Chapter 101
Chapter 101
abinci suka ci. suna zaune a wurin suka jiyo muryar Zakariyya yana cewa. "Mama! Mama!!." bata kulashi ba har saida ya shigo cikin had'e fuska tace. "Sai shegen yawan kira kamar mafarauci ko tsohon makaho." Murmushi yayi kana yasa hannu ya amshi spoon d'in hannun Zaleeha tare fara cikin abincin saida ya had'iyi lomar da yasa a baki sannan yace. "Da Hajja Inna mukazo shine Baba malam yace inzo in gaya miki kije ku gaisa." Tsaki ta d'an ja kana ta gyara zamanta tare da cewa. "Ziyada fa bada ita kuka zo bane?." kai ya gyad'a mata alamar eh sannan ya kalli Zaleeha cikin tsokana yace. "Amaryar watan gobe har kin fara tunanin auren ne haka?." duka ta kai mishi tare tura baki. Shi kuwa ganin yadda Zahira ta zuba mishi idone ya sashi danna mata tsawa. "Ke me haka kike ta kallona kamar tsohuwar mayya, muna fuka kawai." tura baki tayi kana ta kauda kanta sam shi baya shiri da ita. Sunan zaune suka jiyo muryar ya Ameenu yana cewa. "Kai Zakariyya fito ku tafi." Da sauri ya mik'e ya fita. Jin haka yasa Mama mik'ewa tabi bayanshi hakama, Maryam da Zaleeha. Suna shiga parlour Baba malam suka sameshi zaune gaban mahaifiyar tashi tamkar yaro k'arami shi kuwa Ahmad na zaune a gabanshi, bisa dukkan alum farce yake yankewa kakar tasu Habu kuwa na gefensu. Suna shiga ta kalli Maryam cikin son jikar tata tace "Ah Maryama dama kina cikine?." cikin nitsuwa tace. "Eh Hajja inna ina ciki salla nakeyi sanda Zakariyya yaje kiran Mama." "Ayyah." tace da ita tare da kallon Zaleeha cikin yar tsamarsu tace. "Rasa kunya berar tanka uwar kid'e-kid'e, ke ba abinda kika iya sai rawa da wak'a da kid'a ko." Baki ta murguda mata tare da watsa mata harara. cikin zaro ido tace. "Iye ni kikewa wannan kallo lallai wannan yarinya in ba'a aurar da keba to tabbas zaki tashi gari, hegiya mai zubin nasara." Sai ta kuma juyo ta kalli Mama data tab'e fuska ko gaisheta batayi. kwaffa tayi kana ta kalli d'an nata sannan tace. "Kai Bashiru wlh infa kana son tsira da mutuncinka to ka aurar da wannan fitinenniyar yarinyar. In ba haka zataci gaba da worwore maka tubkar da kakeyi. Kullum kana kan hanyar zuwa gidan radio kana shirin tafarkin tsira al'ummar musulmai na k'aruwa da kai. Abin takaici ana gama shirinka sai a sako shirin wannan dujaliyar yar taka wai mushak'ata, haka zatayi ta zubawa wak'ok'i ka jita tanabin waken tamkar zabiya." duk shiru parlour sukayi sai Zakariyya dake cewa. "Ni dai da zata amshi shawarata ta dena bin wak'ok'in tana hanamu jin abu d'aya. Mu jita ko muji radio." Da sauri ta gyad'a kai tare da cewa. "Uhun ai dai kunji ko?." shi kam Ahmad da Habu sai murmushin sukewa inna boris. Ya Ameenu kuwa sai harara yake watsawa Zaleeha. cikin muryar jin haushi Mama tace. "Inna an wuni lfy?." A hatsale Inna tace. "Lau na wuni! gsky ce dai sai na fad'i ehe!." Dariya sosai Ahmad yayi yayinda Baba malam ya murmusa. ita kam Zaleeha ficewa tayi abinta, ita kuwa inna sai cewa tayi. "Dama iyayen yara sunfi son marasaji, shiyasa take son Zaleeha kamar ranta bata son laifinta. Kuma dole in fad'i dan ba yadda za'ayi in haifi d'ana malami ke kuma kizo ki haifa mishi zabiya, amara k'irjin biki." Su duk dai ba wanda ya kuma mgn, shigowa Mamy ne da kulan soyayyun kaji yasata washe baki tare da cewa. "Allah dai ya miki al'barka Mamyn Ahmad." Cikin sanyi Mamy tace. " Amin Amin ." dan ita dai bata fiye son abinda inna kewa Zaleeha ba, dan ita tana matuk'ar son Zaleeha kuma itama Zaleeha tana