Chapter 118
Chapter 118
Zaleeha kamar ta mutu dan baƙin ciki, dan tasan abinda yasa Ya Ahmad ɗin nata yayi musu haka. Bilkeesu kuwa gyara kwanciyarta tayi tana kallon film d'in Sanam Teri Kasam da ake haskawa a tashar MBC Bollywood. Biyar dai-dai Ahmad ya shigo tare da ishaq. Kai tsaye parlour'n Saifuddeen suka nufa. zaune suka sameshi bisa wellchair ɗinshi, mai kalan golding ash. Wani irin murmushi Ahmad yayi tare da cewa. "Fatabarakallahu fi hasanil Kaliƙin, tsarki ya tabbata ga ubangijin sammai da ƙassai da yayi wannam kyakyawar halitta." Ishaq ne ya amshi zancen da cewa. "Masha Allah!." Murmushi Saifuddeen yayi wanda yake sanye da wata ɗanyen yadin getzner mai azabar kyau kalar dark green mai turuwa, irin dark mai shinng ɗinnan, yayinda aka zubawa kayan wani fitinennen ɗinkin half jumper and pencil trouser, daga wuyan rigar kuwa aka watsa mishi wani tattausan zaren surfani. yayinda ya murza wata kyakyawar hular damanga mai ratsin dark green akansa, daga ƙafansa kuwa wasu irin fitinannun toms mai kalan shaddarsa yasa, ƙiran company'n Gucci, me matuƙar tsada, still kuma zazzafan agogon company'n Gucci ne ke ɗaure atsintsiyar hannunsa wanda kuɗinsa kaɗai ya haurawa 80k, sai wayarshi ƙiran iphone 11 pro max daya zura cikin al'jihun gaban rigarshi, wanda abayyane ta saman al'jihun rigartasa, kake iya hango kyawawan camera's ɗinta guda uku dake jere reras, biyu asama ɗaya aƙasa. Yanayin shigar tasa ta matuƙar ƙara fito da farar fatarshi kai ka rantse da Allah cewa balarabe ne. Sajen nan nashi yayi wani lub-lub yayiwa fuskarsa ƙawanya sai sheƙi da ƙamshi yake, red colour lips ɗinshi sai shinning skeyi tamkar an shafa mishi mai a kansu. Shida kanshi ya sarrafa whellchair ɗinshi suka fito zuwa parlour. Ummi suka samu ita da Hayatuddeen azaune. gabanta suka tsaya cikin shirinsu na fita, murmushi tayi tare da godewa Allah daya bata wannan kyakkyawan ɗan, cikin gane batun da ya mata tace. "Allah ya kaiku lafiya, ya dawo daku lafiya, Allah ya baku nasara da sa'a kan abinda zakuje nema. Allah ya sadaku da al'khairin dake cikin tafiyar ya rabaku da sharrin dake tare da tafiyar." Da "Amin." Suka amsa baki ɗaya. Shi kam Saifuddeen wani sanyi da farinciki ne suka rufeshi sabida addu'o'inta gareshi. Shiko Hayatuddeen sai hotuna yaketa musu. Daga nan suka fita, har bakin gate Hayatuddeen ya rakasu, saida yaga sun fita sannan shima ya ɗauki machine ɗinsa ƙirar UD, ya nufi gidan Inna dan zaije wurin Zakariyya. Su Saifuddeen kuwa suna isa G.R.A. Ahmad ya rinƙa bin ƙwatancen da Baffa Ali yayi musu, suna isa bakin gate ɗin suka danna horn, sunyi biyu ana uku aka wangale musu makekem gate ɗin. Cikin nitsuwa Ahmad ya dai-daita parking ɗin motar, a hankali ya buɗe marfin motar ya fito cikin shigarsa ta al'farma, both ɗin motar ya buɗe tare da fiddo whellchair ɗin Saifuddeen, ta inda yake yazo, buɗe mishi murfin motar yayi kana ya gyara mishi keken. Yayinda tuni Ishaq kam ya fito. Yana gama gyara zamanshi kan whellchair ɗin sai ga Ahmad ya fito daga cikin gidan hannunshi riƙe da Unaisa ganinsu yasa cikin sauri ya nufi inda suke, ganin haka Ahmad Abban farida ma ya saki fuska kana ya nufi inda suke hannu suka bawa juna, Abban Farida ne ya fara magana, inda yace. "Assalamu alaikum." "Ameen wa alaikassalam, barkanku da zuwa." "Yauwa barka dai." Murmushi yayi tare cewa. "Ahmad yayan Zaleeha." cikin sakin fuska Abban Farida yace.. "Ni kuma Ahmad yayan Saifuddeeen." Murmushi sukayi baki d'aya, sannan suka taho inda su Ishaq ke tsaye, cikin