Skip to content

Chapter 112

Chapter 112

Nakasa Ba Kasawa Bace Book One Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

rashin sanin inda Saifuddeen ɗin yace zaije shiyasa cikin karaɗi yace zai bisa, suna kammala cin abincin, Saifuddeen ya wuce ɗakinsa, wanka ya ƙarayi inda ya shirya kansa cikin wata tsadaddiyar shadda Milk colour ɗinkin half jumper wanda taji coffee colour'n aiki a wuyanta, sosai shaddan ta sake fidda sihirtaccen kyaunsa, wata haɗaɗɗiyar hulan zanna bukar ya kafa akansa wanda gaba ɗayanta kalar coffee gareta saidai tana da ratsin milk colour ajikinta, hatta takalman dake ƙafansa kalan coffee garesu, inda farar fatarsa tafito tayi ɗas acikinsu, tsadadden agogo ya ɗaura ahannunsa inda ya feshe gaba ɗaya jikinsa da turare, masha Allah Saifuddeen baƙaramin kyau yayi ba, sai ayanzune ma nake lura da cewa ba kayanne sukeyi masa kyau ba shine keyiwa kayan kyau, don kuwa kowani irin kaya yasaka sai yayi musu kyau, haƙiƙa Allah mabuwayine ayayin daya tauye Saifuddeen da tawaya irin ta rashin jin magana da takawa da k'afaffunshi sai ya basa wani irin ɗanɗareren kyau haɗi da kwarjini yakuma sa ya zamto abunso azuƙatan mafi yawancin mutane, haƙiƙa kyawun Saifuddeen madubi ne wanda ko wacce cikakkiyar ƴa mace zataso fuskanta don ganin kanta acikin sa. falon ya fito cikin kamala ya zauna gefen Ummi yayinda Raliya da Hayatuddeen ke gefe sunata hirar zasuyi kewar Raihana da itama gobe zata koma KD da mijinta. nan suka d'anci gaba da hira, cikin hirar Ummi tace. Raliya tare da cewa. "Rana tayifa tashi ki shiga kitchen ki hada mana lunch kinga yau Hammanku wunin gida zaiyi yace yau lokacinsa namu ne." dato ta amsa kwana ta mik'e ta shiga kitchen. Raihana ce ta mik'e da sauri taje bakin k'ofar falon nasu jin ana d'an bubbugawa. cikin fara'arta da sakin fuska ta kalli Mom d'in Amina tare da cewa. "Sannu da zuwa shigo ciki." cikin mmki ta kalli Amina dake bayan Mom da sauri ta k'ara matsawa ta basu hanya tare da cewa. "La kamar na ganeki, ku ise." murmushi sukayi baki d'aya kana suka kutsa kai cikin falon bakinsu d'auke da sallama. Hayatuddeen ne ya mik'e da sauri tare d'an yin tsalle yayi gaban Amina tare da cewa. "La likita bokan turai? Yaushe kika zo gombe? waya kwatanta miki gidanmu?." Ummi ce ta mik'e cikin kamala take cewa Mom. "Lale marhabin maraba lale ga wurin zama." cikin sakin fuska Mom tace. "Yauwa." ita kuwa Ummi dak'uwa tayiwa Hayatuddeen tare da cewa. "Kai auta me haka zaka tsareta da tambayoyi?." kanshi ya fasha tare da nuna mata kujera kana yace. "Kai naji dad'in zuwanki, zauna mana." murmushi tayi tare d'an hararanshi k'asa-k'asa kana tace. "Ba nace maka munyi fad'aba?." dariya yayi sosai kana yace. "Karki damu zan rarrasheki da dambun naman da Ummina tayimin." Ummi kuwa cikin rashin saninsu ta gaisa da Mom. kana ta juyo ta kalli Amina dake durk'ushe a k'asan carpet kusa da k'afafun Ummi tare da cewa. "Ummi ina wuni." cikin sakin fuska Ummi tace. "Lafiya lau Alhamdulillahi." kanta ta d'an d'ago ta kalli Saifuddeen dake can gefe kan weelchair d'inshi da system nashi bisa cinyarshi yana sarrafa cikin gwarewa, a hankali tace. "Ya jikin Hamma Saifuddeen?." zuba mata ido Ummi tayi tare da cewa. "Alhamdulillahi jiki kam da sauk'i sosai." a kunyace tace. "Allah ya k'ara sauk'i ya bashi lfy rabbi ya sa yanada rabon sake takawa da sawunshi." cikin wani irin tsananin jin dad'in addu'arta ga Saifuddeeen Ummi da yaranta duka suka amsa da. "Amin Amin Ameeen ya rabbil izzati". cikin nitsuwa Ummi ta kalli Mom daketa kallon Saifuddeeen kana