Skip to content

Chapter 8

Chapter 8

Nakasa Ba Kasawa Bace Book One Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

yace. "Saifuddeen kasha ruwa zakaji sanyi a ranka." a hankali ya fara shan ruwan domin jin zuciyarshi yake tamkar ana soya mishi ita, ajiyan zuciya ya rink'a sauk'ewa akai akai kana hawayenshi suka tsagaita, Ya Nuruddeen d'inshi ne ya fad'o mishi a rai, tabbas da yana raye da bazai bari kukansu ya tsanantaba, wani numfashi yaja kana ya kalli Malamin nashi da yake ce mishi. "Tashi muje woje Saifuddeen muje ka tsaya a sallaci gawan mahaifinka, kayi mishi addu'a a madadin kukannan da kake mishi, ka sani dukkan tsanani yana tare da sauk'i in sha Allah muna zatawa d'an uwanka da mahaifinka rahama, kada kayi musu kuka domin su mutanene na gari musu imani da tawakkali basu da abakan musu bare na fada ko gaba, ka sani babu maraya sai rago, kuma nakasa ba kasawa bace. Kada kayi ta kuka domin kukanka shi zaisa yan uwanka kuka, kuma kukanku shi zaisa mahaifiyarku kuka har ta kai ga ta kamu da wata cutar ka daure ka jumre ka zama Garkuwarsu." Cikin tsanani rauni ya mik'e tare da yi mishi alama da yaji zai bari, daga nan sukaje suka sallaci gawar kana aka kaita makwancinta. Nan aka zauna zaman makoki. Yau akayi sadakan Uku, duk da haka Bappa Ali dasu Malam Ashiru da Baba Hamisu dasu Saifuddeen d'in suna zama dan akwai masu zuwa gaisuwa. Bayan sallan azahar ne duk suna zaune a gindin bishiyar limis dake harabar massalacin k'ofar gidan nasu, wasu maza su uku sukazo wanda kusan abokan Abban ne bayan sun gaisa ne d'aya daga cikinsu ya zurawa Saifuddeen idanu yana kallonshi ido cikin ido, shi kuwa Saifuddeen bai kauda idanshi bane dan ganin mutumin yana jujjuya kai alamun zaiyi mgn to sanin in ba kallon bakinshi yakeyi ba bazai gane abinda yake fad'anba shiyasa ya tsurawa mutumin ido, shi kuwa mutumin cikin jujjuya kai yace. "Allah sarki duniya mutuwa bata zabi, Allah bai barin wani dan wani yaji dad'i." sai ya kuma kalli su Bappa da Malam Ashiru da suke jinjina kai sannan ya meda hankalin shi ga Saifuddeen tare da cewa. "Da ana bawa mutuwa zab'i ai da an bata zab'i ta d'auke wannan nakasasshen ta bar Nuruddeen da shike kula da rayuwar k'annenshi." da sauri su Bappa Ali suka zaro ido tare da cewa. "Subahanallahi Mala Bala wannan wanne irin mugun furuci ne?." kai jinjina musu tare da jaddada musu cikin rashin iya mgna yace. "A ai gsky ne Malam Ashiru shi wannan dame zai amfani kanshi ma bare ya amfami wasu, yaron dashi da dutse bashi da banbanci ai su Rahma sun tagaira da mutuwa ta d'auke Nuruddeen ya bar musu mara amfani, ko su da kansu ai zasuce da mutuwar ta had'a uban nasu dashi wannan kurman ta yashe su ta bar musu Nuruddeen." cikin tsananin b'acin rai Malam Ashiru yace. "Kai tafi daga nan gaisuwa kazo ko cin zarafi?." Bappa Ali kuwa ya gaza cewa komai sai idanu ya zubawa Saifuddeen wanda ya rumtse idanunshi da tsananin k'arfi dan azabar b'acin ran kalaman da Mala Bala ya mishi gashi abokin mahaifinshi ne ba daman ya mishi wani abun. Sauran abokansu biyun da suka zo tare da Mala balanne suka mik'e cikin jin haushin kalamanshi suka sallami su bappa Ali tare da basu hak'uri sannan suka tafi. A daran wannan ranar Saifuddeen yayi kukanda bai tab'a yiba, inda yake ganin inama shi mutuwar ta d'auke ta bar Ya Nuruddeen d'inshi a ranar mutuwar ta dawo mishi sabuwa a ranshi, tausayinsu Rahma da Ummi ya hanashi sukuni ya zaiyi ya kula da rayuwarsu? haka dai kwanaki sukayi ta tafiya Randa akayi sadakan bakyai duk