Skip to content

Chapter 78

Chapter 78

Nakasa Ba Kasawa Bace Book One Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

tsananta ne jin tafin hannunshi bisa hab'arta yana share mata hawayen tare da jujjuya mata kai kana yana wani irin sihirtaccen murmushi mai cike da zallan tawakkali da yarda da k'addara, Hayateddeen kuwa kanshi ya kife bisa pillow da kan Hamma Saifunshi ke konce goshinshi ya manna da hab'ar d'an uwan nashi kuka yakeyi mai cin rai da cushe farin ciki murya na rawa yake cewa. "Dukkan jarrabobinmu sukan riskemu da tsananin zafi da tarin k'una, ko yaushe ciwo ko mutuwa basa zabi duk inda Allah ya aikosu nan suke zuwa, mutuwa ta yashe mana jigonmu, yayinda kowa ya yanke k'auna sai ubangiji ya sauk'ar da k'udurarnsa bisa d'an uwana da duniya ke ganin bama zai amfanin kanshi bama bare ya amfane mu, Hamma Saifuna ya karya zaton mutane da suke ganin nakasa kasawa ce, ya tashi ya tsaya kaida k'afa ya shiga rana dare zafi sanyi ya ratsa duhu da ruwa da iska na damuna dan tsaida hawayenmu ya zame mana Garkuwa kana bongo abin jingina jigonmu abin al'faharinmu." sai ya kuma taso ya kalli Hamman nashi da yaketa juya musu kai murya na rawa yace. "Wallahi! Wallahi!! Wallahi!!! da ana canza ciwo da na canzashi ya dawo kaina, da ciwo bazai kuma rab'ar d'an uwana ba da ina da dama da na tsare maka dukkan wata cutar da zata kai ga tab'aka bare ta nakasa mana kai." Ummi kam ta kasa cewa komai sai sunkuyar da kanta tayi k'asa tana zubda hawaye tare da ambaton Allah. Shiko Saifuddeen jawo Hayatuddeen yayi bisa k'irjinshi ya rink'a shafa kanshi cikin alamun lallashi kana ya d'auki woyarshi da d'aya hannun rubutu yayi mai yawa ya mik'a wayar ga Ummi. ba tare da ta kalleshi ba ta amshi woyar, sabida hawayen dake kwaranya a idanunta yasa take ganin rubutun bibbiyu d'ad'd'aya rumtse idonta tayi hawayen da suka cika mata idon suka zubo sannan ta fara ganin rubutun a dai-dai kana ta fara karanta abinda ya rubuta mata "Ni kam Saifuddeeen bani da wani ciwo da zai firgitani koya tayarmin da hankalin a duniya, kamar yadda ganin hawayen Ummi na da k'annena zai sani d'imuwa, zuciyata na k'untatuwa in naga hawayenki, Ya Nuruddeen ya bar komai a hannu na bisa ya k'inin zan hana idanunku zubda hawaye, ya Nuruddeen ya shaida min nakasa ba kasawa bace, ya gina min zuciyata da rayuwata ta yadda zan iya zame muku Garkuwa duk da nakasata, Ya Nuruddeen ya haram tawa hannuwana rik'e k'ok'on bara ya damk'a min Al'k'alami da da jarumta. Ummi ya zanyi da raina? sai yaushe zanyi nasarar tsaida hawayenki? Sai yaushe zan saku farin ciki, Ummi bani da baki dana fad'i miki irin k'unar da zuciyata keyi in naga zubar hawayenki bana jin k'unci a kan larurata sai naga hawayenki na zuba. Ummi kalli yadda Hayatuddeen ke kuka tamkar zai shid'e wannan ya nuna min gazawata ce kenan, ni nasan Ya Nuruddeen bai tab'a barina na zubda kwallaba, to ya akayi ni na kasa hanaku zubda naku hawaye ko dai nakasa tace sila? yanzu Ummi kema kuka kikeyi su Rahma Raihana Raliyya kuwa ya zasuyi, Kalli kunsa Ahmad ma kuka, kalli ishaq bawan Allah da baya ganima kukanku ya sashi kuka, kalli Dr da kanta kun sata zubda hawaye, shin Ummi kin mance imanin bawa baya cika har sai ya yarda da k'addararshi mai kyau ko akasin haka." tuni wani azabebben kuka ya kwabcewa Ummi wanda yasa ta kife mishi woyar gefenshi tare dasa hannunta tsakiyar kanshi ta shafa sumanshi har zuwa kan goshinsa sai kuma ta juya ta fita da sauri, domin tasan in yaga tana kuka zai birkice, Abban Farida kuwa, hannu