Chapter 117
Chapter 117
mai taken. "So makaho ne, kamar walƙiya ya kamani, gashi na zautu al'umma sunata nunani!." Sai kuma ta yi magana a hankali, inda tace. "Da fatan dai kuna jin daɗin waɗan nan zafafan waƙoƙin da muke kawo muku daga tasharmu ta Vission FM. Ku gyara zama domin jin waƙarmu ta ƙarshe sakamakon ganin lokaci na hararanmu. Sai ta kuma saki wata zazzafar waƙa mai tsuma zuciya, inda jarumar ciki ke cewa. "Zo muyi zance masoyi na kajiya." Sai ta kuma sai-sai-ta waƙar tare da dai-dai-ta muryarta data waƙar tana bin baitin. "Karda ka kauce, kasa ai mini dariya. Saida na tace na zaɓo ka guda ɗaya, babu irinka aduk faɗin duniya." Sosai akejin muryarta na tafiya da sautin waƙar. Dai-dai lokacin kuma Baba malam da Ya Ahmad da Aminu, suna gidan Inna wacce ya samu tana jin radio. Cikin kaɗa kai tace mishi. "Ka jiko Bashiru ka haifi zabiya mawaƙiya, Kaji da kunnen ka ko, Yanzu aka gama gabatar da shirinka na masu imani, Kajita ko ita kuma amara zabiya kantalla mai son kiɗe-kiɗe da raye-raye kamar jikar dujjal." Shiru baba malam yayi cikin jin kiɗan da Zaleeha ta ƙure ta haɗe da muryarta yana hawa mishi kai. Kai ya jujjuya dai-dai lokacin da take bin waƙar inda ake cewa. "Kai d'aya gaiyya mazaje kubi baya. Babu irinka na duba duk nahiya!." Cikin takaici Ahmad yasa hannu ya kashe radio'n, dan ya lura ran mahaifin nasu ya ɓaci sosai da sosai, shi kuma sam baya ƙaunar duk abinda zai ɓata mishi rai ko ya taɓa ƙimarshi. Ita kuwa Zaleeha cikin Shauƙi ta gama gabatar da shirinta kana ta fito. A bakin ƙofa suka haɗu da Bilkeesu mai gado, dan zata shiga gabatar da shirin labaran duniya. Cikin kula tace. "Kadafa ki manta Dukku, gobe da yamma zamuzo gidanku nida Rashida zamuje gidan Adama ta haihu muyi mata barka." Kai ta jinjina tare da cewa. "Ba matsala sai kunzo dama gobe ba inda zanje." Daga nan sukayi sallama, a bakin motarta ta samu Raveel dariya ya mata tare da cewa. "Gani nazo muyi zance kar ai miki dariya, ni d'aya gaiya na isheki a duniya, dukka buƙatunki zanmiki ba inkiya." Murmushi tayi dan dama ai Raveel natane yanada abin dariya dasa mutun Shauƙi. Motarta ta shiga tare da cewa. "Kafi kyau a hakanka ka zauna matsayin abokina." Murmushi yayi tare da rufe mata k'ofar motar. Kai tsaye gidan Addanta Maryam ta biya dan tace mata, Yau awaran couscous takeso tayi mata. A dinning table suka zauna tana cin awaran da aka soya da ƙwai. Sai miyan tarugu damn albasa da dusan kifi. Cikin kula Maryam tace. "Kina addu'o'in da na baki ko?." Kai ta kaɗa mata tare da cewa. "Inayi Addana inata rok'on Allah ya baiyana minshi ya kawo minshi gareni in har shidin al'kairi ne a gareni." Cikin sanyinta da haƙuri tace. "Yauwa yar uwata, ki kuma rage jin kiɗe-kiɗe ki yawaita jin karatun Al'Qur'ani. Ƙinga inma aljanine kamar yadda mama ke faɗi zai rabu da ke." Kunun ayan dake gefenta ta kurɓa tare da cewa. "Mutun nema my Adda na, ina sonshi, ina son abuna." Murmushi maryam tayi kana tace. "Allah ya tabbatar miki da al'khairi!." "Amin Amin." Tace tare da miƙewa, ta ɗauki kular da Maryam ɗin ta cika da awaran tace a kaiwa Aunty Lubna da ya Ahmad. cikin kula Maryam tace. "Ki tsaya kiyi salla mana." Kai ta jujjuya tare da rataya hand bag ɗinta kana tace. "Kin san baba malam baya son in kaiwa dare a waje." Kai ta gyaɗa mata kana ta rakata har wojen motarta. Bayan anyi sallan