Chapter 50
Chapter 50
gaba da cewa. "Bari in d'auki jakar kud'in nan inzo mu tafi, amman sai mun biya ta GT bank na ajiye kud'in sai mu wuce ko?." kai ya gyad'a mishi alamar to. A tare suka foto bakin shagon inda kasiyar Ahmad take, shi ya fara hawa kafin Saifuddeen ya hau kana yaja suka tafi, kai tsaye GT Bank suka nufa, tare suka shiga bayan sun gama hidimarsu suka fito nan suka kama layin bello sabon kud'i inda jerin kafintocin jihar gombe suke cike birjic, suna isa wurin kafintan suka samu an gama komai an kimtsasu an lik'esu cikin leda, suna isa Babban kafintan ya kira biyu daga cikin direbobin motocinsu na kwasar kaya ih zuwa gidanjen costumes d'insu, sukazo suka kwashi kayan aka loda a motocin, sannan matasa uku suka shiga wanda su zasuyi jeren, suna gaba motocin na binsu a baya, suna isa Ahmad ya sauk'a ya karb'i key d'in gidan a hannun Saifuddeen sannan ya bud'e musu gate d'in yazo ya shiga suma sukabi bayansu. Daga nan suka fara shisshigar da kayan suna shigarwa cikin can asalin cikin gidan. Ahmad ke musu bayanin yadda zasu sassaka kayan dan su basa gane body language d'in da Saifuddeen zai musu, Bedroom guda biyu dake cikin parlour dake k'asan suka fara kimtsawa suka kafa gadajen tare da durowowin da mirrors d'in, sannan suka sassaka katifun, sai kuma suka dawo cikin parlour suka kimtsa lumtsuma-lumtsuman kujerun masu kama da kiran royal sai dinning table mai azabar kyau da suka shiryashi a dinning area, sai da suka gama kimtsa parlour sannan suka shiga d'aya kofar da zata sadasu da d'an karamin parlour da bedroom nan gado durowar suka kafa, parlour kuma suka barshi ba komai, sai kuma suka haura sama can suna shiga parlour bedroom d'in dake hannun dama suka shiga nan suka kafa gado da durowa da duk sauran kayan gado sannan suka dawo falon nan suka samu Ahmad ya firfito musu da sauran kayayyakin da suka saya suka tara a d'aya bedroom d'in kamarsu cainis carpet da labulaye sai zannuwan gadaye da TV, Firij da dai sauran kayan wuta. daga parlour saman suka fara saka labulayen masu azabar kyau da shek'i kalarsu pink and white, hakama kujerun da carpet d'in. bedroom d'in da suka kafa gado suka shiga nanma suka sa labulayen masu kalar ja da fari, zanin gado ma red and white sai carpet shima red and white, suka gama kimtsa komai sannan suka dawo parlour suka ajiye d'an madaidaicin firij a cikin dinning area wanda shi bai samu damar samun dinnin table ba, sai katon TV da suka manna a parlour, daga nan suka sauk'o k'asa suka gama shirya koma inda kalan labule da carpet suke white and people. sai tv da firij da suka ajiye komai a mazauninshi, sai kuma suka shiga d'an k'aramin parlour nan suka malale tattausan carpet a tsakiyar parlour sannan suka lik'a tv a jikin bongo, daga nan suka ajiye d'an k'ank'anin firij a parlour. Daga nan kuma suka shiga cikin kitchen d'in suka shirya durowowin kitchen d'in na sama da k'asa sannan suka ciccibo kwalin gas suka zo suka sashi a mazauninshi sannan suka had'a ma sank'alin sink da bakin pompo sosai kitchen din yayi kyau. Sosai gidan yayi kyau komai yayi ras, daga nan Saifuddeen ya biyasu kud'in aikinsu kana ya sallamesu, sannan suka dawo parlour suka zauna shida Ahmad bisa kujerun suka zube suna shak'ar k'amshin sabon fenti da k'amshin sabbin kayan d'aki inda ya had'e ya zama daddad'an k'amshi, Ahmad ne yayi mik'a tare da cewa. "Masha Allah gida yayi kyau sosai, sai dai nasan Hayatuddeen zaiyi mitar an sa mishi k'aramin tv