Skip to content

Chapter 138

Chapter 138

Nakasa Ba Kasawa Bace Book One Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

yasa ta nufi d'akin a hankali ta shiga bakinta d'auke da sallama. sai kuma tayi turus a baki k'ofar ta tanya cikin tsananin kad'uwa da firgita, ido ta zubawa Maryam dake tsakiyar akwatunan ta bubbud'esu gaba d'aya tana nunawa Any Aisha kayan, Yayinda Mama kuwa da yayarta Ruda suke kan gado fuskokin nan nasu tamkar suyi ruwan jini kuma tuni sun barbaɗe ƙofar falon Mama da maganin da Ruda ta kawo wanda aka basu tabbacin in dai Zaleeha ta tsallakashi tofa bazata lamunci zaɓin mahaifin nataba zata tashi hankalin kowa har sai an janye batun auren. cikin sanyin murya Anty Aisha take cewa. "Allah ya sanya al'khairi yasa gidan zamanta kenan iya rai da mutuwa." Maryam ce tace Amin Amin. sai kuma suka juyo suka kalli Ruda dake cewa. "Tir da addu'arki Aisha bakinki ya sari guntun kashi, kifa kalli wannan zuk'ek'iyar budurwa ki fasalta zamanta da gurgu kuma kurma musaki mara amfani kice Allah yasa gidan zaman tane. Ke kuma Maryam da yake baki da hankalin da kishin yar uwarki harda wani cewa Amin." ita kam Zaleeha tamkar an dasa tane a wurin ta kasa tantance abinda kunnuwanta ke jiye mata daga bakin Maryam dake cewa. "Addu'a ita ta dace da Zaleeha tunda dai wannan abun yin Allah ne, ko ana so ko ba'a so in Allah yayi ita matar Saifuddeen ne dole taje gidanshi, kuma ke Mama kin san halin Baba malam me amfanin bad'i babu rai, yak'in da babu nasara ai gwara yin mubaya'a du du dufa auren nan saura sati d'aya ne rak." Da sauri Zaleeha tasa tafin hannunta ta dafe k'ahon zuciyarta dake gab da tarwatsewa, idanunta ta rumtse da azabar k'arfi kanta ta fara jujjuyawa tare da zamewa ta durk'usa gaban Mamansu murya a hargitse tace. "Bana sonshi, bazan zauna da shiba, wlh mutuwa zanyi in aka had'ani dashi please Mama kiyi wani abu a kai." Maryam ce ta d'an kalleta a tausashe dan tasan irin abinda Zaleeha keji a ranta tunda itama a dole aka had'ata da Ya Aminu amman gashi yanzu da tayi biyayya tabi umarnin iyayenta tana ganin ribar haka, duk da zafin zuciya irin na ya Aminu zama yake kamar bawa a gareta, baya son duk wani abinda zai sata zubda hawaye. shiyasa a hankali tace. "Zaleeha kiji tsoron Allah kiyi biyayya ga mahaifinmu zakiga ribar hakan kada ki bari rud'in duniya ya Kaiki ya baroki. Ku dena yakice Saifuddeen dan nakasarsa dan babu wanda yasan k'arshensa, kuma in baka mutuba to ba'a k'are maka halitta ba, shimafa bada larurarnan aka haifeshi ba, kaso 95 cikin 100 ba haihuwarsu ake da nakasaba a duniya suke samu. Kaso 5 ne na cikin 100 ake haifarsu da nakasa, because muma bamu da yak'inin a haka zamu k'are rayuwarmu." Cikin tsawa da masifa Mama tace. "Rufe min baki hegiya mara zuciya, mai mugun fata mu nan in sha Allah lfy lau zamu k'are rayuwarmu. Kuma wlh wlh muddin ina raye Zaleeha bazata zauna da wannan gurgunba. Dan ke kinada macecciyar zuciya sun tankwaraki kin zauna a dole to banda Zaleeha." Cikin sanyi Maryam tace. "Kiyi hak'uri Mama ki gafarceni in furucina ya sosa miki zuciya." ita kuwa Zaleeha mik'ewa tayi ganin sunk'i su sarara bare su saurareta, ficewa tayi daga gidan a guje. A Cikin gidan kuwa, Anty Aisha ce ta kalli yayun nata cikin kafiya da fad'in gsky tacewa Mama. "Da hankalinki da tunaninki kike biyewa zugar wacce kin san batayi imani da Allah da manzonsa ba, bare ta yarda da k'addara mai kyau ko sab'aninta." A zafafe Ruda tace. "Ke Rebeka ni kike gayawa haka?." cikin