Skip to content

Chapter 14

Chapter 14

Nakasa Ba Kasawa Bace Book One Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

ruwa tare da cewa. "Yauwa mai ruwa bani biyu, wlh tun d'azu nakeji k'ishin kamar zai karni." gane abinda tace yasa Saifuddeen d'auko guda biyu ya mik'a mata, amsa tayi tare da bashi ashirin d'in, shi kuwa Alhaji Ibrahim cikin iya kula da bak'inshi yace. "A a Hajia bar kud'in." sai ya kuma kalli Saifudddeen tare da cewa. "Basu ruwan kowa ya d'auki yadda zai isheshi." ai nan matan nan kowa ta d'auka wasu bibbiyu wasu d'addaya wasuma cikin hand bags nasu suke ajiye ruwan, tuni sun d'auke yafi rabi. lissafi akayi don lokacin ne forko-forkon da pure water ya tashi daga d'aya biyar ya koma d'aya goma, to nanfa had'a lissafi inda kud'inshi ya kama d'ari da hamtsin. aifa sai yaji k'arfin guiwa ya mik'e yabi layin masu saida gonjo wanda kusan a rana suke, cikin k'udurar ubangiji ya saida ruwan tsab, ba tare da yin k'asa a guiwaba yaje ya kuma saro leda biyu, nan sai ya fito bakin kasuwa nanfa 'yan acab'a suka rink'a saya wani a take yake shanye leda biyu wani har leda uku ya saya bar masu sayan d'ad'd'aya, kana masu taxi ma wasu sai su sayi lada hud'u su aje cikin yar durowar motar nasu. Cikin awa d'aya wannan leda biyun suka k'are, ai da sauri ya kuma komawa ganin azahar tayi sai ya amso leda d'aya, kafin kace kobo ya k'are dan masuyin Al'walene sukayi ta kiranshi suna saya, ganin saura d'aya sai yayi Al'wala dashi ganin a layin shagonsu Jabeer yake sai yaje ya ajiye botikin a barandar shagunsun gefen gadajen jarirai, sahun salla ya shiga, bayan an idarne ya yi addu'o'inshi sannan yaje d'aukan botikin nashi, Jabeer na ganinshi yace. "Aboki balarabe dama har yanzu kana k'asar tamu ne?." hararan wasa Saifuddeen ya cilla mishi dan ya gaya mishi shi bafullatanine ba balarabeba, so da yake Jabeer yanada far-far da jama da wasa da dariya sai yace shi dai yasan sai in satoshi akayi daga saudia. botikin ya d'auka kana ya d'an harari Jabeer tare da tsuke fuska irin na abokai sannan ya bashi hannu. da sauri Jabeer ya kamo hannunshi tare da cewa. "Yoh ai dole ma in baka hannu ko zan samu ka rab'a min farinka da laushin hannunka." dariya yaran shagon sukayi baki d'aya, kana sai ogansun yace. "Gashi dai duk muna inuwa fanka na kad'awa muci abinda mukeso, shi kuma gararamba kawai yake a kasuwa amman in ka ganshi sai kace daga fadar masarautar saudia ya fito." cikin had'e fuska Saifuddeen ya zaro biron dake aljihun rigar Jabeer kana ya fara rubutu a tafin hannunshi yana gamawa ya nunawa ogan nasu tafin hannun nashi, kusan a tare suka lek'o da idanunsu bisa tafin hannunshi cikin mmki suke karanta rubutun da yayi da fillanci. "Oga ba gararamba nakeyiba fa inada sa'a ta nima ba yawon banza nake a kasuwarba pure water nike saidawa." cikin mmki suka kalli juna tare da had'a baki wurin cewa. "Ikon Allah kunga wlh da gaskene fa bafillacene." shi kuwa ogan nasu murmushi yayi tare da cewa. "Eh gskyarka ba gararamba kakeyiba ai shi mai sana'a ba matsiyaci ba, yanzu je ka kawo mana ruwan dan yanzu zamuci abinci." aifa da jin haka ya juya ya fita su kuwa sai Al'ajabi sukeyi, yanzu dai sun tabbatar shi kurmane kuma bafillatanine kana yana gane abinda ake fad'i in yana ganin bakin mutun. Leda biyu ya kuma sarowa cikin sa'a kafinma ya isa wurinsu rabin ledane ya rage, nan suka d'auka to ganin bai ishesu bane sai ya kuma komawa ya dauko leda biyu. kai tsaye wurinsu ya nufa nan suka k'ara guda uku. sun bashi