Chapter 114
Chapter 114
bayyana zallan damuwan da take ciki tace "Yazanyi Zakariyya? Yazanyi da soyayyarsa? inajin zafi acikin ƙirji da zuciyata, inajin idan bansamesa ba bazan taɓa samun cikar farin ciki ba, Ina sonsa! Ina matuƙar son sa!!". Ta ƙare maganar hawaye suna me gangara akan ƙuncinta. Ajiyar zuciya Zakariyya ya sauƙe, duk da cewa shi yarone sannan baisan komai agame da soyayyaba, amma tabbas yaji ajikinsa cewa ƴar uwar tasa tana cikin wani hali, cikin son kwantar mata da hankali yace. "Kiyi haƙuri Adda Zaleeha Insha Allah Zaki gansa, kuma shida kansa zai zo ya furta miki kalman Soyayya, nasan shima yanacan yanata tunaninki, yana kuma taso ya ganki, nasan shima yana can yana kuka akanki, yana cewa wayyo Zaleeha na, idan bake ba zan faɗa rijiya!". Duk da cewa tana cikin halin damuwa sosai maganan Zakariyya ya bata dariya wanda har batasan sanda tayi ɗan murmushi ba, wani irin sanyi kalaman ƙanin nata suka sanya mata azuciya, cikin jin daɗin ganin murmushin Yayartasa yace . "Yauwa ko kefa Adda Zaleeha kinsan idan kina dariya ƙara kyau kike, sannan kuma idan kina dariya maza suna ganinki kamar tauraruwa ne, to waima wayeshi da zaice tunanin ƴar uwata bai kama masa zuciya ba? dagaske nake kiyarda dani shima yanacan yanata tunaninki, harma da inda zai sake ganinki, wataƙila ma yanacan soyayyarki ta kwantar dashi jinya, wata ƙilama baya iya bacci saboda ke, burinsa kawai shine ganinki, tabbas zaki ganshi zakuma ku haɗu nan bada jimawa ba, sannan har ƙasa zai tsugunna miki yace, wayyo Zaleeha na kibani soyayyarki dan Allah!!". Yanzu kam dariya sosai Zaliha keyi inda har fararen haƙwaranta saida suka bayyana, wani irin farin cikine ya lulluɓeta, jin kalaman ƙanin nata takeyi tamkar dagaske, ganin tana dariya ne yasanya Zakariyya ɓare chocolate ɗaya yakai bakinta cikin kulawa yace. "Yauwa to kici chocolate ɗinki, kuma kiyi farin ciki yananan yana zuwa Insha Allah!". Babu musu ta amshi chocolate ɗin taci, wani irin sanyin daɗi takeji azuciyarta. Wani dogon tsuka sukaji yafito daga bayansu hakan yasasu waiwayawa da sauri, Mama dake tsaye tun ɗazu gaba ɗaya taji kome suka tattauna, harara ta watso musu su duka biyun cikin takaici tace. "Ae dama batun yauba nasan cewa daga ke har Zakariyyan baƙananan shashashai bane, kina kuka harkina cewa bazakiyi farin ciki ba idan babu wani wanda baimasan kinayi ba, wataƙila ma yanacan duniyarsu ta aljanu, waya sani ma ko yashiga jikin wata anƙonesa da ayar Allah zuwa yanzu babuma labarinsa, Wallahi Zaleeha kidawo cikin hankali da nutsuwarki, nagama fahimtar cewa tunaninki ne ke neman gushewa, saboda haka ko kinaso ko bakyaso Abdussalam shine wanda zai zamo miji agareki, kai kuma kada ka sake nasake dawowa cikin falonnan na iske ka azaune, baka da aiki sai hauka, har wai kana kwaɗaita mata cewa zaizo gareta". Ƙwafa tayi tare da juyawa ta koma ɗaki. Fuska Zaliha ta kwaɓe tare da duban Zakariyya, murmushi Zakariyya yayi mata tare da yin ƙasa da murya cikin kulawa yace. "Kar maganan Mama ya dameki, ae dai bakyason Abdussalam ko?". Kamar ƙaramar yarinya haka ta kaɗa masa kai alamar "Eh". Murmushi yayi tare da cewa "Insha Allah Bazaki auresa ba, wanda kikeso shi zaki aura, kuma zaizo kamar yanda na faɗa miki, sannan baki dace da kowa ba saishi shi kaɗai!" Murmushi tayi tare da lumshe idanunta, sosai tasamu gamsuwa acikin kalaman ƙanin nata, hannunta yakama tare da cewa takoma ɗakinta, anjima zaizo su buga game a laptop ɗinta, bata musa shiba ta tattare kayan snacks ɗinta inda Zakariyya ya ɗauki cake guda ɗaya, haka ya fita yanaci itakuwa ɗakinta ta wuce tana mejin sauƙin