Skip to content

Chapter 10

Chapter 10

Nakasa Ba Kasawa Bace Book One Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
Download Book

zai biya miki buk'atunki ba gajiyawa bare gori. Ummi kiyi min addu'a ki sanya min al'barla in sha Allah ni d'innan zan cidaku in kuaa shayardaku in jinyaceku in suturtaku." ita kam Ummi ta kasa cewa komai sai ido ta zuba mishi domin yana tsugune sai rubutu yakeyi in inda yake ya cika kana sai yaja baya yanayi jikinshi na rawa cikin zubda hawaye taci gaba da bin rubutun da yakeyi tana karantawa. "Ummi rabuwarmu dasu shiyafi al'khairi domin muddin tana zuwa tana fad'i mana mugayen kalamai wata rana zan karya mata wuya, Ummi na karkiji tsoro in sha Allah k'annena bazasuyi karuwanciba ni kuma bazanyi baraba bare maula, kema bazakiyi aikatauba, ki kalleni ki gaya min dukkan matsalarki kiyi shawara dani ko k'annena kada ki gayawa kowa matsalarki ki sirranta matsalarki damu yaranki. Insha Allah zan fara neman sana'ar yi dan rik'eku ke dai ki samin al'barka." Rahma kam sai hawayenta take shartewa, su Raihana kuwa sai binshi suke suna karanta abinda yake rubutawan. Ita kuwa Ummi da sauri ta isa inda yake hannunta tasa tsakiyar kanshi cikin k'arfin hali tace. "Ya Allah kayiwa wannan bawa naka Saifuddeen al'barka ya Allah ka yalwata mishi samunshi hagu da dama rabbi ka al'barkaci duk abinda ya tab'a ya wahidun k'ahhar ka bud'a mishi k'ofofin samu gabas da yamma kudu da arewa. Ya Allah ka kauda asara da gafala da tab'ewa daga gareshi dashi dama dukkan yan uwa musulmai, ya rabbil izzati ka al'barkaci rayuwar Saifuddeen ka raya minshi ka shirya minshi ka bashi arzik'i mai al'barka wanda musulmai da musulunci zasu al'fahari dashi ya ka bud'a mishi k'ofofin samu ka yalwata arzik'inshi." kasan cewar tunda ta dafa kanshi ya d'ago kai ya kalleta shiyasa yake gane abinda take cewa, yana kallonta still yatsarshi na k'asa yana. Rubuta "Amin Amin Ameeen ya rabbil izzati". daga nan suka zauna tayi ta musu nasiha mai ratsa jiki. Bappa Ali kuwa da matarshi suna side d'insu sam basu san meya faruba. A daren ranar Saifuddeen yaje ya samu Bappa Ali da fefanshi da biro, nan yake neman izinin bappan nashi da kuma shawarshi cewa. A d'auki machine d'in Nuruddeen a bawa wani d'an mak'ocinsu Salisu wanda shima d'an acaba ne to dama na haya yake karba, to kuma an karb'e machine d'in wai mai ita zai saidata ya cikata ya sai sabuwa, ba musu bappa Ali ya yarda dan yasan ko ba komai balance d'in zai taimakesu, shi kuwa Saifudden gyara zamanshi yayi kana ya rubutawa bappan nashi cewa. Kullum da safe in Salisu zai tafi zai bishi su tafi tare, in yaje zai shiga cikin kasuwan Gombe zai nemi sa'ar da zaiyi." da fari Bappa Ali yak'i kasan cewar yanaga Saifuddeen d'in kurma ne, to amman da suka dunguzuma sukaje wurin Ummi sai ta kauda kai yadda Saifuddeen d'in bazai ga bakintaba tace. "Ba matsala Ali barshi yaje, in mun hanashi zaiga ko dan yanada nakasane, mukuma bamu son hakan to amman ai kasuwa saida jari, amman tunda yace a barshi yaje,to mu barshin in yaje yaga ba abinda zai ai zai bar zuwa, mu kuma bishi da addu'a Allah ya taimaka mishi." cikin sanyi bappa Ali yace. "To shake nan ba matsala Allah ya bashi sa'a." "Amin Amin." sukace baki d'aya. Daga part d'in Ummi woje suka fita, sukako yi sa'an samun Salisu a harabar matsallacin k'ofar gidan nasu. Nan bappa Ali ya mishi bayanin yadda sukayi, aiko dad'i kamar ya kashe Salisu, ya kuma yarda da shared'in zaike zuwa da Saifuddeen su kuma dawo tare. A take bappa Ali ya bashi Key d'in machine d'in. sannan