Skip to content

Chapter 29

Chapter 29

Nakasa Ba Kasawa Bace Book One Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
Download Book

alamun yayi azkar tukun, tsaki ya d'an ja tare da cewa. "Kai ni bacci nakeji." bai kulashiba kuma bai sake mishi hannuba dole dai ya zauna sukayi azkar d'in a tare. Suna shiga gida sauri-sauri Ahmad ya gaida Ummi sannan ya nufi d'akin Saifuddeen k'ure iskar fankar yayi sannan ya tura k'ofan d'akin kana ya hau bisa katifar yayi lub tuni bacci yayi awon gaba dashi. Shi kuwa Saifuddeen bayan ya gaisa da Ummi da Rahma su Raliya suka gaidashi sannan ya tambayesu me sukeso ya saya musu kayan salla, kab d'insu zabi suka bashi so da haka ya fita ya nufi k'ofar gida inda Salisu ke jiranshi, yana zuwa suka gaisa kana ya hau yaja machine suka tafi. Bakwai dai-dai suka isa, Saifuddeen na sauk'a Salisu yaja machine ya tafi, shi kuma Saifuddeen kamar kullum cikin masallacin nan ya wuce dan baccin da yakeji yau yafi na kullum, yana shiga ya koma gefe ya konta yana tasbihi a ranshi tuni bacci mai dad'i ya figeshi, sai k'arfe tara da kwata ya tashi al'wala yayi sannan yayi walaha bayan ya idar ya fita ya tsallaka titi ya shiga cikin kasuwar da tuni ta cika tayi mak'il da bani adam. Kai tsaye layin kantin kwari ya nufa inda nanne layin da dilansu yake, yana zuwa ya samu ba kowa a gabanshi nan aka ware mishi aka bashi, daga nan ya cika k'aton kwalin nan ya azashi a kanshi ya fara bin layi-layi lungu da sak'o yana raba musu suna bashi kud'in na jiya. Cikin awa hud'u ya gama, to yau sai bai nufi karb'o omonba sai ya wuce shagon Alhaji ishaq mai atampopi dasu laces materials shadda da dai sauransu. Yana isa Alhaji ishaq d'in da kanshi ya tarbeshi fuska a d'an sake yace. "A Balarabe yau babu omone?." numfashi ya d'an fidda kana cikin yanayin zafin rana ya mishi nuni da kaya yakeso zai saya, gane abinda yake nufi yasa Alhaji ishaq d'in nuna mishi ya tsallako ya shigo daga ciki dan ganin mata sun cika bakin shagon nashi mak'il , yana tsalla kowa ya shiga Ibrahim ya bashi hannu suka gaisa irin gaisuwar nan ta abokai, cikin bada umarni Alhaji Ishaq d'in ya cewa. "Yauwa Ibrahim kama fini gane mgnarshi maza kula da lamarinshi ka bashi duk abinda yake so a farashin sari." cikin jin dad'i Ibrahim yace. "Toh ba matsala." sai ya kuma maida hankalin shi kan paper da Saifuddeen ya bashi inda ya rubuta mishi. "Ina son atampa masu kyau da taushi guda biyu ka bani masu kyau na Ummi nane, sai ka bani laces guda uku masu kyau Adda Rahma orange color takeso Raihana kuma lemon green da ratsin white take so, Raliya kuwa red mai ratsin yellow color, sai ka had'a musu da atampa d'ad'd'aya masu kyau fa." cikin kula Ibrahim yace. "Ba matsala." sai ya kuma juyo ya fara zabo atampopi da laces masu kyau yan ma dai-dai tan kud'i, duk wanda ya zaro in ka ganshi saikayi sha'awarshi. nan ya gama zaro kusan laces kala goma atampa goma, duk ya jibgesu gaban Saifuddeen, nan shi kuma Saifuddeen ya fara zab'o wad'anda zai saya laces uku ya zaro sai atampopi biyar biyu na Ummi ne, sosai ya zabo masu d'an karen kyau. Wata mata dake cikin taron matan da suka cika bakin shagon ne ta zuba sshi ido tace. "Kai wannan kekyawan yaro ya iya zab'an abu mai kyau gsky nima to shi zan bawa zab'i." murmushi mutanen wurin sukayi dan gsky ta fad'i. shi kuwa Ibrahim kud'insu ya rurrubuta mishi, bayan ya amshi