tsuke fuska da tsawa tace. "An gaya mikin! K'arya nayi ne, imanin gareki tunda har yanzu baki samu tsarkin zuciyaba, kina kafura, mara lissafi zata zauna tana bin zugarki, lallai ke yar uwata ce kuma yayata Amman baki da hurimin kirana da Rebeka call me Aisha in bazaki iya ki bari." A zafafe tace. "don't call me Rebeka again." Sai kuma ta juya ta kalli Maryam tace. "Maryam tashi mu tafi, ni dai ina bayan Baba Malam daga yau kuma zamu fara shirye-shiryen auren nan." A hankali Maryam ta maida akwatunan duk wurin zamansu, sannan ta mik'e tabi bayan Anty Shatu kamar yadda suke kiranta kenan... Mama kuwa da kafurar Yayarta Ruda, nan sukaci gaba da tubka da warwara, suna tubke yadda auren Zaleeha da Abdussalam, kana suna warware auren Saifuddeen. Ita kuwa Zaleeha tana fita kai tsaye (Jonapwd) ta nufa tuk'in takeyi tamkar wacce zata bar garin. tana shiga harabar wurin tayi parking, cikin sauri ta fito gaba d'aya ida nunta dishi-dishi suke mata, kai tsaye office d'in Ishaq ta kutsa kanta sam bata iya amsawa mutanen nata gaisuwar da suke mata. shi kuwa Ishaq tun tana babban parlour yajiyo mgnar Sani na mata sannu da zuwa so koda aka turo k'ofar office nashi aka shiga yasan itane. Tana ganinshi kawai sai rauni ya rufe masifarta dan iya tsawon zamanta da ishaq a matsayin yayanta Ahmad take kallonshi ishaq yanada mutunci a ida nunta gashi last time ta surfa musu rashin ɗa'a kuma daga nan yake fushi da ita, a hankali taja kujerar dake fuskantar wacce yake zaune a kai ta zauna. sunkuyowa tayi ta kifa kanta bisa glass table dake tsakiyarsu kawai sai ta saki wani irin mawuyacin kuka mai cike da rauni da tarin k'uncin rayuwa. cikin tsananin mmki Ishaq ya zubawa saitin inda yakejin kukan idanu tamkar yana ganinta. sai kuma yayi shiru kamar baya wurin yana jin sautin kukanta na ratsa kunnuwanshi. Kusan tsawon 10 minutes tana kuka, bai kulata ba, ita kuma bata bariba, har 20 minutes har ta zarta rabin awa tana kukan bil hak'k'i da gsky. daga jin kukan kasan daga cikin zuciyarta yake fitowa kukane mai tattare da k'una da tsoro, sosai Ishaq ya fara jin tausayinta na kamashi ai ko ba komai ita macece kuma mai rauni. cikin sanyin sauti yace. "Ya isa, ya isa haka Zaleeha kada ki cutar da kanki." jin haka sai kukanta ya k'aru cikin kukan murya a raunace tace. "Malam Ishaq bana sonshi, wlh bana sonshi, na tsaneshi, inada wanda nakeso wanda ya bada ranshi da lfyarshi domin kare mutun cina pleaseeee Ya Ishaq kace mishi ya janye batun aure a tsaka ninmu, wlh muddin akayi auren nan cikin mu biyu dole d'aya zai rasu." Sosai ya nitsu yana jin kala manta sai ya kuma ji alamun tazo tana durk'ushe a gabanshi a hankali tace. "Dan Allah Ya Ishaq ka zame min Garkuwa na mana a karo d'aya dai a rayuwa ta, dana rok'eka abu dan Allah dan annabi kaji tausayi na mana ka rabani dashi kar in rasa raina please ya Ishaq kada ka bari ayi min auren dole." Sai ta kuma kife kanta bisa d'aya kujerar taci gaba da kuka. Sosai raunin ishaq ya halarto kan zuciyarshi, me zai hana ya taimaketa, to amman bari yaji meyasa bata son Saifuddeen, a hankali yace. "To waye kike son?." murya a raunane tace. "Ban sanshi ba?." fuska cike da mmki yace. "Ina yake to me sunanshi?." A hankali tace. "Duk ban saniba sau d'aya muka tab'a had'uwa shiyasa a gidanmu ake cewa wai ba mutun bane al'janine." Da sauri yace. "Yes al'janine mana nima haka zance, tunda shi gaibune." kuka

Table of Contents

Chapters

148 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148