tsananin son Saifuddeen ya sunkuyo ya bashi hannu sukayi musabaha, sannan suka gaisa da ishaq wanda shi sam bai gane cewa Ishaq makaho bane. Jagora yayi musu zuwa BQ inda dama yasa Lubna ta gyarashi fes tunda safe. Bayan sun zauna ne yace. "Bari naje na turo muku ita ko." cikin fara'a Abban Farida yace. "Ayi haka babban yaya." "Ai anyima." ya bashi amsa yana ɗan murmushi, kana yafice daga cikin babban falon BQ ɗin. Shiru sukayi kowa da abinda ke ransa, shi kuwa Saifuddeeen azkar yakeyi azuciyarsa cikin nutsuwa. Zahira yasa ta kai musu abin sha, kana ya nufi side ɗin Mama. A Parlour Mama ya samesu suna hira sama-sama dan kowacce da abinda takeyi. cikin tsare girar sama data ƙasa yace. "Ke Zaleeha tashi kije BQ kinyi baƙi." wani irin tsuke fuska tayi tare da yamutsa fuskar kana tace. "Baƙi kuma ya Ahmad." Ya Habune da yanzu ya fito ɗakin Mamansu yace. "Ke shi sa'anki ne yana miki Magana kina zaune, Zaleeha kifa kiyayeni nagafa baki da kunya ji kike kamar kin kamomu ko?." Da sauri ta jujjuya mishi kai tare da miƙewa jiki na tsuma domin ita dai Allah ya sani tana tsoron ya Habu da Ya Aminu mugayene na bugawa a mujalla yazu zasuce zasu kai mutun mari. "Maza ɗauko mayafinki ki ɓace mana daga nan." Da sauri ta nufi ɗakinta, shi kuwa ya fice daga falon. A zatonta yana nan shiyasa tayi maza ta fito tana mai yin rolling kanta da ɗan kwalin lafiyayyar Arabian gawn ɗin dake jikinta, ganin baya nanne ta zumbura baki tare da cewa. "Bilkisu muje ki rakani." Kai bilkisu ta jujjuya tare da cewa. "Tab ina cikin kallon wannan film ɗin ai babu inda zani, Rashida ta rakaki mana tunda ta gama zanen da takewa Aunty Lubna." Ahmad ɗinne ya kalli Rashida cikin bada umarni yace. "Rashida rakata ko." "To" tace tare da miƙewa ta ɗauki mayafinta. Suna gab da fita aka tafi talla, ganin haka Bilkeesu ta miƙe tare da cewa. "MBC Bollywood iyayen talla sun tafi, muje inga sahibin namu kafin in dawo sun gama tallarsu na tsiya." dariyan mugunta Rashida tayi, kana suka nufi BQ. Shi kuwa Ya Ahmad parlour'n Baba Malam ya nufa. Yana shiga ya samesu da Mamy da Mama da kuma Baba Malam ɗin. Gefen da littatafan addini wanda suke jere ya nufa yana mai cewa. "Baba Malam su Saifuddeen sun zofa." kai ya gyaɗa alamun to kana yace. "Ka tura mishi Zaleehan" "ai tama tafi." ya bashi amsa yana me zama kusa dashi, kai ya ɗan kwantar cikin sanyin sauti yace. "Naji tausayin Saifuddeen baba ya bani tausayi, mutun kyakkyawa matashi Allah ya jarabceshi da nakasa mai zafi, wlh Baba sai ka ganshi yama fi kyau a zahiri akan a hoto, in dai Zaleeha ta yarda dashi to haƙiƙa tayi dace da miji managarci, domin sam nakasarsa bata zame mishi kasawa ba, in ka ganshi kamar ba kurmaba, haka inba dan wellchair ɗin da yake zaune a kaiba bazaka taɓa cewa gurgu bane." Cikin mamaki Mama ta ƙara haɗe fuska tare da cewa. "Wai maganar me kukeyi hakane ban gane inda kuka dosaba, Gurgu kurma wurin waye yazo!?." Cikin isa da tsare fuska Baba Malam ya mata bayanin komai akan Saifuddeen ya ƙara da cewa. "Kuma ni yamin na yaba dashi muddin bata fidda waniba to niko zan aurawa Saifuddeen ita!." Kaƙa ƙara ƙaƙa wayyo Mama ina wuta ta faɗa ciki, don baƙin ciki da takaici, cikin tsananin hatsala da takaici tace. "Kurma! gurgu!? Yar tawa zaku haɗa baki kuce gurgu zaku aura mata? ai Wallahi bazata taɓa saɓuwa ba." Mamy ne tayi saurin cewa. "Kiyi mata fata da addu'an abinda yafi al'khairi zaifi akan mugun furuci baki san inda rabonta yakeba." Wani irin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148