Chapter 113
Chapter 113
yadda Ummi batayi akan suci abinci fir sukak'i, dole Ummi ta hak'uri kana sukayi musu rakiya har bakin motarsu inda dama direbansu na nan yana jiransu. saida suka tafi kafin su Ummi suka koma cikin gidan. Washe gari kuwa stab Saifuddeen ya shirya cikin shiga ta al'farma sai k'amshi yake zubawa cikin shirinshi na tafiya Dukku. Yana ƙoƙarin ɗaukar wayarsa dake aje kan gado, yaji anturo ƙofar ɗakin anshigo, Ishaq ne yashigo bakinsa ɗauke da sallama yayinda shima yasha ado cikin yadin getzner me ruwan toka sosai shima yayi kyau. Tamkar wanda ke gani ya lumshe idanunsa tare da faɗin. "Kayi kyau sosai Saifuddeen!" Murmushi Saifuddeen yayi yana me ƙoƙarin ɗaukar wayarsa don ya rubutawa Ishaq din saƙo, maganar Ishaq ta sake dakatar dashi inda yace. "Bama sai ka sha wahala wajen rubutu ba nasan me zaka tambaya, cewa zakayi dawani idon nasan kayi kyau, bayan kuma nasha faɗa maka cewa masu ido abu ƙalilan zasu nunamin donni ma inaganin komai da zuciyata, zuciyata itace idanuna!" Murmushi Saifuddeen yasakeyi aransa yana mejin ƙarin ƙaunar abokin nasa, cikin kulawa ya turawa Ishaq saƙo awayarsa kamar haka inda yace. "Nikam nagaji da wannan surutun naka ni yanzu burina shine naganni a Dukku inda zan faɗi abun dake raina". Ishaq na gama jin saƙon yasaki murmushi abayyane yace. "Lallai Zaleeha tacika mai sa'a dahar ta iya sace zuciyar mutum ɗaya wanda yazama tamkar da dubu, jajirtaccen Namiji wanda samun irinsa keda matuƙar wahala" Murmushi kawai Saifuddeen yayi inda ya danna madannin kekensa nan yafara tafiya, yana gaba Ishaq na biye dashi abaya haka suka fito daga cikin ɗakin, Ummi dake tsaye tana ganinsu ta saki murmushi cike da so da kuma tsananin tausayinsu tace. "Har kun fito, amma dai kafun kutafi ai dai zaku tsaya kuci abinci, musamman ma kai Ishaq musamman na aje maka ragowar dambun nama don nasan kanaso" Murmushi Ishaq yayi tare da cewa. "Shiyasa nake sonki Ummi na, yanzu dai abani dambun natafi dashi sai naci acikin mota don naga wannan abokin nawa sauri yake kamar wanda zai tashi sama burinsa kawai shine ya gansa a Dukku" Murmushi Ummi tayi tare da cewa. "To bari kawo maka sai katafi dashi amma dai inkun dawo kabiyo tanan zanyi abincin dare harda kai!" Murmushin jin daɗi Ishaq yayi inda yace. "Insha Allah!" Nan Ummi ta kawo masa dambun naman, har bakin mota ta rakasu inda tayi musu adawo lafiya, Hayatuddeen kuwa ɗan kalen baki hadda cewa Hamma Saifuddeen ɗin nasa wai yakawo masa tsaraba. Ƙarfe Biyu daidai suka samu isowa cikin garin na Dukku, gari me ɗauke da tarin al'barka da shuke shuken tsirrai masu kyau da ƙawatarwa, agidan Baffa Ali suka sauƙa inda yacika da tsananin mamakin ganinsu da yayi don sam Saifuddeen baisanar masa cewa yana zuwa ba. A falon Baffa Ali'n suka zauna inda Aunty Nina takawo musu ruwa tare daɗan abun motsa baki, gyara zama Baffa Ali yayi tare da duban Saifuddeen cikin kulawa yace "Kashammace ni Saifuddeen nida jibi nake shirin tahowa Gombe'n sai kuma gashi kazo batare da kasanar dani ba, ai da kafaɗamin kanada buƙatar ganina to tabbas da har gida zanzo nasameka". Murmushi Saifuddeen yayi tare da duban Baffan nasa, saƙo ya rubuta awayarsa kamar haka, kana ya miƙawa Baffa Ali'n. "Kagafarceni Baffa Ali, magana me mahimmanci ne ta kawoni, naƙi sanar dakai zuwana ne kuma saboda nasan idan kaji cewa zakayi nabari zaka zo". Ɗan murmusawa Baffa Ali yayi bayan yagama karanta saƙon inda yace. "Shikenan Saifuddeen ina sauraranka, tabbas nasan baƙaramar magana bace zata tasoka daga Gombe zuwa nan". Ajiyar zuciya Saifuddeen yayi tare da sunkuyar da kansa ƙasa, Ishaq ne yaɗan gyara zamansa tare da yin gyaran murya cikin nutsuwa yace "Saifuddeen yaga