Skip to content

Chapter 27

Chapter 27

Nakasa Ba Kasawa Bace Book One Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

alamun da kada ta sake biyoshi gwara tazo da rana. kai ta gyad'a mishi kana itama ta d'auki buta dan yin al'wala. Su kuwa suna gamawa suka nufi masallaci koda akayi insha akayi asham, suna fitowa suka shiga cikin gida ruwa suka sha sannan suka nufi hanyar fita dan tafiya wurin tabsir kamar kullum, har sunje bakin k'ofar fita Ummi tace. "Ahmad ka dawo da wurifa ku tafi kasan Raliyya yanzu zatayi bacci anan." juyawa yayi ya d'an kalli Raliyya cikin lumshe ido yace. "Shike nan in tayi bacci sai in goyata mu tafi gida abinmu." Warisu ne ya d'an bugeshi tare dayin k'asa da murya yace. "Kai a gaban Ummin kake mata wannan kallon kamar wani tsohon maye." ita kuwa Ummi cewa tai. "Asheko yau sai dai ku kwana anan." dariya sukayi kana suka fita, Raihana kuwa da sauri ta isa gaban Saminu da shi yanzu yake shan ruwan, cikin kauda kai ta mik'o mishi dabinon data ciko hannunta dashi guga bakwai ya tsinta kana yace. "Ya isa sai mun dawo." "To". tace dashi a sanyaye. Daga nan suka fita suka tafi masallacin fad'an Dukku. Ita kuwa Ummi ita da kanta ta shiga kitchen dan k'arisa aikin ferfesun zabbin data fara dan tasan yau Rahma ta gaji sosai, Raliyya kuwa k'ofan bappa Ali ta nufa wurin Aunty Nina, Raihana kuwa Attaruhu da al'basa ta d'auko tazo ta zauna gefen Rahma da keyiwa su Hayatuddeen homework shida Faruq, d'an k'aramin bilandan dake hannunta ta had'a kana ta yayyanka su ta jajjagasu sannan ta juye a roba mai marfi, Hayatuddeen kuma saura su kankana da ayaban da akaci ya d'an rage guntayen yake ci shifa a dole baya son cin abu mai nauyi a rayuwarshi. Ummi kuwa a kitchen tuni gidan ya cika da k'amshi dan zabbin sunji kayan had'i bayan ta gama zuba komai ne sai ta rufeshi bisa rushin yaci gaba da bararraka, tea ta kuma tafasawa ta d'ura a filas sannan ta fito gudan dubu ta bawa Hayatuddeen ya sayo musu sabon biredi, guda biyu, da sauri ya mik'e ya amshi kud'in yana zuwa ya kwaso biredi har guda hud'u. Yana shigowa ganinshi da ledodi har biyu yasa Rahma cewa. "Kai amman dai kai kam Hayatuddeen kaga ta kanka shin ba biyu aka aikeka ba?." da sauri Ummi tace. "Barshi ai bazai b'aciba nida nakeda samari yanzuma sun kusa dawowa." Raihana ce ta d'an harareshi kana tace. "Ai shiyasa yake komai na sakalci sabida yasan ba abinda za'ayi mishi ana tab'ashi kad'an Ummi da Hamma Saifuddeen zasuyi ta fad'a." sai ta kuma kalli Rahma daketa dariya tace. "Baga irinta nanba ai harda ke ake sakaltashi." dariya sukayi baki d'aya ganin yana yiwa Raihana gwalo, Raliyya kuma da yanzu ta shigo dungure k'enyashi tayi nan suka fara 'yar tsamarsu ta sak'o da sak'o. Daga bisani suka zauna suna hira cikin nitsuwa Raliyya ta gyara zamanta sannan ta fuskanci Ummi a hankali tace. "Ummi Ya Ahmad yamin d'inki kala biyu ya kuma sayamin takalmi da mayafi ya kuma yiwa Faruq da Adam ma, sai ya kuma yiwa Hayatuddeen dashi da Hamma Saifuddeen iri d'aya." cikin mamaki Ummi tace. "To shi Ahmad duk samunshi a kanku zai k'are ne, yayi ta zaman d'inki yana shan wuya ya kuma k'arar da samunshi a kanku ai wannan d'awainiya tayi yawa." cikin sanyi tace. "Wlh yana wahala kam Ummi kwana fa yakeyi yana d'inki, to amman kuma yana samun kud'i kinsan ya iya d'inki wasu ma daga bajoga da Ngalda duk shi suke kawowa d'inki gashi nan dukku duk ba wani tela daya fishi iya d'inki kinga fa duk zuriyar gidan sarki