damuwarta, don acikin kashi ɗari yanzu babu kashi 80.. Su Saifuddeen kuwa ƙarfe 7:30 pm dai-dai suka shigo cikin garin Gombe, kamar yanda Ummi ta buƙaci da Ishaq yadawo, baiyi ƙasa aguiwaba wajen biyo Saifuddeen suka dawo gidan, Raliya ce ta cika musu gaba da kayan ciye ciye inda Ummi da kanta ta dafa musu fried rice mai rai da lafiya wanda yaji haɗin kayan lambu da hanta, gefe guda kuwa hadda haɗaɗɗen coslow wanda yaji madara da bama tayi musu, dayake Saifuddeen bawani maicin abinci sosai bane hakan yasa baiwani ci da yawa ba, Ishaq ne kam yaci sosai, don dama yana matuƙar son fried rice sosai, koda suka kammala hira ne ta ɓarke tsakanin Ishaq da Ummi inda sukayi hira sosai, har dare yayi sosai batare da sun ankara ba, ƙarfe 11 Ishaq yatashi daniyar tafiya, nan Saifuddeen yakafe kai da fata akan cewa dole lallai saidai ya kwana idan yaso gobe sai ya koma gida, Ummi ce tasa baki anan cewa Ishaq ɗin ya kwana kawai tunda dare yayi, hakan kuwa akayi ranan agidan Ishaq ya kwana tare da Saifuddeen, haka yasha baccinsa yayinda yabar Saifuddeen nata faman juyi, sam yakasa bacci sakamakon wata irin fitinannennen tunaninta da ta addabesa, haka yayita faman juyi akan gadon da ƙyar bacci ɓarawo ya iya ɗaukarsa, ko acikin baccin haka yadinga mafarkai kala kala da Zaleeha, wacce gaba ɗaya ta riƙe masa zuciya. Washe gari. Kamar yanda su Baffa Ali suka alƙawarta masa hakance takasance don ƙarfe takwas dai-dai sai gasu acikin garin Gombe, tarba ta mutumci Ummi tayi musu, inda aranta take me mamakin ganinsu, bayan sun gama gaisawa ne Baffa Ali ya gyara zama tare da sanar da'ita abun al'khairin dake shirin tunkararsu. Wani irin tsananin farin ciki ne yakama Ummi har batasan sanda wasu ƙwalla suka gangaro daga cikin idanunta ba, cikin jin daɗi tace. "Alhamdulillah! Allah Abun godiya, naji daɗin wannan labarin matuƙa Allah kuma yasa matarsace!". Da "Ameen ya Allah ". Su Baffa Ali suka amsa, nan suka ɗan tattauna akan batun daga bisani Ishaq yazo tare da mahaifinsa, saboda tare zasuje, dan sosai mahaifin Ishaq ɗin yasan Baba Malam, mahaifin Zaleeha kenan, dan harma yaƙirasa yasanar dashi batun zuwansu, kai tsaye suka wuce G.R.A. Atare Raliya da Hayatuddeen sukayi Wani irin Tsalle, cikin tsananin farin cikin jin kalaman Ummin nasu suka rungume juna, cike da zumuɗi Hayatuddeen yace "Yesss! Allah Nagode maka Hammana zaiyi aure zan samu Aunty!!" Itama Raliya wani irin farin cikine ya lulluɓe mata zuciya cikin jin daɗi tace. "Insha Allah auren Hamman mu sai yazama abun kwatance aduk Nigeria, zamusha shagali irin wanda wasu basu taɓa yi ba!". Hannu Hayatuddeen ya bata suka tafa cike da murna yace "Dan Allah Ummina asa lokacin bikin nan kusa!" Dariya Ummi tayi tare da cewa. "Amma kai dai Hayatuddeen Allah ya shiryeka, bafa sadaki nace maka ankai masa ba, neman izinin hirafa akaje nema masa!" Baki Hayatudden ya turo gaba tare da cewa. "Duk da haka dai, ai nasan Hammana JARUMI ne Insha Allah bazai taɓa zama LOSER ba, shi zaiyi nasara akan komai!". Murmushi kawai Ummi tayi tare da fita sha'aninsu, nan suka cigaba da murnarsu shida Raliya suna shewansu, Ummi kuwa Adda Rahama taƙira ta sanar mata, sosai Adda Rahama taji daɗin zancen na Ummi, don itama tana da burin ganin auren ƙanin nata, haka Raihana ma tacika da murna alokacin da Ummi ta sanar da'ita. Acan G.R.A kuwa su Baffa Ali sun samu isa babban gidan na Baba Malam bisa jagorancin mahaifin Ishaq, suna isa cikin gidan, Wani matashi mai kamala Ya Aminu kenan ya ƙaraso garesu, cike da girmamawa ya basu hannu suka gaisa, nan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148