Skip to content

Chapter 52

Chapter 52

Nakasa Ba Kasawa Bace Book One Complete Hausa Novel 1,208 words 0 views Progress saved
Download Book

dan Allah ki rage idanunki." sai ya kuma kalli yayar tashi cikin tsigar tsokana yace. "Ke ashe ga wacca ta b'ataki da k'uru-k'urun idanu bamu ankara ba." jin haka ai yasa ta haiyayak'o kanshi wai ya zageta mai k'uru-k'urun idanu, ita kuwa Inna baki ta tab'e tare da cewa. "Wannan dokoki na kiran sunanka ai sai 'yan boko ni ba abinda ya shamin kai Hayatu zan kiraka." dariya yayi sosai jin Imran na ce mata. "To inna ba sai mu shigar dake makarantarba mu samu ki haddace sunan ba Dukke." shi kuwa Zakariyya sanin bayanshi Inna takebi yasa ya mik'e yana tarfawa yayar tashi tsiya, ganin Inna tak'i ta kulashi yasa ta sunkuyo ta zari hand bag nata tare da car key d'inta dake gefen jakar cikin jin haushin tace. "Yaseen bazan zauna a gidan nan ba, zan koma gida haka kawai a turoni dan inzo in taimaka miki tunda kin gurd'e kuma kina ganin jikanki ya rainani da yake kin fi sonshi bazaki mishi fad'aba." cikin sababi irin na tsofaffi masu zafi tace. "Ki tafi mana kada Allah yasa ki zauna dan ubanki! ai bani na kirakiba ni dama Zahira nace a turo min dan itace mai mutunci, amman tunda kikace bazaki zaunan ba ni kuwa yanzu zan kira Babanku kina komawa zaki dawo kiyi asaran man motarki kawai." bata bi ta kan magar tsohuwar ba ta fice abinta, su kuwa duk bayanta sukabi, suna fitawa tana figin motarta ta tana shirin barin harabar d'an k'aramin gidan, Hayatuddeen ne yayi sauri d'aga murya tare da cewa. "Kadafa ki manta kinada tambarin *L* yaseen ki kula kada kije kiyi ta tambola a titi." k'ura ta bud'esu dashi kana tayi ficewarta daga gidan. Su kuwa nan sukayi ta sabgoginsu sai gab da magrib suka fito suka nufi gida duk da akwai 'yar tazara tsakaninsu amman haka suke tattakawa da k'afafunsu har zuwa gida a cewarsu Hayatuddeen yaga garin da kyau, suna isa gab da gidansu Isma'il ne Imran ya tare machine ya tafi, shi kuwa Hayatuddeen jan hannun isma'il yayi a kan dole sai suje gidansu a dole ya bishi. Sannu-sannu su Ummi sun saba da bak'otansu da iyayen abokansu Saifuddeen da Hayatuddeen. Yau jumma'a shiyasa Saifuddeen bai fita da wuriba, sai h'ar k'arfe tara ya tashi daga baccin daya koma bayan sallan asuba, a hankali ya mik'e mik'a yayi tare da yin salati a zuciyarshi, bathroom ya nufa, wonka yayi mai rai da lfy kana yayi al'wala sannan ya fito d'aure da towel a k'ugunshi sai d'an k'aramin dake hannunshi bisa bakin gado ya zauna ya fara tsane ruwan jikinshi, mik'ewa ya kumayi bisa kujerar dressing mirror ya zauna mai ya fara shafawa sannan ya gyara suman kanshi, mik'ewa yayi zuwa gaban durowar bud'ewa yayi ya zaro wani tattausan yadi mai taushi yadin bak'i ne mai shek'i yanada zanen gidan dara-dara, sai kuma ya zaro boxer and vest farare k'al-k'al, a bakin gado ya ajiyesu, sannan ya kuma dawowa gefen durowar inda takalmanshi ke jere bisa wani kekyawan abin aje takalma wasu fararen takalma ya zaro, sai ya kuma bud'e d'aya sashin na durowar inda hulunanshi ke jere, hula zanna bukar ya zaro fara mai ratsin bak'i-bak'i, kimtsawa yayi cikin kayan da ya fidda d'in, bayan ya gama sawane ya dawo gaban mirror yana dai'daita zaman hularshi a kanshi, murmushi yayi wanda har saida dimples nashi suka lotsa shida kanshi yasan yana kama da Abbansu, ya kuma san Abbansu kekyawane na nunawa sa'a sosai bak'in kayan ya k'ara fito da farin fatarshi ras, in ka ganshi tamkar balarabe suman kanshi a konce lib-lib a k'eyanshi da