Chapter 20
Chapter 20
kuma saran ruwa. Koda Jabeer ya ganshi yai ta mishi tsiya wai shine sana'a goma mgnin baccin safe. Haka dai ranarma ya wuni saida kayan sanyinshi, saida akayi sallan isha suka kama hanyar dukku wanda tuni anga wotan Ramadan, gaba d'aya al'ummar annabi gobe za'a tashi da azumi. Kamar yadda ko wanne gida ke shirin d'aukan azumi hakama gidansu Saifuddeen domin. bayan yayi wonkane yaje ya samu Umminshi da Adda Rahma da Raihana, nan ya gayawa Umminshi lamarin kasuwar sai dai bai gaya mata ribar da Dottijon nan ya gwada mishiba don baison ya fad'ad'a burinshi kan ribar gudun kada ya shigar da son zuciya. Rahma ya kalla wacce ta kawo mishi abinci cikin sanyi tace. "Yauwa Saifuddeen wannan k'awar Raliyya Salma sun zo d'azu tace wai in gaisheka in ka dawo." ta k'arishe mgnar tana murmushi da son ganin fuskarshi dan tasan sam Saifuddeen baya shiri da Salma Shi kuwa yi yayi kamar bai gantaba bare ya gane me take fad'i dama in baya son mgna da mutun haka yakeyi. Ummi kuwa ido ta zuba musu tana murmushi, abincin ya d'an tsakura kasancewar shi baida yawan cin abinci. saida ya d'an gyara zamanshi kana ya kalli Hayatuddeen dake gefenshi tare da mishi tambayar azumi nawa zaiyi?." cikin d'oki yace. "30 zanyi ko d'aya bazan shaba." dariya Ummi tayi jin Raliyya na cewa. "Ko kuma ko d'aya bazakayi ba ko?." cikin dariya Rahma tace. "Ai kam saidai hakan." shi kuwa Saifuddeen hannun Faruq yaja tare da cemishi shi kuwa nawa zaiyi. yatsunshi uku na tsakiya ya d'aga alamun zaiyi uku da yake duk sun iya kurmanci. Raihana kuma tana tsakiyar gida tanata kiciniyar tafasa tea da yin miyar asuba, miyar dege-dege take musu dan Ummi dubu d'aya ta bada Hayatuddeen ya sayo musu hanta da jan nama, tofa shine aka gyarashi tayi miyar ganyen albasa da yaji kayan miya dana d'an-d'an dan aji dad'in yin sahur. koda ta gama tafasa tea d'in da tasa citta da kanumfari, sai ta d'ura a filas kana miyar kuma ta barshi a tukunyar sai ta dorashi saman kanta sannan taja kitchen d'in ta rufe sai da asuban Rahma zata k'arisa aikin. tana rufe kitchen d'in taje sukaci gaba da hira, nan Saifuddeen ya bawa Ummi shawarar a hana Aunty Nina girki dan tana laulayin wani cikin, to shiyasa yake son a hanata girki su had'a tukunyar, sosai Ummi taji dad'in haka dan itama taso hakan sabida tasan Bappa Ali mutum ne mai kawaici tana sane cutar mijintane ya medasu basu da wasu yawan kadarori. koda Saifuddeen ya tashi daga nan k'ofan Bappa Alin ya nufa inda ya samu Aunty Nina tana kiciniyar hura wuta a murhun gawayi yayinda shi kuma bappa Ali, yake ruggume da Qur'an alamun zai fita masallaci. nan ya gaya mishi shawarar da suka yanke shida Umminshi. bawan Allah Bappa Ali sai yake jin kunyar wai shi ya kamata yaci dasu ya gaza sai kuma shima su ciyar dashi, da fari kamar bazai yardaba to dole dai ya yarda dan Saifuddeen ya kafa ya tsare haka ya hak'uri, sannan suka kama zance tafsir d'in da zasu fara gobe ya jaddawa Saifuddeen ya shirya dashi za'ake zuwa bayan sun gama mgnane ya fita wurin abokanshi. Salisu ya samu da Mudasir sai Warisu ganin Saminu baya nanne yasa suka raja'a gidan sarki gidansu Saminun kenan, a d'akin saminu suka yada zongo sunata hira, har dai dare ya fara nisa kafin suka fito, Warisu ya shiga gidansu shima Mudassir yayi hanyar gidansu. Saifuddeen kuma da Salisu tare suke tafiya dan kusan katangar gidansu d'aya ne. suna isa bakin masallaci Saifuddeen ya zaro biro kana yayi rubutu a