kud'inshi ya juya zai tafi kenan sai yaga wannan dottijon mai keke wanda suka tab'a had'u a shagonsu Hisham kusan tsawon sati d'aya daya gabata kenan, still yauma kamar ranar dottijon ya kalleshi tare da mik'o mishi banduran leda guda hud'u irin kitika-kitikan ledojin da in an sayi koda katifan jarirai zai iya shiga ciki kai hatta gadon jariran zai iya shiga cikin ledan, kana in zaka sai setin kayan sanyi dana abin goyo dasu rigunan yara dasu setin mayukansu da takalma duk leda d'aya zata iya d'aukansu dan irin manyan ledodi bak'ak'ennan ne, sai kuma masu binsu sai masu zane bak'i da yellow nan, cikin alamun gajiya dottijon yace. "Yauwa yarona dan Allah mik'a musu." da sauri ya ajiye botikin nashi kana ya amshi ledodin ya juya ya mik'awa Jabeer dake kusa dashi, sai kuma ya kalli ogan nasu ganin yanayiwa dottijon mgna. "Yauwa Baba bello ya a bamu ledodin na dubu hud'u dan na dubu ukun basa isanmu sabida yanzu iyayen yara sun fara sayayyan kayan sallan yaransu ga masu haihuwa nan nata zuwa ga yan mata da samari masu sayan kayan aure." murmushi dottijon yayi kana yace. "Masha Allah ai haka mukeso domin cini kinku shine namu, domin sai kunyi ciniki da muyi tunda mu duk kasuwa abin mune k'arshen saya dole sai an gama sayyaya ake tuna sayan leda." Jabber ne ya murmusa tare da cewa. "Gashi kuma kasuwar taku da yawan al'barka take duk mai saida abu dole sai ya sai naku." murmushi sukayi baki d'aya kana Alhaji Adamu ya mik'owa Saifuddeen 4k d'in sannan shi kuma ya mik'awa dottijon amsa yayi tare da sasu a aljihu sannan ya kalli Saifuddeen da kyau kana yace. "Ngd matuk'a yarona Allah ya maka al'barka." Amin Amin duk suka amsa harda Saifuddeen daya amsa a zuciya, Jabeer kuwa cikin tsokana yace. "Kai Baba bello wannan fa balarabene." ba tare da mmkiba Dottijon yace. "Yoh ai ba musu in akace hakanma." Tahir ne dake gefe ya d'an bugi k'eyan Jabeer kana ya kalli Dottijon yace. "K'aryafa yakeyi maka baba bello shi ba fulatanine kawai dai kurmane." da sauri Baba bello ya kuma kallonsa cikin tausayawa yace. "Allah sarki bawan Allah dama ance ko wani d'an adam tara yake bai cika gomba, wato kai kuma nan tawayar ka take." sai ya kuma kalli Saifuddeen da kyau sai ya sauk'o bisa keken nashi. hannunshi yasa ya jawo wuyan Saifuddeen yadda zai iya ganin tsakiyar kanshi ido ya zura mishi tsawon 38 minutes shi kuwa Saifuddeen shiru kawai yayi ya bashi kai d'in, bayan ya gama dubawa yace. "Masha Allah lallai kam wannan kan naka zai d'auki nauyin abu da yawa, domin magergerar gashi tushe ukune a kanka wanda ba kowa Allah ke yiwa wannan halittarba." shiru sukayi yayinda shi kuwa Dottijon ya kalli Alhaji Adamu tare da hawa kekenshi kana yace. "Akwai al'khairi cikin yin mak'otaka dashi." daga nan yaja kekenshi ya tafi, shi kuwa Saifuddeen d'aukan botikinshi yayi tare da bin bayanshi, yana ganinshi ya nufi shagon masu d'inka hijabannan da alamun suma a wurinshi suke sayan leda. Har zaibi bayanshi sai kuma yaga ana kiranshi a shagon alhaji ishaq haka yasa ya nufi can. Pure water suka sassaya bayan sun bashi kud'in ya juyo kenan sai yaga Dottijon nan tuni ya bar wurin, to sai kawai yaci ga da zageye da ruwan, amman sai cinikin yayi d'ib tun bayan azahar ya d'aukosu amman har la'asar basu k'areba, to saida aka kira sallan la'asarne sai kuma akayi ta saya ana al'wala nan ya samu wannan leda biyun suka k'are. To koda aka idar da salla ya gaji sai ya

Table of Contents

Chapters

148 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148