gefen sajenshi, turare ya d'auka ya feshe jikinshi dashi lungu da sak'o, ido ya lumshe a hankali tare da shak'an numfashi dan jin sassanyan k'amshin turaren dake ratsa mishi jiki da zuciya. Towel d'in daya ciren ne ya d'auka ya shiga bathroom ya shanyashi sannan ya fito, ya nufi parlour. Ummi kuwa da yaranta duk suna parlour suna tab'a hira, Ummi na bisa 3 str Hayatuddeen kuma na konce kusa da ita yayi !!! kan tv, da sauri Ummi ta d'ago kanta ido ta zubawa steps d'in sauk'owa k'asan dan jin takun d'an nata, murmushi tayi tare lumshe ido kana tana godewa Allah daya azurtata da wannan kekyawa halitta a matsayin d'anta cikin sanyin sauti tace. "Masha Allah, babana yayi kyau matuk'a gaya." murmushi yayi shima dan idanunshi na kanta a hankali yaci gaba da tako steps d'in cikin takunshi mai d'arka hankali har ya sauk'o, gabab da ita yazo ya zauna cikin kurma-kurma ya gaidata. "Lfy lau Babana ka tashi lfy ko?." hannunta ya kamo ya manna a habarshi alamun lfy lau Alhamdulillahi. cikin girmamawa Raliya ta kalleshi tare da cewa. "Ina kwana Hamma Saifuddeen." kai ya jinjina mata ta lamun lfy lau, sai ya kuma kallin Hayatuddeen dake kallonshi yana mirmushi cikin k'aunar d'an uwan nashi, murya a sake yace. "Barka da jumma'a Hamma." bai jira amsarshi ba yaci gaba da cewa. "Kayi kyau sosai Hamma na." murmushi yayi kana ya shafa fuskar k'anin nashi. Ummi kuwa mik'ewa tayi ta nufi dinning table tare da yafitoshi tai mishi alamar yazo yayi breakfast." mik'ewa yayi yabi bayanta, Zama yayi a kujerar dake dab da ita yana kallon yadda taken had'a mishi tea, tana gamawa ta mik'a mishi sannan ta zubo mishi soyayyan dankali da kwai sai kuma ta jawo wani filet d'in da alamun wani abun zata kuma zuba mishi, da sauri ya jujjuya mata kai, tare da mata alamun sauri yakeyi tea d'in kawai zaisha da d'ankalin, sanin halinshi da halittarshi ta rashin cin abinci da yawane yasata meda filet d'in sannan ta zauna gefenshi yana d'anci suna kuma d'an tab'a hira sauri-sauri ya gama ya sallameta ya fita ya tafi. Ita kuwa Ummi ta haura sama kai tsaye bedroom nashi ta nufa ita da kanta ta gyara mishi d'akinshi da bathroom da parlour nashi duka ta sassake mishi labuye sannan ta feffesa turaren d'aki mai suna touch me sannan ta rege mishi gudun AC kana ta fito. Tana sauk'owa taci karo da Hayatuddeen a tsakiyar parlour yanata kiciniyar kwance bel d'in k'ugunshi, ido ta zura mishi ba tare da ta k'arisa sauk'owanba hakama Raliya ido ta zura mishi, shi kuwa baima san sunayi ba yana zare bel d'in yayi k'asa da dogon wondon Blue Jeans dake jikinshi ya rage dagashi sai d'an gajeren wondo dake jikinshi, sawunshi ya zare kana ya tsallake wondon inda ya sab'uleshi ya nufi hanyar d'akinshi tare da cilla bel d'in a tsakiyar parlour, sai kuma ya fara kiciniyar cire rigarshi tare da cewa. "Nima bari inje inyi wonka dan yau a masallacin fad'ar jiha zamuyi salla dasu Imran dasu Sulaiman Zakariyya shi yace yama je tun d'azu." tsayawa yayi tare da juyawa da sauri jin Raliya na mishi mgna cikin tsawa take ce mishi. "Wai kai kam Hayatuddeen wanne irin yarone mara kan gado, kalli yadda ka watsa mana parlour dan tsabar sakarci da sakalci inda ka cire wondonka nan kake bar mana shi wato kai gaka auta mai buhun sakalci uwar wa zata tattara maka kwamutsan naka to da ka barshi?." wani dogon tsaki yaja tare da cewa. "Uwata mana ce miki akayi bani da gatane banza kawai uwar sa ido." yana fad'in haka yayi

Table of Contents

Chapters

148 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148