rabi zaizo ya amsa, dagana kuma ya sayi jan nama na dubu 3 sannan ya wuce layin masu tattasai, inda yaje ya sayi, Tattasan, attaruhu, tumatur, al'basa, kabeji, karas, green beans. Da dai sauransu, sai ya kuma sayi dankalin turawa kond'o d'aya, daga nan ya wuce shagon da yake saran pure water inda ya samu Rabi'u nan ya sayi katon d'in fanta da Coca-Cola sai rabin ledan molt sannan ya had'a duk su tattasai ya kai aka marked'a mishi sannan ya ware wasu tattasan da taruhu da al'basan kuma wanda ba'a marked'aba ko za'a buk'acesu hakan. Kana ya harhad'a duk abinda ya sayan a shagonsu Rabi'un dan yasan shi da masu nama suna kai har dare kuma dama ya gayawa Salisu yau sai anyi sallan isha zasu kama hanyar tafiya dukku, k'arfe uku da rabi dai-dai ya gama duk sayyarshi sannan ya nufi masallaci ganin anata haraman sallan la'asar, baya an idar da sallan ne ya kama hanyan gidansu Ishaq wanda shi kuma tun jiya yake zuba idon ganinshi. K'arfe hud'u saura mai machine ya sauk'eshi k'ofar gidansu Ishaq dake cikin tudun wadan nan layin fad'a, yana sauk'a ya nufi cikin gidan, tare da sallama a ranshi ya shiga. Mommy ya samu a tsakar gida mai aikinsu tana mata kitso, tana ganinshi ta fad'ad'a murmushinta tare da bud'a baki cikin d'aga sauti tace. "Wa alaikassalam lale marhabin da Saifudddeen Ishaq ina kake ga amininka ya iso." shi kuwa gefenta ya rusuna tare da gaita, shi kuwa Ishaq da Imaran da Mamansu kusan a tare suka fito, yana ganin ishaq ya mik'e ya nufi inda yake yayinda shi kuma ishaq k'amshi turaren Saifuddeen d'inne ke masa jagora, ruggume juna sukayi lokacin da suka had'u sai kuma ishaq ya sakeshi sannan ya ware hannunshi ya manna bisa fuskan Saifuddeen cikin raha yace . "Iye iyeh my friend watoma kai azumin nan k'ara maka kyau yayi ka ganka kuwa yadda kayi kyau." dariya sukayi baki d'aya dan ganin yadda Ishaq yakeyin abu kamar mai gani, shiko Saifuddeen wayar ishaq ya karb'a tare da rubuta mishi. "To kanari sarkin zance da wanne idon kaga kyan nawa?." da sauri ya kauce ganin Ishaq d'in zai kai mishi bugu shi kuwa Ishaq cikin fara'arshi yace. "To kai da wanne kunnen kaji abinda nace?." murmushi yayi tare da kuma rubuta mishi amsa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148