Chapter 55
Chapter 55
dan ganin ana gab da kiran salla shiyasa yake son ya koma gida ya samu yayi bud'a baki yasha ruwa a nitse. A irin ya wannan lokacin duk mazauna gombe sunsan yadda ababen hawa ke cika titinuna especially wuraren da fitilun bada hannu suke haka yakesa cunkoson ababen hawa ke yauwaita tamkar a birnin Lagos. Hakan ce ta kasance a wannan babban titi daya ratsa daga gaban babban gate d'in Gombe State University (G.S.U) wanda titin zai ratsa gaban k'ofar babbar fadar masarautar jihar ta. Gombawa kana daga hannun dama kuwa Gate d'in babban ofishin k'ungiyar nakasassu ta jihar Gombe mai taken joint national association of persons with disabilities. (jonapwd) Gombe state chapter. All the best! ne wanda yake fuskantar ratsestsen ginin G.S.U kana daga gefen (jonopwd) d'in akwai wata yar kasuwar Tudu wato kasuwan mata, in ka mik'a titin kad'an kuwa akwai fitilar bada hannu, wacce gefen titin wurin akwai shaguna a cikin jerin shagunan kuwa a nan babban shago na saye da sayarwan magunguna wato A.A Aliyu pharmacy d'in yake wurinda Saifuddeen yake a yanzu haka kenan!. Wasu jerin ayarin tsala-tsalan motocine suka ratso harabar gate d'in G.S.U moto cin sun sun kai guda 5 , kai da gani kasan yara ne suke jan motocin dan yadda suke tsula gudu tamkar zasu tashi sama, sai gilmawarsu kawai zakaji fiw-fiw suna gibtawa. Da sauri mutane suka rink'a kaucewa sanin rashin mutuncin shugaban ayarin, *Dalla* haka yasa akabi ayarin motocin da ido, dukansu kyawawan motocine amman, akwai guda d'aya daga cikinsu duk ta fisu tsada da sabunta, bisa dukkan alamu bugun 2019 ce motar dalliyace mai azabar kyau sai shek'i da k'elli takeyi, hatta tayoyinta tamkar ka lashe, koda yake haka baya rasa nasaba ne da yanayin tsabtace titunan birnin Gombe da akeyi ne a ko wanne safiya wannan yasa gombawa sukayiwa sauran jihohi zarra a fagen tsabta dan daga bakin gate din G.S.U. zaka iya cilla ganinka har kan shatale-talen dake k'ofar fadar jiha baza kaga koda tsinkeba a bisa titinunan ba,, motar ruwan tokace sai gilashenta da suka kasance masu duhu, yadda na ciki na iya ganin na woje na woje kuwa bashi da damar ganin na ciki, motoci biyu dake gaban wannan motar sun wuce kenan sai kuma ita motar da tafisu kyau d'in tana biye dasu, yayinda biyu ke bayanta gudu sukeyi tamkar titin dan su kad'ai akayishi . Sun zo dai-dai bakin gate d'in K'ungiyar nakasassu ta jihar Gombe, Joint national association of persons with disabilities, (jonapwd) d'in kenan, sai kuma ga ratsetsiyar motar Zaleehs ta fito daga cikin harabar (jonopwd) d'in kai tsaye ta danna hancin motarta bisa titin kana ta ratsa tsakiyar ayarin motocin nan, inda ta shiga tsakanin motar nan mai kalar toka da saura biyun nan masu biyoshi a baya, Zaleeha kekyawar budurwace a cikin motar wacce da ka ganta kasan tana cikin ganiyar k'uruciyarta iska na kad'a igiyar budurcinta, tutarta na karkakad'a zuk'atan maza tauraronta na d'auke idon dukkan lafiyayya namiji ganin fuskarta kawai kansa duk lafiyayyan namiji yayita yayyafi, taka motar takeyi tamkar zatabi takan motarnan dake gabanta, dole tasa saura biyun nan suka biyo bayanta, kasan cewa gudu sukeyi cikin abinda bai gaza 58 seconds ba suka isa madakatar fitilar bada hannun dake tsakiyar titin, dole tasa suka d'an tattaka birki tare da tsagaita tafiyar tasu, a hankali ta lumshe idonta tare da bud'esu kana ta shak'i sassanyar iskar hunturu dake ratsa jikin mutane, kanta ta d'an juya ta kalli gefen gabas inda taga nanma cike yake mak'il da ababen hawa, wani d'an gajeren tsaki taja tare da d'an juyawa ta kalli gefen yamma inda nanne dai-dai bakin babban kemis d'in