ya wuce cikin sangayarsu ya fara ratsa tsakiyar d'aliban nasu. shi kuwa Saifuddeen gida ya koma ya sanarwa Ummi yadda sukayi, ita ko Ummi sai addu'a da samishi al'barka takeyi. A daren ranar Ummi da Rahma da Raihana da Bappa Ali kusan kwana sukayi sunayi mishi addu'ar samun madafa da sa'a. Shi kam Saifuddeen baiyi bacci a ranar bare ya rumtsa, Kwana yayi yana neman yardar Allah da sanya al'barkanshi ya bashi sa'a a cikin k'udurin da yayi. Washe gari da sanyin safiya Saifuddeen ya shirya bayan ya karya Salisu ya shigo yace su tafi. gaban Ummi ya tsuguna kanshi ta dafa tare da sa mishi al'barka. sannan su Rahma suka mishi addu'a baki d'ayansu kana suka fita suka tafi. Suna shiga Gombe Salisu ya wuce dashi k'aramar kasuwa, gab da San Hussen mall ya ajiyeshi, kamar yadda sukayi tun jiya da dare, bayan ya sauk'ane Salisu ya kalleshi tare da cewa. "Ana yin sallan magrib kazo ka tsaya a nan, dan zanzo in d'aukeka mu tafi in munyi sa'a bayan isha mun isa Dukku." cikin nuna alamar ya gane ya gyad'a mishi kai alamar toh. Salisu na ganin haka yaja machine inshi gaban wata yar budurwa data tsaidashi, lokaci d'aya suka shirya kud'in da zata bashi kana ta hau yaja ya tafi. Shi kuwa Saifuddeen juyowa yayi ya zubawa makeken wurin San Hussain d'in idanu a lokacin tun forkon-forkon bud'eshi kana wurin ba'a wani gyarashi sosaiba kamar yanzu ba, ajiyan zuciya yayi lokacin daya karanta sunan wurin, sai kuma ya k'auda kai kana yayi tafiya kad'an yazo dai-dai mashigar kasuwan, inda zai bulla ta babban layin na k'aramar kasuwan. ida nunshi ya lumshe kana ya bud'esu a hankali hannunshi ya had'e wuri d'aya kana ya fara karanto addu'o'i yayi kusan 16 minutes yana addu'o'in kana ya shafa a fuskarshi kasan cewar da d'an sanyin safiya ne wurin bai cika jama sosaiba kuma kowa sauri yake ya wuce ya isa wurin sana'arshi ya bud'e. bayan ya shafa addu'ar ne yayi bisimillah tare da d'ago k'afarshi ta dama ya shiga cikin kasuwan. Sannan ya mik'e gabanshi samb'et, yana tafiya a hankali. har yazo dai-dai wani babban shagon seye da sayarwa inda mata keta shiga da fita irin masu zuwar sassafen nan shagon kuma cike yake mak'il da atampopi, shadda, laces, material, voyels, su wagbari, gyalulluka. da dai sauransu, ido ya zubawa yaran shagon kowa na hidiman gabanshi. a hankali ya kalli saman shagon inda yaga an rubuta. Alhj Ishaq, murmushi yayi dan sunan mai shagon ya tuno mishi sunan abokinshi wanda kusan sau biyu kenan yana zuwa Dukku bayan Abba ya rasu. juyawa yayi d'aya sashin inda yaga wani k'aton shagon mai cike da gyalulluka da dogayen riguna, kana ya kalli d'aya sashin inda yaga k'aton shagon saida takalma, sai kuma kusa da inda yake shagon masu saida yadin hijabai ne da masu d'in kasu. shiru yayi sai ya kuma ci gaba da tafiya ganin ya b'ata kusan 30 minutes a wurin. A hankali yake taku har ya isa konan shagunan alhaji Yawale, shiga yayi nanma ya dad'e a tsaye sai kuma yayi baya ganin kusan irin kayayyakin wancan shagon ne daya wuce, kan babban layin ya dawo kana yaci gaba da tafiya, Dai-dai shagunan ba mishkila ya tsaya yana kallon yadda mutane ke cike a wurin mazansu da matansu yara da k'anana, ido ya d'an zubawa yaran shagon ganin kowa da abinda yake aunarwa kuma awu mai kyau irin awunda musulunci ya yarda dashi, sunan shagon ya kalla sai kuma yayi murmushi ganin sunan shagunan ba mishkila a ranshi yace. "Eh tabbas kam ba mishkila." A takaice dai a wanan ranar kam kusan aikin daya wuni

Table of Contents

Chapters

148 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148