Skip to content

Chapter 31

Chapter 31

Nakasa Ba Kasawa Bace Book One Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

ciki sai kad'an-kad'an , gaban Ummin ya dawo tare da mata alamun, "Ya akayi ba ruwa a randunan me Raihana keyi da bazata ja ruwan ba tunda Raliyya bata nan Hayatuddeen kuma bazai iya dan rijiyoyin suna da d'an karen zurfi, Rahma kuma na fama da aiki." juyawa tayi a hankali ta nufi can gefen wata k'atuwar bishiyar maggoro da rijiyoyin ke k'asanta duk suna cikin inuwan bishiyar da sauri yabi bayanta, suna isa ya zura gugar a cikin rijiyar dad'in, ita kuwa Ummi da sauri ta rik'e tare da cewa. "Je ka huta zan ja ruwan ita Raihana yau tun da safe cikinta ke ciwo, Rahma kuma jiya ta yanke a 'yar yatsarta garin yankan lemu." da sauri ya jujjuya mata kai kana yaci gaba da zura gugan alamun shi zai ja ruwan. Ita kuwa Ummi tausayinshi ne ya rufe mata zuciya da jiki tasan muddin in dai yana nan tofa baya tab'a yarda taja ruwa, to shi kuma in dai yaja ruwa sai hannunshi suyi jazir musamman yatsunshi da sai sunyi alamun d'ura ruwa, Ummi tafi kowa sani jikin Saifuddeen baya juran wahala yana tsoron wuya so amman sai yake b'oye musu hakan da jarumtar zuciyarshi da take tirsasa gangan jikinshi jajircewa koda ko zai wahala. ido kawai ta zuba mishi ganin yadda yake jan ruwan da karsashi tamkar baya jin wahalan, yana cika botikin yaje ya juye mata rabin a tukunyar rabin kuma ya juye a rand'a kana ya yafito Hayatuddeen tare da nuna mishi d'an k'aramin botiki alamun ya d'auko yazo suna kai ruwan rand'a, da sauri Hayatuddeen ya mik'e tare da suran botikin. daga nan sukaci gaba da d'iban ruwan in ya cika botikin shi sai ya cikawa Hayatuddeen sannan su d'auka a tare suje su juye a rand'a. Ita kuwa Ummi tuni ta koma gindin murhunsu na wojen tanata hidiman dama kunun Rahma kuma na kitchen tana k'arisa aiyukanta. Cikin k'ank'anin lokaci suka cika randa biyu sun fara sawa ana ukun ne Rahma ta fito daga cikin kitchen d'in tana ganin Saifuddeen ne ke jan ruwan tayi maza ta isa gindin rijiyar cikin sauri tasa hannu ta kamo igiyar gugan tare da cewa. "Ka bari haka ya isa, Ummi ya za'ayi ki barshi yaja ruwa kinsan yanzu hannunshi zai d'uri ruwa." cikin kula Ummi tace. "Yak'i ya barni inja kin san ba yarda zaiba, kuma bazai bari mu zauna ba ruwa ba." fuska ta kwabe ganin ya amshi gugar yaci gaba da jan ruwan, cikin sanyi tace. "To ka rink'a ja nida Hayatuddeen zamu rink'a jida, ni da ka bari ma dan na aika Mudassir yazo kuma nasan in yazo in na sashi ba k'i zaiyiba." cikin k'arfin hali ya nuna mata alamun karta damu, daga nan sukaci gaba da jan ruwan. Suna gamawa ya cika botikin ya shiga wonka, tuni Ummi kuma ta gama dama kunun, inda Raihana da cikinta ya d'an lafa ta tashi zaune ta jingina da bishiyar dimurin dake tsakiyar gidan nasu kusan nanne wurin zamansu, Rahma kuma duk ta had'a komai na bud'a baki har miyar asuba tayi musu tunda Raihana maiyin bata da lfy, Hayatuddeen kuwa tuni Ummi ta d'ora mishi kulan masa ya kai ya dawo kana ta d'ora mishi na k'osan tare da bashi robar dake cike da dabino a hannu bayan ya dawone ta kuma aza mishi kulan kunun tare da cewa. "Zaka iya ko autana?." cikin dakiya da jarumtar da yake koya a wurin Hamma Safuddeen d'inshi yace. "Eh Ummi zan iya." kai ta gyad'a sannan tace. "To in kaje kace a sauk'eka kada kace zaka sauk'e da kanka dan bazaka iyaba." juyawa yayi yana fita