A.A Aliyu pharmacy yake, ido ta kuma lumshewa kana ta kuma bud'esu a hankali, ido ta tsurawa fuskar Saifuddeen mai tsananin kyau dake gefen pharmacy d'in, a hankali ta fesar da sassanyar iska daga bakinta kana ta kuma bud'e kekyawan idanunta a hankali ta zubasu kan surar Saifuddeen da ya gama zama cikekken matashi d'an 30 years kekyawa ne mai cikar zati da haiba wanda Allah yayi mishi cikar halitta, farine k'al tamkar balarabe sumar kanshi tamkar ba indiye, yanada tsawo dai-dai misali, kana yanada halittar gwanji duk da suturar dake jikinshi yana son b'oye asalin halittarsa ta k'ak'k'arfan namiji mai zarra, fuskarshi mai kyau da haiba ce gashin girarshi kad'ai abin ganine fuskar ras babu saje, a hankali ta kai idonta kan yarinya dake tsaye a gabanshi wacce bazata wuce 7 years ba, da alamun tsantsar so da k'aunan yarinyar a fuskarshi, sunkuyowa yayi d'ai-dai tsawon yarinyar kanta ya shafa tare da mik'a mata ledar hannunshi cikin d'an yin d'igirgire yarinyar ta manna mishi kiss a kumatunshi murmushi yayi tare da juya yarinyar alamun ta tafi. Matashin dake cikin motar nan kalar toka kuwa, shine ya d'an gyara zamanshi tare tsurawa motar dake bayanshi ido ta cikin madubi motarshi yaga sai matsoshi takeyi kuma yaga ba motocin shi bane, bai gama nazartar ya akayiba, sai kawai yaji gib-gib motarnan ta iso gareshi ta bugi wannan motar tashi da yakeji tamkar k'ok'on ranshi motar da aka binne miliyoyi aka saya mishi ita kuma du-du-du yau ya fara hawanta, idanunshi ya rumtse da k'arfi bala'i ji yakeyi ko uban waye ya tab'a mishi motar nan sai ya illatashi. ita kuwa Zaleeha gaba d'aya ta shagala da kallon Saifuddeen da babyn nan sam bata ankare da cewar motartafa na tafiyaba kuma sam ta mance cewa a madakata suke, bata dawo haiyacintaba saida taji motarta ta bugi motar dake gabanta, kana motarta ta d'anyi baya sannan ta kumayi gaba ta k'ara bugar motar dake gabantan, cikin tsananin firgici da razani ta taka birki da k'arfi ji kakeyi, k'uuuuh, ta caki motar ta tsaya. Sautin bugun da tayiwa motarnan da kuma sautin taka birki da tayi shiya jawo hankalin mutanen dake wurin gaba d'aya. Kai mutane suka rirrik'e tare da cewa. "Innalillahi". sabida motar ta kasa sarrafuwa har saida ta kuma bugan jikin motarnan a karo na uku, sannan ta samu ta tsaya, gaba d'aya jikinta rawa yakeyi sabida tsananin tsoro da razani, yayinda duk mutanen dake sashin wurin suka zuba musu ido tare da sassauk'e numfashi da furta. "Alhamdulillahi." duk sautin nan da bugun motar ta Saifuddeen dake bakin kemis d'in nan shi baima juyoba, duk da hatta ma'aikatan cikin kemis d'in saida suka fiffito, idonshi ya zubawa bakin d'aya daga cikin maikatan kemis d'in yana ganin yadda lip's inshi ke motsawa hakan yasa ya gane abinda yake fad'i inda shi saurayin yake cewa. "Innalillahi wannan wacce ce tsautsayi ya rubtawa rayuwarta ta bugi motar Dalla shi kenan zai illata rayuwarta gashi macece ya samu abinda zayita bibiyar rayuwarta." d'aya dake gefenshi ne yayi saurin cewa. "Kai subahallahi *Zaleeha M. B.S. Dukku ce. da sauri Saifuddeen ya juyo ya kalli inda yaga mutanen wurin gaba d'aya suna kallo, dai-dai lokacin kuma wanda aka kira da Dalla ya bud'e marfin motarshi gaba d'aya fuskarshi tayi jazir sabida tsananin bala'i fuskarnan tasa tamkar tayi aman jini, wani irin taku yakeyi wanda yafi kama dana azzalumai, gaban motarta ya nufa gadan-gadan. Yayinda ita kuwa Zaleeha ta zazzaro ido tare da kame jikinta tanajin hanjin cikinta na bada sautin k'ululuku sabida tsananin tsoro da firgici. Shi kuwa yana isa gaban motarta cikin rumtse ido
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148