takardar ya karanta rubutun Ibrahim sai ya rubuta mishi amsa da cewa. "Nima in nazo nan ba a farashin sari nake baku ledodina ba so nima kada kuce bazakuci riba a kainaba ai ita kasuwa ba k'arya bace kuma dan riba akeyinta sai ni kuma ba sarin zanyiba so naji duk yadda kuka saidawa saura laces in nan nima haka zan biya, dan haka samin su a leda." dole a dai yadda suke saidawa kowa a haka ya biyasu. Daga nan sai ya nufi shagon Alhaji Yawale nan ya sayi wasu datsastsun yaduka masu hegen kyau yad'i ashirin ya saya dan sun bashi tabbacin yadi uku zai isha kamanshi d'inkawa dan haka ya sai yadi ashirin, yayi lissafi yadi tara shida Salisu da Ahmad yadi tara kuma Warisu da Mudassir da Saminu yadi biyun sama kuma Hayatuddeen. sai ya kuma sayan wani yad'i mai kyau yadi shida uku nashi uku kuma Faruq da Adam, bayan ya gama biyan kud'in sai ya kuma fito ya nufi shagon su Jabeer nan ya sayawa su Rahma gyale daddaya wanda zai shiga da kayansun duka bibbiyun, kana yaje shagon masu d'inka hijabai ya d'inkawa Umminshi hijabai guda biyu, sannan daga nan ya fito da ribanshi na yau ya sayawa Faruq da Adam kayan kanti kala daddaya. Bayan ya gama had'a kayayyakin da ya sayan sai ya samu kowa ya samu kala bibbiyu sai Hayatuddeen ne ya samu kala d'aya, so shiyasa ya ciro sauran kud'in nashi ya saya mishi wani yad'i kalanshi mai kyau, daga nan ya had'a kayanshi kab wuri d'aya cikin irin k'attin ledodin nan, sannan yaje ya ajiyeshi a shagonsu Hisham daga nan yaje ya d'auko omonshi yayi ta zaga yawa, Alhamdulillahi yau garin akwai lumshi alamun hadarin forkon damuna sai manyan gajumare masu yiwa sararin samaniya rumfa. Ya saida omon sosai inda ya samu riban 2,700. Ganin yamma tayi sai ya saya musu fruits na 700 d'in. ganin biyar tayi sai ya fito inda Salisu zai sameshi ba tare da ya d'auki kayan daya saya ba, ya barsu a shagonsu Hisham sabida yana son sai gobe in yazo ya sayawa Goggo Dada da Aunty Nina da Bappa Ali kafin ya meda kayan, sabida yanaga in ya medasu yau tamkar ya waresu ne. Koda ya koma yayiwa Ummi bayani, Ahmad kuma yau bai zoba a zatonshi Saifuddeen zaizo ne. Washe gari kuwa kamar yadda yayi niya haka yayi, daya gama hada ribarsa na jiya sai ya sayawa Goggo Dada turmin zani hakama Aunty Nina sannan ya sayawa Bappa Ali shadda mai kyau. daga nan ya hada kayan sannan ya tafi tallan omonshi. Biyar dai-dai suka nufi dukku suna isa Dukku, kamar kullum bayan sun gama komai ne sunje tabsir sun dawo ne ya fito da kayan yayi musu bayani sannan ya bawa Ahmad kayan tare da cewa yau Salisu ne zai maidashi da mashin, Saminu kuwa nan yake ce musu. "Yauwa ni nama manta ban gaya muku ba na saya mana takalma da huluna, wanda zamuyi fitan idi dashi dama d'inkin naso in yi mana to sai naga takalma da hulunan zaifi armashi." sosai suka cika da farin ciki nan Salisu kuma yace. "To ni kuma zan saya mana agogo masu kyau." Ahmad ne ya kalli Saifuddeen da yake mishi bayanin wannan 10k d'innan ya sayi kayan d'inki dasu. harara ya mishi tare da zaro kud'in dan dama ya taho dasu dan ya zargi hakan bashi kud'in yayi tare da cewa. "Ingo amshesu inada kayan d'inki kai dai ba ka saya ba ka kuma bani to ba ruwanka da batun d'inki in naga dama in d'inka na iyayenane da abokaina da k'annena da yarana in naga dama ink'i dinka naka in

Table of Contents

Chapters

148 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148