yan uwa suka watse gida ya rage su kadai. Hakan yasa suka zauna sukayi ta kuka. Washe gari da safe duk suna tsakiyar gidan time to time in Ummi ta kallesu sai tayi ta zubda hawaye. ganin haka duk sai jikinsu yayi sanyi, Rahma kam tuni kuka takeyi dan ita kam rayuwa ta mata zafi ba miji ba uba ba yayansu jigonsu, wanda suke ganin zai zama gatan nasu kuma gashi kurmane. jin kukan Rahma yasa Ummi tsananta kukanta, shi kuwa Saifuddeen idanu ya rumtse sabida ba abinda yafi tsana a duniya kamar yaga hawayen Umminshi, Raihana kuwa ruggume Hayatuddeen tayi tana kuka Raliyya kuwa su Faruq ta ruggume. Suna cikin haka sukaji sallama, cikin sauri Ummi ta d'ago kanta jin muryar Bappanta k'anin babanta da Goggonta, sai matar Bappan nata iya bukku muguwar mace, shiyasa Ummi take rayuwa tamkar bata da dangin Uba. da sauri ta taso ta nufi Goggonta, kan taburma suka zube nan raunin Ummi ya tashi ganin danginta kife kanta tayi kan cinyar Goggo Rabinta d'in ta saki wani marayan kuka. itama Goggo Rabi kukan takeyi dan tausayawa d'iyar yayanta. hakama Bappa idintan shima kukan yakeyi dan tausayawa rayuwar Ummi da yaranta, ita kuwa Iya Bukku sai wani mugun kallo na rashin imani take bin su Rahma dashi. Yayinda shi kuwa Saifuddeen ita ya zubawa idanu ganin mugun kallom data juyo tana yiwa Ummimshi. cikin tausayawa Goggo Rabi ta d'ago Ummi cikin sanyin murya tace. "Kiyi hak'uri Bisije dukkan tsanani yana tare da sauk'i, ki dena musu kuka Allah yana sane dake da marayunki." murya a disashe Ummi tace. "Goggo Rabi ya zanyi ina zan shiga a duniyar nan inji dad'i wa zai rik'e min yarayuna wazai tallafawa maraicina dana yarana da marayun jikokina?". sai ta kuma juyowa ta kalli Bappa idin nata cikin rawan murya tace. "Bappa ya zanyi wa zai zama gatanmu wa zai zama garkuwarmu, tunda shima bappan su Rahma ba wadata yakeda shiba, sana'ar me zanyi in rik'e yarana?." kafin Bappa idin yayi mgna tuni iya bukku ta cab'e mgnar da cewa. "Wannan kurman d'an naki mai kama da dutse shi baida amfanin komai ne?." sai ta kuma tsuke fuska dan bata son bappa idi yace zai d'aukesu su koma garinsu dasu, da sauri ta kauda kanta lokacin da ta kalli Saifuddeen sabida wani irin mugun kallo daya watsa mata. sai kuma ta tsuke fuska kana taci gaba da cewa. "In dai bazai amfanekiba ai sai ku jefar dashi ku huta da ciyar da mai zubin mutanen b'oye yaro tun yana k'arami ni tsoro yake bani dan wannan kyawun nashi ya zarta na mutanen mu. in kuma bazaki iyaba, tunda ke jakar 'ya'yace akan yaranki zaki mutu, to sai ki shiga cikin gari kije gidajen masu kud'i kina musu share-share da wanke-wanke da girki, suna baki dubu 6 a wata kullum kuma kina kwatsawa zugan yaran naki tuwo, nasan harda k'anzo zasuke baki." wani irin mugun kallo da tsana Saifuddeen yake cilla mata, domin tunda yake a duniya bai tab'a jin mgnar da tai mishi zafi kamar wannarba, kana bai taba jin mutun mai munanan kalamaiba kamar iya Bukku ba. Goggo Rabi kuwa kai ta rink'a jujjuyawa alamar batajin dad'in kalaman da matar yayan nata takewa d'iyar yayanta marigayi. Bappa idi kuwa sunkuyar da kanshi yayi dan yasan motsi kad'an zaiyi iya Bukku zata solleshi. Raihana ce ta share hawayenta tare da murgud'a mata baki kana tace. "Allah ya kiyaye Umminmu tayi ai katau a gidajen wasu, kuma Hamma Saifunmu ba k'aton banza bane kurwarshi kur sai dai kici kanki wlh yafi k'arfinki, har zakice mishi baida amfani to in sha Allah aniyarki

Table of Contents

Chapters

148 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148