tare da cewa. "To, duk da yaso yayi irin na Hamma shi duk abinda ake tunanin bazai iyaba sai ya yin, to amman ina ai shi Autan Ummi akwai ragwanci over. Shi kuwa Saifuddeen bayan yayi wonka yana fitowa ana kiran salla. Ummi da kanta yau ta zuba mishi madara da sugar bisa kankanan ta kuma wonke mishi dabinon, yana isa inda suke ya zauna gefe bisa wani dutse wanda nan suke zama suyi al'wala, Faruq ne ya mik'a mishi buta yayinda Ummi kuma ta mik'o mishi dabinon, Ummi da Rahma da Raihana duk tafin hannunshi suka zubawa ido ganin sunyi jazir tamkar ka tab'a jini ya tsallo, kan yatsunshi kuma sunfi ko ina yin ja, cikin muryar ciwo Raihana tace. "Dan Allah Hamma kada ka sake jan ruwa kalli yadda tafin hannunka sukayi fa." yi yayi kamar bai gane me take cewaba. Ummi kuwa kamar tasa kuka takeji dan tausayinshi, Rahma kuwa hannunta tasa ta shafi tafin hannun nashi ganin duk inda ta shafa sai jinin wurin ya gudu wurin yayi fari sai kuma a take wurin yayi ja kamar da, sai kuma duk suka juyo kan Raihana dan ganin ta kamo hannun Umminta ta rik'e gam alamun, ciwon cikin nata ya murd'a, gaba d'aya jikinta rawa yakeyi dan azaba, kusan a tare suke ce mata sannu, shi kuwa Saifuddeen nuni yayiwa Ummi da ta, had'awa Raihana zuma da ruwan zafi ta bata tasha." cikin gane abinda yake nufi tace. "Na bata ta sha tunda da yamma nace tasha amman tak'i wai ita sai ta kai azuminta, to sai yanzu da auta ya kai dabino masallaci yace ansha ruwa to shine ta amshi ruwan zafin da zuman tasha yanzu kuma inaga cikin ya kuma murd'awane." sai kuma suka bita da idanu ganin ta mik'e da sauri ta zari butan dake gaban Saifuddeen d'in ta nufi band'akinsu, tuni kuma Al'adar tata ta iso har ya d'an b'ata mata zani, ai da sauri Saifuddeen ya rumtse idanunshi dan yanada tsananin k'yank'yani yanzu haka bazai sake cin abin hannun Raihana ba har sai yaga ta samu tsarki tana salla, Rahma kuwa dariya tayi tare da cewa. "Hmmmm Deeen kenan tunda kai na mijine ai da sauk'i, sai dai kuma tunda zakayi aure ba mmki wata ran kayiwa matarka wonki." kame jikinshi yayi alamun tsikar jikinshi ya tashi da batun wai shi dai yayiwa matarshi wonkin wannan k'azantar, Ummi kam tuni ta bar wurin shi kuwa yawu ya tofar kana ya d'auki pillet d'in kankana ya mik'e tare da yiwa Adda Rahman tashi alamun Allah ya kiyasheshi da sharrin bakinta, dariya tayi tare da bin bayanshi da ido, tabbas tasan su duka zuriyarsu kyawawane amman babu wanda ya kai Saifuddeen ita kanta wani lokaci ganinshi take tamkar balarabe ko ba indiye, gashi komai nashi da nitsuwa da tausayawa, gashin k'eyanshi ta zubawa idanu har saida ya b'acewa ganinta. Shiko yana fitowa woje yayi gefen su Warisu nan suka shanye kankanan a tare amman time to time yakan rumtse ido in ya tuno jinin da ya gani sai ya kuma tofar da minyau. Ana idar da salla suka shiga gida inda suka samu, yau kuma awaran couscous Adda Rahma tayi musu sai masan da ta d'iba musu cikin na masallaci sannan tayi musu miyan alaiyahu da tontok'oshi wanda da miyar zasuci masan, sai kuma tea da ta kawo musu amman ba madara, dan azumi yazo k'arshe mafi yawanci cefenensu yayi k'asa sai kuma kunun gyad'a, nan sukaci sukasha kamar kullum, sannan suka tafi jin tabsir wanda yau zasu rufe 27 ga watan Ramadan d'in kenan. Suna dawowa ta kawo musu tuk'ek'k'en tuwon

Table of Contents

Chapters

148 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148