shi suke bawa d'inki tunda Ya Saminu ya hadasu dashi." sai ta kuma kalli Raihana tare da cewa. "Ai naga kema Ya Saminu ya bada aiyi miki dunkuna har kala uku, d'aya atampa ce d'aya kuma lace d'aya kuma shadda ce kedashi iri d'aya." shiru tayi kamar bataji ba dan kunya takeji bata son a gane Ya Saminun sonta yakeyi tunda yace mata sai ya gama karatunshi, dan yanzu yana level 2 a G.S.U kunsan duk abokan Saifuddeen sun wuceshi da shekaru biyu sanadin nakasar daya samu ta sashi tsagaitawa da karatunshi sai daga baya da Nurudden ya kawo shawarar ya fara zuwa gombe dashi yana kaishi makarantar kuramen. so shi Saminu shiyasa bai fiye zaman Dukku ba Salisu kuma kusan shine ya rik'e kakarshi inna shatu, Mudassir kuwa yanzu iyayensu hankalinsu na kan karatun Ya Adnan da yake karatun likita yakeyi shiyasa basu bi ta kan mudassir ba tukun tunda sunaga shi Adnan ya kusa gamawa ason ransu sai sun gama da Adnan sannan su dawo kan Mudassir. Warisu kuma yak'i ya nemi sana'a sai dogon buri to shima mudassir ai da yanada sana'a da duk sun d'auki nauyin karatunsu tunda su ba nauyin ciyar da wasu a kansu, to Saminu kuma da yake d'an gatane dan sarki kuma shalelenshi shiyasa tuni yayi nisa a karatunshi shiyasa ma yakeda damar yiwa Raihana hidima Ganin Raihana tayi kamar bata jisu bane yasa suka kauda zancen. Suna cikin haka suka jiyo hayaniyarsu Ahmad alamun sun dawo daga wurin tabsir d'in. Bayan sun shigo duk suka zauna bisa taburma sunata hirarsu ta abokai matasa, ganin Ahmad ya sake ko a jikinshi kamar ba har Shabewa zasu komaba ne yasa Ummi ce mishi. "Kaida zaku tafi kuma shine harda konciya kallifa har tara da kwata tayi." sai ta kuma juyo ta kalli Raliyya dake konce kanta bisa sallayar da aka ninnenke. "Ke maza tashi ku tafi." cikin alamun bacci tace to, Saifuddeen kuwa gyara zama yayi tare fuskantarsu cikin body language yace dasu. "Ba inda fa zaku tafi a daren nan ku bari gobe kwa tafi da safe." ido Ahmad ya zaro tare da cewa. "To uban wa zaimin d'inkunan da na yanka na ajiye da kake cemin mu kwana." hararan shi Saifuddeen yayi tare da rubuta mishi. "Uban uwarka ne zai maka d'inkin." dariya Ahmad yayi sosai yayinda Ummi taketa hararansu tare da ce musu. "Kada ku sake samin kawuna a shirmenku kuyi da iyayenku banda salihan iyayenmu kam da suka bar duniya da dadewa." cikin dariya Ahmad yace. "Yoh dama wa zaice iyayenshi ba salihaiba mu nan gani muke duk duniya ba salihai kamarku." shi dai Saifuddeen murmushi yayi had'i da shafa k'eyanshi da Ummi ta d'an dungura. kana sai ya kuma tsuke fuska sannan ya musu alamun, dolefa su Ahmad su kwana da shi kad'ai yazo kamar kullum da zasu rakashi so tunda ya taho da Raliyya kuma dole su kwana, ita kam Raliyya tuni ta b'ink'ire, shi kuwa Ahmad tsaki yaja tare da cewa. "Yaseen d'inku nanka sai bayan salla zan maka su, tunda dama gashi har yanzu baka kawosuba kuma kasan tun kafin azumi nake rufe karb'an d'inki amman da yake kai d'an gadarane da can da saya maka akeyi ma kullum wai sai ishirin da d'aya ga watan kake mik'o min dinkin ka kakuma samin naci dole in d'inka maka." Tab'e baki yayi tare da d'aga mishi girarshi duka biyu alamun dolenka ai, Warisu da su Salisu kuwa kanshi sukayi da cewa kadafa yayi musu al'k'awarin teloli. mik'ewa yayi ya nufi d'akin Saifuddeen tare da ce musu. "Kunga kada ku d'aura min jakar tsaba kaji su bini su tsatstsageni

Table of Contents

Chapters

148 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148