ishane, Ya Habu ya shigo falon Mama inda ya samu Zaleeha da Zahira da Aunty Lubna suna hira, cikin yanayinshi na rashin sakin fuska dan shi ya gadi rashin fara'ar Mama amman shi yanada mutunci fuska a haɗe yace. "Ke Zaleeha kije Baba malam na ƙira." Da sauri ta dafe ƙirjinta tare da cewa. "Ya Habu meya faru?." "In kinje ai zakiji." ya bata amsa ataƙaice, jin hakane yasanya ta miƙe da sauri tare da zumbula hijabin sallanta, wanda yake har ƙasa ta nufi parlour'n Baba malam ɗin. A bakin ƙofar parlour'n tayi kiciɓis da ya Ahmad, cikin sauri ta kamo hannunshi tare da cewa. "Please ya Ahmad muje ka rakani dan Allah!." Murmushi yayi sannan yace. "To muje." Shiru sukayi baki ɗayansu a gaban mahaifin nasu, yayinda Aminu ke gefe riƙe da wani littafi. Ganin shirun yayi yawane murya na rawa tace. "Baba malam gani." tsareta yayi da ido kana yace. "Na ganki ai, ke nake jira inji ko kin fidda tsayeyye kamar yanda na umurceki." Kai ta jujjuya a hankali kana tace. "A'a." Murmushin girma yayi tare da cewa. "To ba matsala, ni na zaɓa miki, zai zo gobe ki ganshi, in ya miki shike nan, in kuma bai mikiba ba dole na baki kwana biyar daga goben sai ki kawo wanda kike so, In kuma har kwana biyar ya cika baki kawoba to tabbas zaɓina ya zama naki." Da ƙarfi ƙirjinta ya wani irin wawan bugawa, take tsoro mai tsanani ya rufeta, da sauri ta rumtse ido jin Ya Aminu na cewa. "Gobe da yamma zaizo kuga juna kada kije ko ina." Kai ta ɗago da nufin zatayi magana kenan. Baba Malam yace. "Tashi kije sai da safe, Allah ya muku al'barka." Da kyar ta iya cewa. "Amin. " kana ta miƙe ta fita. Kafinma ta isa falon tuni hawaye sun ɓata mata fuska. kai tsaye ɗakinta ta nufa. Da sauri Aunty Lubna tabi bayanta tsaye ta sameta ta kifa kai jikin gini tana rera kuka. Kamota tayi suka zauna kan gado. Cikin sassauta lafazi tace. "Meyasa bazaki zama jaruma ba wurin tinkarar matsalarki abu kad'an ki fara kuka." Cikin zubda ƙwalla ta gaya mata abinda Baban nata ya gaya mata. Gyara zama tayi tare da share mata hawayenta kana tace. "To ai da sauƙi tunda har yanzu dai an baki damarki, ki kuma dage da addu'ar Allah ya kawoshi gareki kafin kwanakin da Baba malam ya faɗan su cika. Kuka ba naki bane addu'ace ta kama ceki." cikin jin ƙarfin guiwa ta gyaɗa kai. Haka dai tayi ta rarrashinta har ta sake. Sannan ta fita ta koma side ɗin Mamy, inda ta samu tuni Mamy ta tafi wurin Baba malam. Ɗakin da take sauƙa idan sunzo ta shiga, nan ta samu Ahmad ɗin na yiwa yaransu addu'a. yana gamawa suka dawo parlour'n Mamy nan yake bata labarin komai a kan Saifuddeen, shiru tayi a ranta tana cewa nakasasshe kuma? a fili kuwa lafewa tayi jikin mijinta. A can wurin baba malam kuwa sosai yayiwa Mamy bayani sanin tanada nisuwa kuma Alhamdulillahi don ai ita tasan Saifuddeen farin sani. Ita kuwa Mama Allah-Allah takeyi girkinta yazo, ta shigar da batun Abdussalam a wurin baba malam, akan zata ce mishi Zaleeha ta amince dashi. Washe gari da yamma ƙawayen Zaliha Bilkisu da Rashida suka zo, inda tuni itama ta shirya, har zasu fita Ahmad yace kada su fita su bari sai gobe in yaso suje, ya fake da yasan Rashida ta iya zana lalle yace ta zanawa Lubna. Sosai suke ganin daraja da girman Ya Ahmad ɗin, dan haka ba musu suka amince. Nan Rashida ta fara zanawa Aunty Lubna lalle, ita kuwa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148