Skip to content

Chapter 143

Chapter 143

Nakasa Ba Kasawa Bace Book One Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
Download Book

ruwan mamaki, in -dai-da-raina da lafiyata bazan taɓa bari ƴata Zaleeha dana haifa acikina ta auri wannan shashashan nakasashshen ba, bazan taɓa bari wannan banzan auren da suke shirin ƙullawa ya tabbata ba, Ni nan nayi al'ƙawari ƴata Zaleeha ba zata taɓa auren MUSAKI ba!!.". Murya akausashe Mama taƙare maganan domin kuwa ji take kamar zatayi aman wuta don bala'i, alwashi ne bazata taɓa bari Zaleeha ta auri Matsiyacin gurgu kuma mayataccen kurma ba, tayi al'ƙawarin saita tashi hankalin kowa dake gidan, sannan kuma sai takau da duk wani zaman lafiya dake cikin gidan matuƙar akaƙi bin zaɓinta. Cikin jin daɗin kalaman Mama Balkeesu ta saki wani ɓoyayyen killer smile, tabbas so take Mama ta jajirce wajen ganin Zaleeha bata auri Nagartaccen Namiji kamar Saifuddeen ba, tasan cewa Saifuddeen nakasashshene, amma sam ita bata hango nakasartasa, don kuwa babu wata nakasa da ta nuna ajikinsa, hasalima ita bata taɓa ganin wani nagartaccen Namiji kamar Saifuddeen ɗin ba, tahango abubuwa da yawa dangane da Saifuddeen ɗin wanda maza da yawa basu dashi, irin Saifuddeen sune mazan da suka fi ƙaranci aduniya, haka kuma irin sa mata da yawa ke fata da burin samu matsayin abokin rayuwa. Kullum haushinta d'aya kada Zaleeha ta rigata aure, kuma kada ta fita samun miji na nunawa sa'a shiyasa ta dage ta raba Manager da son Zaleeha tana ta son cusa kanta gareshi, dan Raveel dai ya nuna mata baya tare da ita, A wani sashi na ranta kuwa dadi takeji dan in zaliha ta auri nakasasshe ta samu abin nunawa mutane tawayarsa. Miƙewa tsaye tayi yayinda ta nufi ɗakin Zaleeha. Zaleeha kuwa tana shiga cikin ɗakinta, kai tsaye kan lallausan gadonta ta faɗa, cikin tsananin baƙin ciki da takaici haɗi da tsanar Saifuddeen tashiga rera kuka, tayaya zai fuskanci cewa ta tsanesa? mai yasa bazai gane irin tarin tsanar da tayi masa ba ya rabu da ita? meyasa shi baida zuciya? ta tsanesa tsana irin ta wuce misali, sam batason duk wani abu da ya shafesa, ganin fuskarsa na sawa tanajin kamar takashe kanta, meyasa har yanzu kowa ya kasa fahimtar irin raɗaɗi da kuma zafin da takeji? meyasa kowa yakasa sanin zafin ƙiyayya irin wanda takeji, mutum ɗaya takeso aduniya shi ɗaya za kuma taci gaba da so, har iya ƙarshen rayuwarta, batajin zata so wani koda kuwa kwatan kwacin rabin yanda takeson wanda yakasance mai taimako agareta, abu ɗaya tasani shine, ko duka mutanen duniya zasu taru suyi mata kallon mahaukaciya akan son da takeyi masa to bazata taɓa fasawa ba, koda kowa zai yi mata kallon shashasha, tayarda zata amince za kuma ta jure matuƙar akan soyyayarsa ne, tariga tasa aranta cewa komai wahala komai daɗi, komai kusa komai nesa zata bada kai da ƙarfinta wajen zaman jiransa, sau dayawa zuciyarta na gaya mata cewa watarana zaizo gareta, ta kuma aminta da hakan, saboda haka tasa aranta cewa, har abada bazata taɓa daina so da ƙaunarsa ba. Balkeesu ce ta turo ƙofar ɗakin ta shigo, ganin Zaleeha kwance na kuka, yasanyata taɓe baki, cikin ranta tace. "Bakiyi komai bama Zaleeha, sai alokacin da idanunki suka buɗe ki ka gane cewa kinrasa nagartaccen namiji kamarsa, daga wannan lokacin zakiyi kuka irin wanda ake ƙiransa da sunan kuka bawannan sharan fage ba, wanda ni kuwa dama hakan shine burina." Afili kuwa ƙarasawa gaban gadon tayi tare da zama abaki bakin gadon, cikin son zuga tasanya hannu ta dafa kafaɗan Zaleeahan, cikin ƙoƙarin ɓoye manufarta tace. "Kuka baya maganin damuwa Zaleeha, sam kuka bai kamaceki ba ba kuka yakamata ace kinyi ba." Afusace Zaleeha ta tashi zaune, fuska caɓa-caɓa da hawaye tace. "Bakuka yakamata nayi ba? dariya kenan kikeso nayi