matuk'ar sonta. Ido suka zuba mata ganin ta mik'e tare da cewa Zakariyya. "Shalele na maza tashi mu tafi." da sauri ya amshi kular sannan Suka fito, suna zuwa parking lot nasu Baba malam yace. "Inna muje in maidaki." da sauri tace. "Lalala bari a machine d'in Shalele na mukazo, kuma a kanshi zamu koma." Cikin tsoro baba malam yace. "Inna a machine kuwa, to Ahmad ya maidaki ko Ameenu." Kama hannun Zakariyya tayi tare da cewa. "Muje ko Shalele yaro yana jin dad'in yau na hau machine d'insa kuma shine zaku hana." Habu ne yayi dariya tare da cewa. "Allah sarki watarana sunan hak'oranta babu." Mamy ne tayi mushi dak'uwa su kuwa jikoki suka k'elk'ele da dariya. Koda suka koma cikin gida Baba Malam da Ameenu da Ahmad da Habu mgnar Zaleeha sukaci gaba da d'an tattaunawa inda shi Ahmad yaje jaddada musu wai al'janine. Jirgunsu na sauk'a a Abuja. Ya Rabi'u da kanshi yazo ya d'aukeshi dan acan zasu kwana sai da safe zasu samu jirgin Gombe. Sosai suka samu kulawa da karramawa ta musamman a wurin Aunty Mami. Inda tayi tayiwa Hayatuddeen tsiya wai ya zama ba'indiye. Washe gari k'arfe tara na safe jirginsu zai tashi. So tun bakwai da rabi suka fito kai tsaye asibitin su Dr Aliyu sukaje. Sosai fa Dr Aliyu yaji dad'in ganin Saifuddeen ya fara samun lfy, Dr Batulu kuwa saida akayi mata kwatancenshi sannan ta tunoshi dan da fari tayi zaton ko ba indiye ne yazowa Dr Aliyu ziyara. Karfe tara dai-dai jirginsu ya d'aga zuwa Gombe doma. A hankali Hayatuddeen ke tura weelchair d'in da Saifuddeen ke zaune a kai, cikin shiga ta alfarma, wani dakekken yadine mai tsananin azabar kyau blue irin blue mai hasken nan sai ratsin d'igo-d'igo yellow irin yellow mai d'an duhun da za'a iya cemai ruwan k'asa. Sai wata dakkeyar hukar damanga mai azabar kyau shina irin kalan kayanshin sai kuma takalminshi sau ciki suma kalar yellow mai d'an duhuwa, sai agogon Gucci na fata shima kalan takalmansa, ya kafa hular tayi ras a kanshi, Sajenshi ya konta lib wanda hakan ya k'ara k'awata kekkyawar fuskarsa farar fatarshi ta k'ara baiyana red lips ɗinsa suka kara yin kyau cikin zagayen saje da kota million dake fuskarshi. Shi kuwa Hayatuddeen wasu k'ananun kaya yasaka masu azabar kyau. Tura weelchair d'in yakeyi a hankali da hannu d'aya, yayinda d'aya hannun kuma ke janye da trollinsu. a d'aya sashi kuwa ma'aikatan jirginne ke turo sauran kayan nasu wanda yake hade da wani weelchair d'in a ciki da dai sauran abun buk'a tunsu. A hankali iska mai sanyi ke ratsa jiki da zuciyar Saifuddeen. Tasbihi yakeyi ga ubangijin talikai daya sake nufarsa da dawowa k'asarsa jiharsa ta haihuwa wacce lokacin d'aya barta baisan inda yake bama tsawon shekara d'aya kenan dayawuce. Isakar ya kuma shak'a tare da lumshe idanunshi yana maijin wani yanayi mai kashe jiki. Suna isowa inda masu tarbarsu suke, Kamar daga sana Hayatuddeen yaji an ruggumeshi ta baya, da sauri ya juyo tare da sakin weelchair d'in , ganin Raliyya da Faruq ne ya sashi hadesu da jikinshi cikin tsananin jin dad'i, jin sun sakeshi ne yasashi binsu da ido ganin inda suka nufa, Adda Rahma ne sunkuye a gaban Saifuddeen dayi mishi wata iriyar rugguma ta yan uwa na jini, madadin tayi mgna ina sai murmushi takeyi ga kuma hawaye nata kwaranya a idanunta. Hakama Rainaha sarkin kuka tuni ta kasa isowa inda suke sai wani irin sark'ekk'en kuka da takeyi. Ahmad kuwa wayarshi ya zaro yanata yi musu hoto a cikin duk motsin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148