mata kuma yana fatan aurenta wannan dalili shiyasa mukazo don musanar dakai, saboda yana da buƙatar anemamasa izinin fara zuwa zance daga wajen manyanta kamar yanda addini ya koyar!" Wani irin murmushin farin ciki ne ya bayyana akan fuskar Baffa Ali, cike da tsananin jin daɗi yace "Alhamdulillah masha Allah, Allah Abun godiya, haƙiƙa kun zomin da labari mai daɗi Ishaq, na kuma yi murna ƙwarai matuƙa, tabbas yanzu naƙara yarda dacewa NAKASA BA KASAWA BACE, haka kuma nakasar Saifuddeen bata tauye masa zamowa cikakken ɗa Namiji ba, Allah Abun godiya". Duban Saifuddeen wanda kansa ke ƙasa Baffa Ali yayi cike dajin daɗi yace . "To ita yarinyar a inane take sannan wanene mahaifinta?" Ishaq ne yace. "Anan Gombe take cikin G.R.A sannan mahaifinta babban Malami ne wanda ƙasa gaba ɗaya ke alfahari dashi Malam Bashir!" Cikin jin daɗi Baffa Ali yace "Alhamdulillah mungodewa Allah, Insha Allahu yau yau ɗinnan zan sanar da aminin mahaifinka Malam Ashiru, don kuwa gobe zamu dira acikin garin Gombe, bazamuyi k'asa a guiwaba don ba'a wasa a lamarin aure". Sosai daɗi ya cika zuciyar Saifuddeen wani irin farin ciki yakeji, yayinda zuciyarsa ta cika da annuri, kasancewar tanaji ajikinta cewa takusa samun muradin ta. Anan cikin Dukku su Saifuddeen suka wuni inda suka zazzaga ƴan uwa da kuma abokan arziki a gidan Goggo Dada ma sun dad'e. har gidan Malam Ashiru sukaje da Baffa Ali, nan Baffa Ali yayi masa bayani, sosai yaji daɗi shima kuma yayi na'am tare da nuna farin cikinsa, inda suka tsayar akan cewa gobe insha Allah zasu sauƙa acikin garin na Gombe. Anan cikin Dukku su Saifuddeen sukayi sallan Magriba daganan suka kama hanyan dawowa cikin Gombe. Zaleeha ce zaune acikin falon Mahaifiyarta yayinda ta tanƙwashe ƙafafunta washe guda, kayan ciye ciyene zube agabanta dangin su snacks da chocolates, sanye take da wata ƴar riga marar nauyi wanda taɗan kama jikinta, idanunta ta lumshe akaro na barkatai tare da jingina bayanta da jikin kujera, damuwane ke ƙoƙarin hallaka nutsuwarta, yayinda wutar ƙaunarsa ke tsananin ruruwa acikin zuciyarta, gaba ki ɗaya kwana biyunnan sam bata da nutsuwa, ko abinci bata wani ci sosai, sam batajin daɗin zaman gidan nasu ayanzu, don kuwa akowacce rana sake hura mata wuta ake akan fitarda gwaninta, sam idanunta sun rufe, bataji bata gani akan soyayyarsa, akullum akuma koda yaushe, duk bayan shuɗewar wasu mintuna soyayyarsa ƙara ninkuwa take azuciyarta, yayinda abun ke ƙara girmama akowacce rana, don yanzu hartakai ta kawo hatta numfashin da zata shaƙa da Soyayyarsa yake tafiya, zuciyarta tuni ta narke akan tsantsar ƙaunarsa, takanyi kuka sosai akan soyayyarsa amma babu me rarrashi,, ahankali take fitar da numfashi tana mejin tsananin kewa da begensa. Zakariyya da tun ɗazu ke tsaye akanta batare da ta sani ba ya gyara tsayuwarsa, duk da cewa suna yawan faɗa atsakaninsu, amma duk da haka yana matuƙar son yayartasa, haka kuma yanajin duk wata damuwa tata shima damuwarsa ce, cikin tausayawa yace. "Adda Zaleeha!" Jin muryan Zakariyya acikin kunnuwanta yasanyata buɗe idanunta wanda sukayi ja. Ganin yanda idanunta sukai ja, yasanya Zakariyya zama akusa da'ita cike da kulawa ya kamo hannunta, cikin ƙaunar ƴar uwartasa kuma yayarsa yace. "Wace damuwace haka take neman rabaki da nutsuwarki? wace damuwace haka ta sauya gaba ɗaya yanayinki? Dan Allah Adda Zaleeha kidawo kamar yanda kike da, banason wannan damuwar taki, kiduba fa kiga yanzu ko ƴar faɗannan bamayi banajin daɗin hakan wlh nafi son muna fad'a abinmu a shiga tsakaninmu aji kunya!". Idanunta ne sukayi rau rau, yayinda hawaye ya cika cikinsu, cikin sassanyar muryar dake
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148