jikin takardar daya b'alla. "Yauwa Salisu dama inaso in gaya maka an rage balance enka ka rink'a bada dubu biyu duk sati, sai mu rink'a tasowa biyar dai-dai na yamma kafin a kira magrib kuma mun iso dukku kaga zamuyi bud'a baki a gida kuma zamu dena tafiyan dare, in kuma gari ya waye in yaso ana fitowa masallaci mu tafi tunda ba batun jiran karyawa." cikin tsananin jin dad'i Salisu ya ruggumeshi tare da cewa. "Kai Alhamdulillahi wlh ka kawo shawara mai kyau, amman dubu biyu yayi kad'an gsky zan dai bada 4k tunda du-du du dai awa d'aya da rabine aka rage. Ngd matuk'a Allah bar zumunci da k'auna my friend." cikin sanin mutuncin juna ya kuma ce mishi. "No kai dai kabar 2k d'in ai kaima kanada buk'atun kanka dana iyayenmu." cikin sanin ya kamata Salisu yace. "To naji na kuma gode, amman gsky 3k zanke badawa kada ka cemin komai." jin haka yasa Saifuddeen rubuta. "To Allah ya musu al'barka." da haka sukayi sallama, Koda ya shiga gida tuni su Ummi sunyi bacci acewarsu kada suyi dogon hira su zo su makara. Shima hakance a wurinshi shiyasa yanayin wonka yayi al'wala yazo yayi konciyarshi. 2:00 Am Ummi ta farka kamar yadda Ummi takeyi ko wanne lokaci in dai cikin Ramadan ne, kana ta bud'e k'ofa ta fito tsakar gida yayinda iska mai sanyi ke kad'awa, babbar taburma ta shimfid'a kana ta fito da wani d'an madaidaicin cainis carpet amman irin na da fa, ta shimfid'a bisa taburmar kana ta ajiye hijabinta da carbinta da Qur'an sai lantanta mai wadaceccen haske. al'wala tayi kana kana taje baki k'ofar d'akinsu Rahma kira d'aya ana biyu Rahma ta amsa. Itako Ummi tana jin Rahma ta amsa ta koma bisa taburmar ta fara nafila, Rahma kuwa tana tashi ta tada Raihana Raliyya. sun jima kafin suka tashi, suna fitowa duk sukayi al'wala kamar yadda aka sabar musu tun basu kai hakaba, kana sukazo ko wacce tayi iya nafilar da zata iya daga bisani suka fara karatun Qur'an. Yayinda tuni Saifuddeen ma ya tashi yazo ya tashi Hayatuddeen sun je bakin k'ofar d'akinshi bisa k'aramar taburma ya shimfid'a musu sallaya, suka fara nafila bayan sun zauna sun fara tilawa ne ba jimawa Hayatuddeen ya fara gyangyad'i yana rab'awa jikin Hamma Saifuddeen d'in nashi tuni bacci ya sureshi shiko Saifuddeen gyara mishi jinginar yayi kana yaci gaba da tilawarshi. 3:20 Am Rahma tayi addu'a tare da shafawa kana ta mik'e ta cire hijabinta ta ninke ta ajiye gefe sannan ta shiga kitchen ruwan zafi ta d'ora bayan ya tafasa ne ta d'an zuba man gyad'a cikinshi kana ta d'ebo couscous dai-dai misali tazo ta zuba kana ta meda marfin ta rufe, sanan ta harhad'a kofuna tare da pilet da cokula, ta fitar taje ta jera bisa babbar taburmar, kana ta dawo ta d'auki filas d'in duka biyu babban da k'aramin, sannan ta koma kitchen d'in, bud'e tukunyar tayi tare da duba couscous d'in yayi lugub yadda akeso kuma yayi wasar-wasar bai kwab'e ba amfanin zuba man gyad'an kenan, sauk'e tukunyar tayi ta ajeshi gefe sannan ta mik'e ta sauk'o dana miyar ta d'orashi kan rushin. sai ta kuma sauk'o da kuloli guda biyu d'an madaidaci shi ta fara zubawa saida ta cikashi yadda zai iya isar mutun ukuma, kana ta kwashe sauran duka a babbar kulan, sannan ta kwashi kulolin ta kaisu bisa taburmar, tana dawowa ta bud'e tukunyar miyar da sai bol-bol yakeyi sai mai da tsokokin da suka yiwa miyar k'awanya, tukunyar ta d'auka baki d'aya kana ta d'auki d'an k'aramin kulan miyar, tana fitowa ta zauna
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148