Skip to content

Chapter 21

Chapter 21

Nakasa Ba Kasawa Bace Book One Complete Hausa Novel 1,209 words 0 views Progress saved
Download Book

gefen taburmar kana ta kalli Raihana tare da cewa. "Na mance ban d'auko biredin nan ba, tashi ki kawoshi yana d'akin Ummi." to tace tare da mik'ewa ta nufi d'akin. Ita kuwa Rahma miyar ta saka a k'aramar kulan tare da tsokoki kusan shida kana tasa k'ashi biyu, sannan ta d'auki k'aramin filas d'in nan ta had'a da kulolin kana ta amshi biredi d'aya a hannun Raihana da ta iso da su a hannunta, cikin nitsuwarta tace. "Yauwa Raihana bari in kaiwa su Bappa Ali nasu ke kuma ki sa mana ki sawa d'an uwana." da yake haka take kiran Saifuddeen wasu lokutan ba musu Raihana ta tsuguna tare da fara zuba musu, shi kuwa Saifuddeen da sauri ya mik'e yaje ya amshi abincinsu bappa Alin kana yayi mata nunin da ta koma taci abinci bari shi ya kai musu. To tace mishi kana ta bashi kulolin, sannan ita kuma ta koma ta zauna kofi ta d'auka tea ta had'a mishi mai kauri ta san ba wani abinci mai yawa zai iya ciba, bayan ta had'a mishi ne sai ta kuma d'iba mishi couscous d'in tare da sa mushi miyar hantar a d'an k'aramin side soup tuni Raihana kuma ta gama had'a musu nasu a tire, ta ajewa kowa kofin tea a gabanshi. bisimillah sukayi tare da addu'a sannan suka fara sahur d'in. Shi kuwa Saifuddeen koda ya dawo tuni k'arfe hud'u ta kusa gefen Umminshi ya zauna tare da d'aukan kofin tea d'in da Rahma ta had'a mishi ya fara sha, ido ya lumshe jin k'amshin citta da kananfari da masoro da ganyen na'a-na'a, yana sha yana lumshe ido ko dan dama shi yana son tea yana nan kamar buzu, ita kuwa Ummi cikin kula tace. "Babana kaci abincin mana kanata shan ruwan zafi." ido ya zuba musu yadda suka had'u su duka sunaci a kwano d'aya sai ya tuna mishi da baya, wanda baushe ke cewa kowa ya tuna bara baiji dad'in banaba, idon ya kuma bud'ewa yana mai tunanin dah ita Ummi taci da yaranta mata shida Nuruddeen kuma tare sukeci da Abbansu da bappa Ali koda last year haka sukeyi, sai gashi bana kuna ba Abba ba Nuruddeen bappa Alinma da yake raye baizoba sabida rashin d'an uwanshi, oh mutuwa wato dama haka abin yake ta rabaka da macecce ta rabaka da rayeyye, gashi Hayatuddeen yanata baccinsa. itako Ummi kamar ta gane me yake tunawa sai ta d'an gyara zama sannan ta zare cokalin cikin abincinshi ta saka cikin tiren da sukeci tace. "To muci tare, kada kayi zurfin nazari gamu Allah ya barmaka mu gashi nanda bad'i kuma zakuyi taci da autana." ganin ta tsareshi da ido ne kuma in baiciba bazata ji dad'iba yasa ya d'anci kad'an kana ya kuma amsar kofin tea d'in da Rahma take rik'e dashi tana sha kurb'a biyu yayi kana mik'a mata sannan ya mik'e da sauri. ruwan wonka ya d'iba sannan ya shiga d'akinshi ruwan randar sanyinshi ya d'ansha kana ya d'auko soson shi da makilin da burosh. a nitse yayi wonkanshi yana fitowa ana kiran assalatu. Dama tuni su Ummi sun gama sahur d'insu har Raliyya ta tattare wurin. D'akinshi ya shiga kasan cewar yau jumma'a ace kuma azumine, shiyasa ya zaro wani tattausan yadi mai sauk'in kud'i fari k'al rigar anyi mata d'inkin zamani anyi d'an aiki da yellow zare, bayan ya gama sa kayan sunyi d'as a jikinshi sai yasa hular zannabukar mai d'an surkin yellown zare sai takalma suma farare masu d'an ratsin yellow. Sosai yayi wani irin baiyanennen kyau, wanda gani d'aya zakayi mishi kasan Allah ya masa cikar halitta da haiba, gaba d'aya alamun zarra da tsurar cikekken d'a