tace. "Sai dai har yanzu ban ganeku ba?." da sauri Hayatuddeen yace. "Ummi baki gane Amina ba itacefa wanna nurse d'in dake kula da Hamma a Abuja kafin mu tafi Indian." cikin mmki Ummi tace. "Allah sarki Amina kai ngd ngd matuk'a Allah bar zumunci." cikin tsananin jin dad'i Amina tace. "Amin." Raihana ce tayi sauri cewa. "La wlh kuwa nima saida ka fad'a na tunata, yaudin tayi kyau da yawane shiyasa bamu ganeta ba." dariya sukayi baki d'aya, yayinda Raliya kuwa take ta kawo musu ababen sha dana motsa baki. ita kuwa Ummi da kanta ta kalli Saifuddeen lokacin da Amina ta kallonshi. tab'ashi tayi tare da nuna mishi Amina da mom sannan tace. "Nurse d'inka ta Abuja ne da mamanta ko?." ta k'arishe mgnar da kallon Amina alamun tambaya, cikin nitsuwa ta gyad'a kanta alamun eh. shi kuwa Saifuddeen cikin d'an sassauta had'e fuskarsa ya gaida Mom tare da mata godiya duk cikin body language. sosai Mom ke kallonshi, shi kuwa kauda kanshi yayi daga kallonsu sam yak'i yarda ya kalli Amina. shi kuwa Hayatuddeen sai jan Amina da hira yakeyi hakama Raihana. Ummi kuwa da Mom hirar ciwon Saifuddeen suke d'an tabawa. Raliya kuwa tuni ta koma kitchen. Mom ce ta kalli Amina tare da cewa. "Mu tafi ko Amina lokaci ya tafi." cikin son bak'i Ummi tace. "A a ai kwa tsaya kuci abinci." da sauri Mom ta girgiza kai tare da cewa. "A a kai Alhamdulillahi ai a k'oshe muke, jiya muka shigo gombe bikin yar k'awata a nan unguwartaku, to shine fa Amina na zancen Saifuddeen sai aka samu wanda ta sanshi da gidan naku har ta kwatanta mana, shinefa fir Amina tace sai munzo, ashe ba nisama layi biyu tsakani." cikin jin dad'i Ummi tace aiko na gode matuk'a wlh naji dad'i. Amman dai kuyi salla kafin ku fita tunda an kira sallan azahar." sam Mom bata soba amman dole Ummi tasata suka shiga bedroom ta nuna mata k'ofar bathroom kana ta shimfid'a mata sallaya. Hayatuddee kuwa kitchen yabi Raliya tare da cewa Amina. "Bari inje in kawo miki abin dad'i." murmushi tayi tare da kallon Raihana da ta nufi corridor d'in dasu Ummi suka shiga. ido ta juya kudu da arewa gabas da yamma, ganin ba kowa a falon daga ita sai Saifuddeen da yaketa saurin ya k'arisa aikinsa ya shiga side d'inshi. da sauri ta d'auki goran ruwan Faro ta garashi har zuwa gaban Saifuddeen d'in. Da sauri ya d'ago kanshi ya kalli ta inda yaga an turo goran, fuska ya kuma had'ewa ganin ta zuba mishi sosai ya haɗe girar sama data ƙasa. ita kuwa Amina, murmushi tayi tare da d'aga mishi gira kana tace. "Eye kayi kyau, k'asar Indian ta amsheka ji yadda kayi wani fresh da kai kamar ba kaiba." baki ta tura ganin ya k'ara had'e fuska a hankali taci gaba da cewa. "Bafa zaginka nayiba kake wani had'emin kekyawar fuskarnan taka, ko dai baka son in kalli wannan kekyawan sajen nakane." dib yayi dan baya son yayi abinda zata gane yana gane abinda take fad'an. ganin haka ita kuma ta lumshe ido kana ta bud'esu a kanshi a hankali tace. "Wai kai baka gane mai sonka ne? to in ma baka ganewa ni dai ina sonka, dan kana min kyau." da sauri tasa tafin hannunta ta rufe ido dan ganin Raihana a tsaye a gefeta tanata dariya. dai-dai lokacin Hayatuddeen da Raliya suka fito kitchen, wanda suma suke dariya dan sunji mgnarta ta k'arshe inda take cewa dan kana min kyau. wayyo ai ji tayi kamar ta nitse cikin k'asa ganin hakane Raliya ta jata suka tafi side d'inta inda acan tayi salla. shi kuwa Saifuddeen baibi ta kansuba ya wuce side d'inshi. Koda su Ummi sukayi salla suka fito ba

Table of Contents

Chapters

148 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148