Skip to content

Chapter 16

Chapter 16

Nakasa Ba Kasawa Bace Book One Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

to duk abin saidawa in dai na cine cinikinshi ya mutu da rana sai dai in darene, to kaga ita kuma kasuwa da rana takeci, shi kuma d'an dukkune kullum zuwa yake da safe bayan sallan isha yake komawa, toh shine yaketa nazarin wani abu zai fara saidawa cikin azumin, da yayi zaton zaike saida dabino da kwakwa to gsky itana sana'ar yawace kuma kada yaje garin talla ya tsalli dabino ya afa a baki." Ya k'arishe mgnar cikin tsokana da wasa, k'eyarshi Saifuddeen ya bugi tare zare mishi irin yadda akewa yara masu surutu, dariya sukayi baki d'aya ganin yadda Jabeer ya tura baki tare da cewa. "To nayi shiru." shi kuwa ogansu Jabeer gyara zama yayi tare da cewa. "Baba Bello bananma da wuri zaka shiga itikafin ne?." cikin kauda zancen Dottijon yace. "Waya ce da kai itikafi nake shiga, kawai dai ina ajiye kasuwancin ne da ramadan sabida tsufa yazo kuma azumi na wahaldani." Murmushi kawai Alhaji Adamu yayi sabida yasa Baba Bello itikafi yake shiga shi kuma yana b'oyewa sabida gudun riya, shiyasa yake ce musu hutun Ramadan kawai yakeyi. shiko Dottijon cikin kulla ya kalli Saifuddeen kana murya a tausashe yace. "Yaro na zaka iya yawon bin shago layi-layi kana raba musu ledodi, suna yi maka biyan bashin daddawan k'auye?." murmushi yayi tare da gyad'a mishi kai alamar zai iya. Shiko Dottijon sauk'owa yayi daga kan keken nashi kana ya zauna kusa da Saifuddeen cikin tattausan lafazi yace. "Kullum in azumi yayi ina barin kasuwa duk costomomina sai dai suyi ta kame-kamen sayan leda wurin wasu, anayin salla kuma da kwana biyu zan dawo to duk masu kawo musu sai su bari inci gaba da kawo musu kamar kullum to amman tunda gashi bana Allah ya had'ani da kai, in dai ka amince kayi al'k'awarin rik'e amana to zan kaika wurin babban dilanmu da yake bamu talla bisa farashi mai sauk'i, zaike baka kaya ba tare da ka bashi ko asiba, sai kai kuma ka tallata ka d'ora ribarka, misali yau in ka kawo bazasu baka kud'iba sai gobe in ka kawo musu sai su baka kud'in na yau, na yau kuma sai ka kawo musu na gobe. to wasu ba ruwansu kana kai musu zasu biyaka, wasu kuma dole sai goben, to anan amanar da nakeso ka rik'e zan kaika gaban dilanmu amatsayin kai jikanane dan in baisan wani nakaba bazai bakaba, in ya amince zai baka kuma zan had'aka da costomomina baki d'aya, nasan duk masu amana da gsky ne, suma kuma zan basu amanarka kada su ganka bakaji su cuceka, nasan zaka iya kasuwancin kam tunda kayi karatu zaku rink'ayin komai a rubuce." cikin lumshe ido Saifuddeen ya had'e hannunsu wuri d'aya kana ya jinjina mishi sannan ya zaro biro ya fara rubutu a tafin hannunshi saida ya gama kana ya nunawa Jabeer nan Jabeer ya fara karanta abinda ya rubutan. "In sha Allah Baba bazan kasance mara gsky ba a cikin had'akarmu, nayi alk'awarin rik'oda gsky da amana bazan kunyataka ba, ga Oga Adamu da abokina Jabeer da sauran maikatan shagon nan su zama shaida, Allah kuma ya bamu sa'a ngd matuk'a Allah ya k'ara lfy da wadata." Murmushi sukayi baki d'aya, daga nan Dottijon nan yayi gaba Saifuddeen na binshi a baya har shagon babban dilansu na leda, nan ya gabatar dashi ga Alhaji Babayo, ba wani dogon bincike Alhaji Babayo ya aminta da Saifuddeen sabida ganin Baba Bello ne ya kawoshi Dottijon da sunfi shekaru 20 suna tare a harkar leda. shi kuwa Baba Bello ya musu bayanin Saifuddeen kurmane amman yana gane duk abinda ake cewa in yana