Skip to content

Chapter 127

Chapter 127

Nakasa Ba Kasawa Bace Book One Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
Download Book

rantse Adda Raihana saina baku mamaki, saina nunawa Hammana cewa idan yana dani bashida damuwa a duniya!." Yaƙare maganar yana me jujjuyawa, tare da soma yin rawar shaku-shaku. Dariya Ummi da Raihana suka saka, don abun na Hayatuddeen ya wuce tunaninsu, ganin hayaniyan su Hayatuddeen ɗin na ƙoƙarin damunta yasanya ta miƙewa ta koma ɗaki bayan tace da Hayatuddeen ya kaiwa Saifuddeen ɗin abincinsa, tana shiga ɗaki ta dannawa number'n Adda Rahama ƙira, bugu biyu Adda Rahama dake kwance jikin Dr Adnan suna shan love ɗinsu ta ɗaga wayar, cikin son dai-dai-ta nutsuwarta tace. "Ummi barka da dare." Murmushi Ummi tayi tare da cewa. "Barkanki dai, fatan kuna lafiya baki ɗayanku." Da "Lafiya ƙalau." Adda Rahama ta amsa mata. Gyara zama Ummi tayi, take tashiga labartawa Adda Rahama maganan auren Saifuddeen ɗin da ta taso lokaci ɗaya. Hmmm faɗar irin tsananin farin cikin da Adda Rahama tasamu kanta aciki ma ɓata lokaci ne, sosai taji daɗin labarin nan tace zata tambayi Dr Adnan gobe idan yabarta zatazo gidan, da haka sukayi sallama ita da Ummin nata, cikin ɗoki haɗi da marari ta rugume mijin nata ƙam-ƙam, fuskarta ɗauke da farin ciki tace. "Yaya Adnan Saifuddeen zaiyi aure, ina cikin tsananin farin ciki wallahi, nasan shima zai samu salihar mace wacce zata kawar masa da duk wata damuwarsa!." Cikin jin daɗin labarin Dr. Adnan yasake hugging ɗinta, dogon gashin kanta ya shafa, tare da sanya hannuwansa ya ɗago haɓanta, ido cikin ido suke kallon juna cikin nuna jin daɗinsa yace. "Alhamdulillah lallai zamusha biki, masha Allah mun kusa zama surukai!." Murmushi Adda Rahama tayi tare da cewa. "Farin cikina bazai faɗu ba Ya Adnan, akullum da tausayin Saifuddeen nake kwana nake tashi, raunin Saifuddeen raunina ne, naji daɗi matuƙa saboda nasan shima ayanzu zai samu gamsuwa irinta aure!." Murmushi Dr Adnan yayi tare da jan dogon hancinta cikin salon tsokana yace. "Hmmm irin wato ke kinsan gamsuwar aure ɗinnan ko?" Dariya suka sanya atare, cikin yanayi najin kunya ta ɓoye kanta acikin ƙirjinsa, sake matseta yayi cikin raɗa yace. "Dama kuma nima gashi yau inada buƙatar wata gamsuwar, ke ma kinsani bana taɓa gajiya dake!." yafaɗi maganar yana me haɗe bakinsu waje ɗaya. *** Fitowarsa daga wanka kenan, wata brown jallabiya yasanya ajikinsa, tattausan darduman sallansa ya shumfuɗa inda ya gabatar da sallan Isha, kana kuma ya gabatar da sallan shafa'i da wuturi, yajima zaune akan sallayan yana addu'o'i har Hayatuddeen yakawo masa abinci ya fita, bai idar ba, cikin nutsuwa yajawo kekensa, cikin yanayi na ɗan dabara daya saba ya zauna akan lafiyayyar keken nasa, food flask d'in da Hayatuddeen yakawo yashiga bubbud'ewa, kulan farko daya bud'e yam balls ne aciki wanda yaji kayan ƙamshi da kuma ƙwai, sai kuma sauce ɗin egg and onion da akayi musamman don cin yam balls ɗin dashi, ɗayar kulan kuwa pepper chicken ne aciki wanda yaji curry da kayan ƙamshi, gaba ɗaya ƙamshin abincin ya cika ɗakin, pepper chicken ɗin yaɗan ɗiba kaɗan a plate, wani ɗan madaidaicin flask ya jawo wanda ke ɗauke da tafashashshen coffee, ruwan coffee ɗin wanda yaji kayan ƙamshi ya zuba acikin wani ɗan madaidaicin cup, bawani sosai yaci naman ba saidai ace ba laifi, coffee ɗin nema yasha sosai, minti 10 da gamawa Hayatuddeen yazo ya kwashe kwanukan yafita dasu, kekensa ya tura inda ya nufi bathroom, kaitsaye gaban ɗan madaidaicin sink ɗin dake cikin toilet ɗin wanda yake dai-dai tsawonsa ya nufa, yana daga zaune akan keken nasa yayi brush, yayinda ya sake ɗaura sabuwar al'wala ajikinsa, don sam hakanan yake baya wasa indai wajen zama da alwala ne shi gwanine awannan fannin, domin