namiji sunata baiyana a jikinshi tuni muryarshi tayi kauri alamun cikar balaga da d'an dad'ewa, gwarabanshi suna ta hab'aka yayinda duk wani sashi na jin d'an adam dake iya fidda gashi, nashi sunata yabanya, hatta gefen kunnenshi yana ta nuna alamun tsirowar saje, hakan sharabanshi da singalalin hannunshi da k'irjinshi, tuni gashin girarshi ta zama d'aya daga cikin abinda ke Jan hankalin mutane ih zuwa ga kallonshi dan gashin girarshi har had'ewa suka bisa karan hancinsa, hakama gashin idanunshi zar-zar dasu lips enshi kuwa jazir dasu ko yaushe kamar an shafa musu man baki zakaga suna shek'i sirarane sai dai sunada d'an fad'i da taushi dan ko d'an dannesu yayi da harshenshi sai kaga wani wurin ya lotso ya kuma yi fari, yana kuma janye harshenshi zakaga ya koma janshi, yatsun hannunshi da sawunshi kuwa suma kansu abin ganine. Tsayuwa yayi gaban wannan dogon madubin hannunshi rik'e da turare, feffesawa yayi a jikinshi yadda bazaiji gafinshi a mak'oshinsa ba. carbi ya d'auka kana ya fita nan ya samu Raihana ta tada Hayatuddeen da Faruq sunyi al'wala, shiyasa ya tasasu a gaba suka nufi masallacin k'ofar gidan nasu. Bayan an idar da salla su Hayatuddeen suka tafi gida shi kuma sai ya d'an zauna yayi azkar saida ya gama sannan ya mik'e ya fita a harabar tsank'ayarsu ya samu Salisu na jiranshi. Dan haka sai yayi sauri-sauri ya shiga gida a tsakar gida ya samesu duk suna ninnike hijaban da sukayi salla dasu, Ummi kuwa har yanzu carbine a hannunta gefenta ya d'an rusuna kana ya motsa lips enshi a hankali alamun. "Ina kwana?." "lfy lau Babana har zuku tafi ko?." tace dashi cikin kula kai ya gyad'a mata alamun eh, sai ya kuma gaida Adda Rahma kana su Raihana suka gaidashi, Raliyya kuwa tuni ta har-had'a kwanun wonke-wonke tana wonkewa. da sauri Ummi tace. "To Allah ya kiyaye hanya ya kaiku lfy ya dawo daku lfy." sabida jin Salisu nata danna mishi hon Amin Amin suka amsa baki d'aya kana ya mik'e ya fita. Suna isa gombe kamar kullum Salisu ya ajiyeshi kana yaja ya tafi ya fara aikinshi. Shi kuma cikin masallaci ya shiga, baccin da baibane ya dan fara fizgarshi haka yasa ya konta, cikin k'ank'anin lokaci yayi bacci. 8:00 Am ya farka da sauri ya mik'e, ya fita harabar wurin ruwa ya saya yayi al'wala sannan yazo yayi walaha, daga nan ya nufi cikin kasuwa. Yana shiga kai tsaye dilansu ya wuce yana zuwa ko yayi sa'a ba layi sosai tofa nan take aka bashi na 60k ganin bashi da wurin zubasu ne sai yace musu bari yazo, shagonsu Hisham yaje yace musu kwali yakeso nan take suka bashi yankekken kwalin Gas yana amsa yaje ya cika kwalin da lododin. Da shagon ba mishkila ya fara dan yafi kusa dashi kuma yasan me yawa zasu karb'a zasu rage mishi nauyi, yana zuwa kuma ya samu shagon a cike mak'il da masu sayan abubuwa irin su Gero, kunu gyad'a kunun wake k'osai, waken awara. Rid'i, sugar, madara, acca, al,kama, masara, maiwa, shinkafa, dawa, fulawa, da dai sauransu a k'alla yaran shagon sun kai goma amman still ga layin masu awu, d'aya daga cikin yaran shagon ne ya yafitoshi tare mik'o mishi 5k d'in jiyan kana yace. "Alhaji yace yau na 15k zaka bamu ko?." kai ya gyad'a mishi kana ya sunkuyo ya rink'a mik'o mushi faket-faket na ledodin hawa-hawa kamar dai yadda yaga Baba Bello ya basu jiya. Yana basu ya rubuta kana ya bawa yaron shima yasa hannu, daga nan ya fara bin duk shagunan da Dottijon ya nuna mishi,

Table of Contents

Chapters

148 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148