ganin bakin mutun. an yarda tuni an rattaba sunan Saifuddeen a jerin sunayen masu amsar talla, yasa hannu shaidu sun saka hannu. daga nan suka juya Baba Bello ya tasa Saifuddeen a gaba duk inda yasan yana kai ledodi saida ya nuna musu Saifuddeen yana ce musu jikanshi ne, kuma shi zai rink'a kawo musu Leda cikin azumi har sai bayan sallah shi zai dawo, to dama duk kostomominshi sun san da baya kawo musu leda cikin azumi to sai sukaji dad'in wannan ci gaban koda sukaje shagon Alhaji Ibrahim baban Hisham yaji dad'in abun sosai ya sanya albarka haka dai duk wunin wannan ranar kam sukayi shi ranar bag d'in pure water takwas kawai ya saida sai dai ya saida su Coca-Cola sosai. Sun bari akan sai ana gobe azumi zai fara tallan ledan tunda ranar Baba Bello zayi zuwan k'arshe sai kuma bayan sallah. Anayin sallan magrib Salisu yazo ya d'aukeshi kamar kullum, yau wurin mai shayi sukaje kwai aka soya musu da indomi kana sai ruwan tea, bayan sunci ne sukayi sallan isha, kana suka kama hanyar Dukku. Koda suka isa Saifuddeen na sauk'a Salisu ya zaro dubu biyar d'in balance ya mik'ashi, amsa yayi kana ya zare 2k ya bashi yace yaje ya sayawa Mamanshi sugar da Lipton baiso karb'a amman dole ya amsa, shi kuwa Saifuddeen yana shiga gida kai tsaye d'akin Umminshi ya shiga inda ya sameta ita da Aunty Nina suna hirarsu. Bayan sun gaisane ya mik'e tare da yiwa Ummi alamun bari yaje yayi wonka. To tace mishi kana sukaci gaba da hira, shi kuwa solle jikinshi yayi suk'al kana ya shafa mai tare da fesa turare, canza kaya yayi sannan ya nufi tsank'aya wurin Bappa Ali duk da yasan yau al'hamis ne ba karatu so ya kuma san canne wurin zaman Bappa Ali ko yaushe bayan sun gaisane ya mishi bayanin canjin sana'ar da zaiyi da tsarin kasuwancin da dokokinshi, sosai Bappa Ali ya gamsu da hakan addu'a yayi da fatan al'khairi. Koda ya tashi tafiya sai ya kwaso cinikinsa na yau duka da riban da jarin duk dubu 3 ne. sai ya kuma zaro da sauran dubu ukun balance d'in ya had'asu inda suka bashi dubu shida kenan. Cikin nitsuwa ya mik'awa bappa Ali. Cikin tsuke fuska da fad'a bappa Ali yace. "Me zanyi dasu? shin ba nacema Ka dena bani kud'iba in dai ban bakaba to ai baici ka baniba, fatana Allah ya bud'a maka yadda zakayi kaci gaba da rik'e marayun k'annenka dani bappanku na gaza rik'ewa." da sauri ya girgiza mishi kai kana ya rubuta mishi. "Dan Allah Bappa Ali ka amshi kud'innan in dai ba rainawa kayiba, meyasa kullum in na baka abu baka amsa, to in ban makaba waye zanyiwa kainefa uba a garemu ka sanya al'barka a lamarinmu in bani dashi zan baka ne?." to ganin ranshi ya b'acine yasa Bappa Alin amsar tare da samishi al'barka. Har ya tashi sai ya kuma zauna ganin Bappa Alin ya rik'o hannunshi bayan ya zaunane yake shaida mishi wannan mutumin daya kad'e Nuruddeen ya kawo musu kayan azumin. Kama daga shinkafa, taliya, doya, Couscous, indomi, mai, manja, magi, gishiri, onga, kwai madara da Milo sugar Lipton, da kud'i 10k. wani irin tsuke fuska Saifuddeen yayi tare had'e rai sai ya kuma yiwa bappa Ali alamun tambayar sun karb'ane?. kai bappa Ali ya gyad'a mishi alamar eh sun amshi kayan, cikin takaici ya... By *GARKUWAR FULANI* 8/ *NAKASA BA KASAWA BACE* *PAGE 5* NA *AYSHA ALIYU GARKUWA* πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ _Wannan shafi gaba Ι—ayanshi tukuicine da saudaukarwa ga Umar ibrahim Wambai, Allau rabbi ya baka lafiya!_ Free page🀝🏻 A

Table of Contents

Chapters

148 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148