yawan zama da alwala ma wata babban kariyace ga bawa. Cikin hikima ya hau kan gadonsa tare da rage gudun AC'n dake ɗakin, luf yayi akan gadon nasa tare da fidda wani irin numfashi, lumshe kyawawan idanunsa yayi yana me imagine kyakkyawar surarta acikin idanunsa, kyakkyawan murmushine ya bayyana akan fuskarsa, sakamakon tunawa da yayi da yanda ɗan ƙaramin bakinta ke motsawa, alokacin da take surfa masa ruwan masifa, komai nata me kyau ne, haka kuma komai nata gwanin burgewa ne, harshensa ya sanya yaɗan lashi laɓɓansa wanda suke cike da muradin jinsu akan nata laɓɓan, wani irin so yakewa Zaleeha wanda shikansa baisan iyakarsa ba, yanason Zaleeha fiye da duk yanda wani zaiyi tunani, sake gyara kwanciyarsa yayi tare da sakin wani killer smile, wani irin nishaɗine yakejin ya cika zuciyarsa, kalmar "Maye." da ta ƙirasa dashi shine abun daya dawo cikin brain ɗinsa. cikin ƙasan zuciyarsa yace. "Am so sorry My Beautyful Wife, dama kin sani da bakicemin maye ba, don kuwa gashi yanzu kinjawo dole saina nunamiki cewa eh da gaske niɗin maye ne." Cikin wani irin azababben shauƙin sonta haka bacci ɓarawo ya ɗaukeshi. Gaba ɗaya ko ina dake cikin gidan nasu ya ɗauki shiru, a irin wannan lokacin mafi yawancin mutane kowa na kwance ne a makwancinsa, yayinda wasu ke gudanar da baccin nasu cikin yanayi mai daɗi, saɓanin wasu kuwa da sukeyinsa cikin rashin yanayi me daɗi, adai-dai wannan lokacin cikin waƴanda suke bacci cikin rashin jin daɗi hadda Zaleeha domin kuwa duk sanyin dake cikin ɗakin ita gumi ne ke fesowa daga jikinta. Binsa takeyi cikin sauri ayayinda ko takalma babu aƙafanta, ƙoƙarin cimmasa take amma yana ƙara yi mata nisa, bayansa kawai take iya hangowa kasancewar ya bata baya, cikin ƙosawa haɗi da gajiyawa ta tsaya tare da sanya hannuwan ta duka biyu ta kama ƙugunta, cikin tsananin gajiys muryar dake bayyana rauninta tace. "Dan Allah katsaya, katsaya atare dani, barinka cikin rayuwata tamkar rabani da numfashina ne, tayaya zaka gane irin sonda nake maka? shin tayaya zaka gane cewa ina buƙatarka cikin rayuwata, Dan Allah kazo, katsaya nazo gareka!!." Cak ya tsaya daga tafiyan da yakeyi, amma saidai ko motsawa baiyi ba balle tasa ran cewa zai juyo ta kalli fuskarsa. Ahankali tashiga takawa zuwa garesa, taku biyu kacal ya rage taƙarasa garesa, ahankali yaɗan juyo gareta, idanunta ne suka sauƙa akan kyawawan laɓɓansa wanda ke ɗauke da kalar red, yayinda wasu kwantattun gargasa sukayiwa bakinnasa ƙawanya, wani irin sheƙi da shinnig gashin dake kwance akan fuskar tasa keyi, idanunta taɗaga daniyar kallon full face ɗinsa, kafun ta sauƙe ganinta akansa wani irin haske wanda batasan daga ina yafito ba ya cika gaba ɗaya idanunta. Azabure ta-tashi daga baccin da takeyi, cikin ƙaraji tace "Dan Allah kada katafi pleaseee help me!!!." Buɗe idanunta wanda suka kaɗa sukai jajur tayi, lokaci guda wani irin gumi ya shiga keto mata, ƙirjinta ne yashiga bugawa da sauri sauri, aƙalla taɗauki kusan 3 minute kafun taɗan soma dawowa cikin hayyacinta gane cewa mafarki take yasanyata sakin kuka mai ciwo, jikinta ta takure waje ɗaya tare da cusa kanta tsakankanun cinyoyinta, kuka take rerawa sosai mai ɗauke da tsanin ciwon so, cikin rufewar ido haɗi da sambatu tace. "Shikenan katafi kabarni? yazanyi? shin tayaya kake tunanin zan iya jure rashinka? nazautu akan sonka, nakai ƙololuwa, nazama kurma, makauniya, har wasu suna mini kallon zautacciya duk akan sonka, Ina sonka! Ina sonka! Ina tsananin sonka!!!." Taƙare maganar tana me rushewa da kuka, sosai Zaleeha tayi kuka awannan dare har da shiɗewa, daƙyar ta iya jan jikinta ta wuce toilet, wanke fuskarta tayi kana ta ɗauro alwala, sosai wani irin

Table of Contents

Chapters

148 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148