mai gado? okay nagane saboda ke bakisan zafin ƙiyayya dana soyayya ba ko shiyasa zakice haka, da ace kinsan yanda nakejin zafi a zuciyata wallahi da ke ce zaki fara cewa naƙara sautin kukana tayanda gaba ɗaya Nigeria zasu jiyoni bama iyaka Gombe kaɗai ba, Natsaneshi Mai gado, Natsaneshi, banason koda ganin fuskarsa, aurensa dai-dai yake da tarwatsewan zuciya da rayuwata gaba ɗaya, da ace na buɗi idona naganni matsayin matarsa gwara ace na wayi gari bana numfashi.!" Wani irin ƙatuwar ajiyar zuciya Balkeesu ta sauƙe, tabbas haƙanta gaf yake da cimma ruwa, saidai kuma har yanzu bata hango irin zazzafar tsanar da takeson Zaleeha tayiwa Saifuddeen ba, haƙiƙa komai na Zaleeha na bayyanar da tsanar Saifuddeen saidai ita har yanzu akwai abun da bata gamsu dashi ba. Cikin yin ƙasa da murya tace. "Bance kiyi dariya ba Zaleeha, ni ƙawarkice maison duk wani abun da kikeso, saboda haka burina shine ki samu wanda kikeso, kishare hawayenki Zaleeha, saikin cire tsoro haɗi da kunya kin fuskanci kowa sannanne zaki samu cikar burinki, saikin dage kin kuma ɗaga hankalin kowa dake gidannan, sannan zasu fuskanci cewa babu soyayyar Saifuddeen aranki." Ɗago jajayen idanunta wanda suke cike da ƙwalla tayi ta kalli Balkeesu, murmushi Balkeesu tayi tare da dafa shoulder ɗinta, cikin son tarwatsa nutsuwar Zaleehan tace. "Nasan kin fahimci abunda nake nufi, dole ne ki tashi tsaye wajen ganin kin samawa kanki ƴanci, wani irin kallo kike tunanin mutane zasuyi miki aduk sanda sukaji cewa da kyawunki da komai kin kashe ƙuruciyarki wajen auren nakasashshe? ki dubeki Zaleeha, kyau, ilimi, diri, hutu, wayewa, aji, sanin darajar kai, duk fa kin mallakesu, babu wani ɗa namiji da zaki gifta ta gaban idanunsa matuƙar ya amsa sunansa namiji ace baiji komai game da ke ba, sam bakiyi kama da matar nakasashshe ba, zama da nakasashshe kuwa agareki tamkar tarwatsa rayuwarki ne!." Ɗan tsagaitawa da maganan tayi tare da miƙewa tsaye, duban Zaleeha tayi da kyau, tare da sakin wani ɗan guntun murmushi, ahankali tashiga takawa harta ƙarasa jikin ƙofar fita daga ɗakin, juyowa tayi still fake smile ne ɗauke akan fuskarta, cikin son tausasa zance tace. "Nabarki lafiya ƙawata, ina fata zakiyi tunani me kyau akan maganata, idan kuma kin amince nakasashshen kurma yazamanto ango agareki am fine, mudai always zamu tayaki murna." Tana kaiwa nan azancennata ta murɗa handle ɗin ƙofar ta fice, tana sakin wani dariya mai ɗauke da tsananin mugunta. Lumshe idanu Zaleeha tayi saiga wasu sabin hawaye shaaaa sun kwaranyo daga cikin idanunta, wani zafi-zafi ɗaci-ɗaci haka takeji acikin maƙoshinta, cikin ɗaya daga cikin trow pillows ɗin dake watse bisa kan gadon ta jawo ɗaya, tare dayin hugging ɗinsa a ƙirjinta, kanta ta jingina da saman gadon tare da sake sakin wani sabon kuka, sosai shawaran Balkeesu yasamu mazauni acikin zuciyarta, don ta ƙudurta aranta cewa daga yau babu wani wanda zai ƙara bacci cikin daɗin rai acikin gidan, saita ɗaga hankalin kowa, bazata nutsa ba kuwa harsai taga ta samu abunda takeso... Ɓangaren su Saifuddeen kuwa daga gidan su Zaleeha kai tsaye wani babban Cafe dake cikin unguwar federal lowcost suka nufa, wanda ananne suka narka kuɗi don buga musu ƙawataccen katin auren nasu wanda yanzu kwana biyar ne kacal ya rage, koda sukaje tuni suka samu an gama kammala musu komai, nanfa suka amsa, daganan gidansu Ishaq suka wuce, domin kuwa musamman Ummu'n Ishaq taturowa Saifuddeen ɗin saƙon text message akan cewar tayi masa tuwon semovita miyar moringa (zogale) sanin cewa yana matuƙar son miyar, koda sukaje gidansu Ishaq ɗin nan sukaci abinci suka ƙoshi, domin kuwa harda wani irin daddaɗan coconut

Table of Contents

Chapters

148 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148