a d'an k'aramin parlour shi." murmushi Saifudddeen yayi tare yin alamun. "Ai zaiyi fushi kam dan zaice ban sa mishi kujeru a parlournba." dariya Ahmad yayi tare da zaro wayarshi daketa ringing da sauri ya d'aga ganin Salisu ke kiranshi. "Hello Salisu ya kake." "Lfy lau Ahmad ya kasuwa?." "Alhamdulillahi ya naka kasuwan?." "Lfy lau wlh, ina kake ne nazo shagonku ban sameka ba." gyara konciyarshi yayi tare da cewa. "Muna gidan Saifuddeen d'azu nai ta kiranka baka picking call." Numfashi Salisu ya fesar tare da cewa. "To gani nan zuwa ku jirani." "To sai ka zo." cewar Ahmad har zai katse kiran sai kuma yace. "Kana inane yanzun?." "Ina nan cikin shagonku." "Yauwa to d'an taho mana da abin sanyi, sannan ka d'an biya ta tashan dukku ka biya Abba bekery ka sama mana abinda zamuci dan wlh ni yunwa nakeji." Dariya Salisu yayi sannan yace. "To ba matsala a cici, ci ba k'iba asaran gaya kawai." yana fad'in haka ya katse kiran, sannan ya juya ya kalli Mudassir dake dariya dan yana jiyo mgnar Ahmad kad'an-kad'an , sai ya kuma nuna Warisu da idanu yace. "Nida Ahmad ci kamar gara, amman bama k'iba, ga oga Warisu kuwa yanata yiwa kanshi k'aidar ci amman a banza sai zuba k'iba yakeyi." hararanshi Warisu yayi tare da cewa. "Kada ka damu yaro nima zan sace." dariya sukayi baki d'aya, sannan Salisu yace. "Yauwa ina son shinkafa buhu biyu d'anya da gumi sai buhun semo, da katon d'in spaghetti and macaroni indomi. d'ad'd'aya Sai kuma mai manja magi sugar fulawa. Bello ne dake tsaye ta woje yace. "To an gama Warisu had'a mishi lissafin kud'in da zai bada." to Warisu yace kana ya jawo Calculator dake gabanshi ya fara had'a lissafin, yayinda tuni shi kuwa Bello ya had'a kayan duka, sannan Warisu ya fad'i lissafin nan take ya biya kud'in sannan ya kira 'yan baro guda biyu suka kwashi kayan suka fita Salisu na biye dasu a baya. Suna zuwa inda yayi parking motarshi ya bud'e but d'in motar kana ya loda kayan daga nan ya sallami yaran suka tafi shi kuma ya shiga mota yaja ya tafi direct Abba Bakery ya nufa ya sai musu abinda zasuci kana ya shiga cikin federal law cos, Yana isa ya kira Ahmad yazo ya bud'e mishi gate sanan ya shiga da motar, daga nan ya bud'e but d'in motar suka fara jidan kayayyakin sukayi ta shigarwa cikin sito d'in parlour da aka gyara. Sosai Ahmad yaji dad'in kawaicin da Salisu yayiwa Saifuddeen, shima kanshi Saifuddeen mutuncin Salisu ya k'aru a ida nunshi duk da bashi da matsalar kayan abinci amman yaji dad'in kyautar. Nan sukaci suka sha sai bayan sallan la'asar suka fito, suna fitowa gidan Alhaji Kabiru suka shiga nan sukayi sa'an samunshi a harabar gidanshi yana shirin fita, bayan sun gaisane yacewa Saifuddeen. "Ya kamata ka samu mai gad'in da zai zauna a gidan dan barin gidan haka ba mai gadi baiyiba." kai Saifuddeen ya gyad'a mishi alamun za'ayi hakan. shi kuwa Alhaji Kabiru buzayen dake zaune can harabar gidanshi ya nuna musu wani d'an ma daidaicin dottijo dake tsakaninsu kana yace. "Ga wannan dottijon yanada kirki dama shine a gidan kauran masu gidan ne yasa nace ya dawo nan kafin a samu mai d'aukanshi aiki." cikin gamsuwa Ahmad yace. "To shike nan ba matsala kawai ya koma can yaci gaba da aikinshi." cikin jin dad'in nitsuwar yaran Alhaji Kabiru yayi musu bayanin kud'in da ake biyanshi sun amince da za'a biyashi hakan, nan take ya kwashi kayanshi ya koma gidan akan za'a rink'a bashi abinci daga gidan Alhaji
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148