yasa ya kamo Hayatuddeen suka fita. Yayinda tuni Dr Batulu kuwa tabi bayan Ummi, shi kuwa Saifuddeen hannu ya mik'o ya kamo na Ishaq kamar yadda suka saba, shi kuwa Ishaq murmushin k'arfin hali yayi still kuma hawaye na kwaranya a idanunshi murya a raunace yace. "Ya Rabi'u yace in gaidaka da jiki. Kana sak'on gskysuwa daga k'ungiyarmu sunayi maka fatan samun sauk'i." hannunsu ya k'ara hadewa tare da jijjigawa alamun ya gode. daga nan sukayi d'an hirarsu sannan Ishaq ya fito. Nan ya samu Dr Batulu da Abban Farida sunata lallashinsu. ganin lokacin salla ya kusa yasa suka, sallami Dr Batulu suka tafi ba tare da Dr Adnan ya fitoba. Shi kuwa Dr Adnan ya dad'e tare da Dr Aliyu yana mishi k'arin bayani, inda yace mai tunima an fara mishi alluran, sannan kada su damu zai rink'a taho mishi da abincin daya dace yaci, a nan asibitin Dr Adnan yayi sallan isha kana daga bisani suka shiga wurin Saifudddeen shida Dr Aliyu d'in. suna shiga suka samu, nurse biyu maza masu gyara mishi jiki kamar taimaka mishi yayi wonka da al'wala da da juyashi ya fuskanci Al'k'ibllah yayi niya yayi sallanshi a koncen. Suna shiga su kuma suka fita dan sun gama mishi shirin baccinsa, Yana ganin Dr Adnan yayi murmushi tare da lumshe ido kana ya bud'esu ya kalli Dr Aliyu dake zaune bisa welchair d'inshi, a hankali ya mik'o mishi hannu sukayi musabaha, cikin kula Dr Aliyu yace. "Ya jikin?." lips enshi ya motsa alamun da sauk'i kana ya jinjina kai, shi kuwa Dr Aliyu cikin tausayawa yace. "In sha Allah in an fiddaka zuwa India nanda wani d'an lokacin zaka fara tashi zaune da kanka." da sauri Dr Adnan yace. "Allah yasa." Amin Dr Aliyu yace kana ya duddubashi sannan suka d'an k'ara bashi k'arfin guiwa da sama mishi nutsuwa sannan suka fita, a bakin harabar wurin Dr Aliyu da Dr Adnan suka had'u da Nurse d'innan Amina, da sauri ta iso inda suke, cikin shigarsu ta nurses wanda sunyi mata cib a jikinta sai d'an k'aramin hijabi, hannunta na cikin haljihun gefe da gefen rigardata da iya karta guiwa, rusunawa ta d'anyi tare da cewa. "Sir barka da dare." "Barka dai Amina Usman Jada." murmushi tayi dan yadda ya kira cikekken sunanta, gaida Dr Adnan tayi kana tace. "Sir bari inje in bashi maganinshi, zan wuce gida." jim ya d'anyi kana yace. "To ba matsala amman dan Allah kiyi sammakon zuwa, kinga na damk'a amanar wannan aikin a hannunki, dan naga bafulatanine d'an uwanki." cikin girmamawa tace, "In sha Allah ba matsala zan taho da wuri". daga nan sukayi sallama ita tayi ciki su sukayi woje. A hankali ta tura k'ofar ta shiga bakinta d'auke da sallama, kasan cewar idonshi biyu yana rubutawa Ummi text ne yasa yaga shigowarta, baibi ta kantaba yaci gaba da sarrafa woyar tashi, ita kuwa gefenshi ta tsaya, tana harhad'a alluran da zatayi mishi, bayan ta gama ne ta d'an matsoshi, tare da d'an zuba mishi idanu, kallonshi takeyi tamkar tauraro, gashin girarshi ta zubawa idanu wanda suke tamkar an zanasu da gazal sunyi lub lub dasu kana hancinshi zuwat har baki lips inshi jazir sai shek'ek'i sukeyi, ido ta lumshe tare da cewa. "Matarka taji dad'i koda ranta a bace yake in taga kekyawan fuskarnan taka farin cike zai kauda bak'in cikin." lip's enshi ya d'an tsotsa ta ciki dan yana kallon motsin bakinta ta cikin fuskar woyarshi. So ya gane duk abinda tace. ita kuwa yatsunshi ta zurawa ido yadda yake sassarafa wayar tamkar shi ya halicceta, lips enshi ta kuma kalla kana tace. "Wannan labban

Table of Contents

Chapters

148 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148